Sashe 122
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
kallon shi "Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ara kara e kunnuwansu... Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matu aga hankulan su fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun." Ummi tace"Anila raba kanki da an adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"? Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina wa annan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu anyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba. Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali "Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi" Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta bu e baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" fa a sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru. ewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai ra i da tafara ji, gaba aya suka bita da kallo ganin ta mi i hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta. da sauri Abie yabi bayanta ya dam i hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin wace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..." Tana cikin yin magana ta sar e kwatsam ta yanke jiki zata fa i da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar ki ima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya fa asa. La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh? dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da bu ar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na auko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta bu e min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun azu, sai na mi a mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai aga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba aya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe. "Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr, duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi. Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows asa dressing mirror dinta ya kife asa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ara jefasu a rudani...." Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta auko robar ruwa a fridge mai sanyi ta bu e murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta bu e idanunta wa anda suka ka a jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su da yar ta iya motsa la66anta da suke bushe amas ta furta"mami ina junaid ina? Ana ta dawo min da shi" shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta... Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna har ewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su. "Zahra kun kira layin Ana in"? aga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ru e qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya kara e kunnuwan su Uncle an iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki" __________________________________ UNAISAH ANGEL Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata atutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta fa o mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani. Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya auketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab.... Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa.. "Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita... "Ya jikin naki? azu naga kamar kin samu lafiya.." shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka.. Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta an sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa bu e baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta an rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"? "Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta fa a tare da saukowa daga kan gadon ta fara aga pillow tana nemanta, hada kokarin