← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 58 OF 247

Sashe 58

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

bar gangar jikin ta, komai na duniyar nan ya sire mata, taji takaici da tsanar rayuwar da ta daukarwa kanta saboda takasa hakuri ta rungumi addarar ta, Sai gashi yau taji abunda Ya jefata adanasani, Yan kananun Yara da basu ji ba basu gani ba, wadannan ma tun suna jarirai suke fuskantar jarabawar rayuwa, Ita kuwa da ilminta da hankalin ta da tunaninta ta fa a harkar karuwanci saboda ta kasa cinye jarabawarta lamarin yayi matukar gigita tunaninta... Faucet ta kunna ruwa ya soma shararowa ta tarfa hannu tana watsa shi akan fuskarta, kamar an zare mata karsashin jikinta, da wata irin kasala ta fito jiki babu wari ta fa a kan gadonta tare da kifa kanta jikin pillow, bakomai take tariyowa ba face rayuwarta ta baya... Sam ba taji motsin shigowar mutun ba, saboda ta lulu duniyar tunani A hankali batool take tafiya tana tunkarar gadonta, hayewa tayi kan gadon ta zauna kusa da ummi tana le en fuskarta "Aunty Ummi," kamar daga sama taji muryar batool, a hankali ta bu e idanunta da suka kumbura ta daura su kan fuska batool. "Dan Allah ki daina kuka aunty ummi, bana son ganin hawayen ki, bana jin dadi" ta fada muryarta na rawa alamar zata fashe da kuka. Janyota ummi tayi tare da kwantar da ita kan kirjinta, sosai ta rungumeta ta daura hannunta akan bayanta batare data furta magana ba. Aranta tana mai mamakin tawakkalli irin Na Yaran, abunne da daure kai, da ace wani mai karancin imanin ne hakan ta faru da shi da tuni yajima da hadiyar zuciya ya mutu amma su a haka suka jure da dadi da ba dadi sukai ta rayuwar unci a kulle tun kafin su mallaki hankalin su. Numfashi taja, wani irin kaunar yarance taji ta ara kama zuciyarta, har ta fara tunanin tawace hanya zata taimaka masu don ganin sun inganta rayuwarsu tun da basu san komai ba . Bakomai ne ya fado mata aranta ba face zagin da ta ta6a yima batool har ta kirata da sunan jahila wadda bata san komai ba sai ci da bacci... Runtse idanunta tayi sosai tana mai jin takaicin kalaman da ta furta mata, gashi yanzu yarinyar tafi kowa kaunarta Shafa sumar kan batool taci gaba dayi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba dasu arungume da juna kamar zasu dawwama ahaka....... ___________________________________ Unaisah Angel Fitowa tayi daga part dinsa bayan ta gama gyara masa shi, A hankali take saukowa down daga kan stairs zuciyarta cike fal da tunanin abubuwa da dama wadanda suka faranta mata rai a yau kamar wata zautacciya sai faman sakin murmushi take yi. "Daughter i'm back" miryar taj ce ta katse mata zancen zucin nata, kallon shi tayi fuskarta da fara'a, da sauri ta karasa sauko down, mayafin kanta har yana kwancewa daga kanta ya zame ya fa o kan kafadarta, sumar kanta ta rufa mata bayanta. Tana arasawa ta fada kan kirjinshi kamar wadanda suka dade basu ga juna ba. Murmushi yasaki yana fadin"sannu da kokari ina fata kin yi abun da Ya dace" agowa tayi da kanta ta daura idanunta akan nashi"har gyara masa part din sa nayi, kafin ma na kammala har ya fita ban same shi ba" "May be ya tafi gidan kakansa ne" acewar chief, "Kinsan me naje yi agida" girgiza mashi kai tayi alamar a'a. "Auntynki na fa a mawa ta hada maki wani abu mai dadin gaske zuwa anjima zatay ba uwa, amma fa ban gaya mata wacece zata zo ba" "Naji dadi daddy, kana ji dani" Mayafin ta dake akan kafadarta ya ruko yana fadin"bari na gyara maki shi" A hankali Ya soma na a mata shi, bayan ya kammala ya manna mata sumbata kan kuncin ta kafin ya ago da kansa kwatsam! Ba zato ba tsammani Yaji saukar dundu akan bayanshi tamkar za'a rusa shi, tsabar zafin da yaji ne yasa shi saurin dafe bayan da hannu, tuni ya fara ganin jiri a cikin idanunsa. Hankalin ta amatu ar tashi ta wurga idanunta don ganin wane yayi wannan aika aikar saboda itama taji sautin dundun da akayi mashi. Har saida gabanta Ya fa i lokacin da tayi arba da shi atsaye yana huci tamkar mayunwacin zaki, tsabar fusata jikin shi har gumi yake fitarwa, magana yakeso yayi amma saboda zafin da zuciyarshi keyi mashi ya kasa sai la66ansa dake kerma. Harara ta watsa mashi saboda ya bata haushi, zuciyarta ajagule ta ru o hannun taj Tana fadin"Inna lillahi! daddy dan Allah kayi hakuri..."_ bata are maganar ba, danish Ya fusgo ta tare da janyota jikin shi, yasa hannu biyu ya rungumeta kamar zai maida ta cikinsa Lamarin yayi matu aurewa taj kai, idanunsa jawur yake kallon danish Yama rasa me zaiyi, amma tabbas dundun da yayi masa ya kusa yi mashi illa saboda zogin da bayansa keyi mashi kamar an ana masa wuta yadda kasan ba hannun mutun bane yayi dundun, yaji zafinsa sosai. Kiciniyar kwace kanta tafara yi hawaye tuni sun wanke fuskarta ganin baida alamun sakinta ne yasa ta daddage ta gartsa mashi cizo kan kirjinsa, ko gizau baiyi ba, saima ya kara hadeta da jikin shi, zuciyarta har tafarfasa take yi mata saboda 6acin rai. Kallon kallon suke jefawa junansu tsakanin shi da tajuddeen, kwata kwata bai yi yun urin Janye angel daga jikin danish ba, saboda ya fahinci Yaron ba shi kadai bane tun daga kan dundun da yayi mashi ya shaida hakan. Shigowo Falon big guy da an saurinsa Yana ganinsu Ya nufe su da mamaki Yake kallon Danish daya rungume unaisah "Lafiya? Meke farune"? Taj ne yai karfin halin fada masa abun da danish yayi masa Zuciyarshi ta sosu Harara Ya watsa masa kafin Yace"Sakar ta, tun kafin na 6ata maka rai, kaida bawani koshin lafiya ba har ka fara neman rigima? Ko kunya baka ji ba ka rungume Yarinya gaban ubanta! Idan ma baka sani ba to bari na fada maka wannan da kake gani mahaifinta ne wanda Yai silar zuwanta duniya...." ko ajikinsa bai ma fahimci me Big guy yake nufi ba, sai ma haushin shi da yake ji, Jira yake big guy yakai hannu zai raba shi da ita anan ne zaiga ainihin true colour dinsa... Atsawace big guy yace"baka ji me nace ba, ka sake mana"! "Ka daina yi mashi tsawa, Ka kyale shi kawai, nayi mashi uziri saboda baisan komai ba, kuma Yaro ne sai muna lalla6a shi" Big guy bai tsaya sauraron Taj ba Ya kai hannu zai ja rigar unaisah, wata irin kururuwar tsawa danish Ya daka mashi tamkar saukar aradu, Gaba aya saida suka firgita saboda Yadda sautinta Ya cika masu kunnuwan su, Unaisah dake manne ajikinshi tsabar ki ima kiris Ya rage ta saki fitsari a wando, saboda firgitar da tayi. idanunsa sun ka a jawur Yana huci Ya furta"kada ka kuskura ka ta6aba, Ranka zai 6aci, zanyi maka abun da baka ta6a tsammani ba, Idan har kayi gigin shiga tsakanina da ita...." ya fa a yana faman cije red lips dinsa, yadda kasan ba daga bakinsa kalaman suka fito ba saboda girman su. da gudun gaske Naufal da Sajeed suka fito daga dakunansu, kamar wadanda aka koro tun wannan tsawar da danish ya kwatsa kowan nan su Ya firgita har wadanda ke adaki, kai hatta Ummi da batool sai da suka farka daga bacci jiki na 6ari suka sauko down stairs, aya bayan aya suke fitowa wansu da kwarkwatarsu, hankalinsu gaba daya yana akan Daninsh dake a rungume da unaisah, jikinta sai kerma yakeyi duk tabi ta ru e, numfashinta kanshi dakyar take fidda shi. Kusan atare suka hada baki suna tambayar meya faru? danish dan Allah kayi mana bayani meyasa ka ruke Unaisah ka sake mana ka matseta.. Sajeed ne yai maganar, Big guy daya gama harzu a Har Ya yunkura zai ara kamo rigarta Taj yai saurin dam ar damtsen hannun shi, suka hada ido da juna girgiza mashi kai yai alamar a'a saboda shi yasan mai yaji dakyar in ba sai yayi jinyar bayansa ba. "Haka zamu zuba mashi ido muna kallon shi? Baka ga yadda Ya matse ta bane? Ko magana takasayi"! Cikin muryar lallashi Taj Ya dubi Danish dake ta faman zare idanunsa tsabar masifa har ance su yakeyi "Dan Allah kayi hakuri ka sake ta, indai saboda ni ne bazan ara taba maka ita ba" Mamaki da al'ajabine Ya kama su Ummi dake kallon Ikon Allah "Meyasa zaka bashi hakuri? Kaida arka? Tsoron shi kake ji ne"? A harzuke Big guy yai maganar Taj yace'ba tsoron shi nake ba, fitina ke bana so, idan mukace zamu bi ta karfi da yaji donmu kar6e ta wlh ba zamu iya ba sai dai muja yai mata wata illar kwara mu lalla6a shi' guntun tsoki Big guy yaja, gaba daya haushin danish Ya cika shi, duk da yana tausayin prisoners sai dai ayanzu lamarin danish Ya fara sanya shi kokwanto akansa, gani yake kamar yaron yana da wata muguwar manufa. Haduwa su Naufal sukayi suna ta yi mashi magiya don Ya sake ta, Amma Ya i sakinta Suna acikin wannan Halin, a lokacin da basu yi tsammani ba, Sallamar Salsabeel Ta katse su, gaba aya suka dago suna Kallon shi Ganin shi yasa danish sakin Unaisah tai taga taga zata fa i da sauri batool ta ru ota, sai faman haki takeyi tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu.... Sunyi tunanin shi kadaine Yazo, kusan atare muryoyinsu khadeeja Ya daki kunnuwansu, tunkafin su karasa shigowa suka fara kokarin tunano su wanene? Saboda sun haddace muryarsu ko tari sukayi za su iya sheda su. aya bayan aya suka fara Shigowa bakunansu dauke da sallama, Lokaci aya suka Ci burki suna Kallon su Unaisah dake kallon su, kusan atare zuciyoyinsu ke harbawa da matsanancin karfi, Tsabar rudani da al'ajabi Ya hana su gasgata abunda idanuwansu suke nuna masu, har abada ba zasu ta6a mantawa da muryoyin yan uwansu ba, balle kuma kamannin su da basu ta6a gogewa a idanunsu ba, Kokwanto sukeyi anya kuwa yan uwan sune da suka baro prison ba rai? Ko dai mafarki sukeyi ne? Ko kuwa idanunsu ne suke nuna masu badai dai ba? Tayaya ma haka zata yiwu? Murza idanunsu suka farayi don su kara tabbatarwa da kansu abun da suke gani dagaske ne ko akasin hakan!
Chapter 58 · 0% Book details