Sashe 125
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi aya bayan aya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma ya i ci, ta koma kitchen ta ha o mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi ya i mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah ___________________________________ *ALHAJI MUSA Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta anyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar. Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya aure mashi kai babu kowa a kan kujerun yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba. Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani" "ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"? "Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..." bata kare maganar ba, rai a6ace ya aga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba. "Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta "You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!" ta fa a tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka ka a jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi. Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya dam i arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta. softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta are maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya fa a tare da dago da fuskarta suka ha a ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri, idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" aure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" ma e mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba" "It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs. A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin arar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi, Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin bu e toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa shatunsu ya fito rudu rudu, sai yaji ba dadi aran shi, ganin irin illar daya yi mashi kuma yayi imanin zafin marin da yayi mashine ya haifar mashi da rashin lafiya a jikin shi kamar yadda yaji Tani tace bashi da lafiya. Kwata kwata shureim bai lura da Alhaji musa ba, cikin rashin kwarin jiki ya nufi dressing mirror. "Shureim"!Ya kira sunan shi, aure fuska yayi batare daya kalli inda yake ba, duk da yayi mamakin jin Muryarshi a cikin kunnanshi aranshi ya ayyana kome yazo yi dakin shi?ya dai san ba hakuri yazo bashi ba abune mawuyaci. "Da kai fa nake magana"! ya fa a fuskarshi adaure, da farko yaso ya shareshi don yaga iya gudun ruwan shi amma sai ya fasa saboda mutunne shi mai matukar ladabi da biyayya yana ganin girman nagaba da shi bayan haka akwai na annabawa wato hakuri. Juyowa yayi suka fuskanci juna Muryar shi kasa kasa ya furta"Uncle, barka da safiya? Ka tashi lafiya"? ya dan yi mamakin tarbar da shureim yayi masa, amma bai nuna a fuska ba, "ka zauna inason magana dakai" kasa kasa ya amsa da toh, kafin ya juya ya shiga wurin closet dinsa, jim ka an ya fito sanye da jallabiya fara, a kan couch suka zauna shureim ya kau da idanun shi gefe aya yana jiran jin dame yazo! "Shureim dangane da abun da ya faru jiya bana a cikin hayyacina, kasan inada bad temper idan raina ya 6aci bana iya controlling kaina..." yanayin yadda yayi maganar ya aurewa shureim kai har saida Ya juyo dakai ya kalle shi don ya tabbatar idan dagaske uncle musa ne ke yi mashi magana ba wani daban ba. a ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe aya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ru e mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi. o hannun shi yayi a cikin nashi ya ru e su gam na an wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya fa a yana an jinjina kan shi. "Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi. Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi. Kafin ya aura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace aya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"? Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da