Sashe 30
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 3 min read
ba. Kafin ta are zancen zucin nata ba, da mamaki taga danish yabi prime minister hannun su ru e cikin na juna suka nufi hanyar fita daga hall din ko irin ya waigo ya kalle su baiyi ba, ajiyar zuciya ta sauke, sarai ta fahimci masu satar kallon ta. gimbiya mujeedat sai bin su da kallo take yi, tarasa ma wani irin tunani zatayi game da bawon Allan nan mai tsantsar kama da Nazli, kasa jurewa tayi da sauri ta bi bayan su, ita ma Yazrin ta bi su, Nazli ce ka ai ba tayi yunkurin bin su ba, kwata kwata babu annuri akan fuskarta, Ita bakomai ne damuwarta ba face abu biyu, na farko yaron da ke kama da ita! arayuwarta ta tsani ace wani yana kama da ita, saboda izzarta, tafi so mai nata ya kasance ita kadai ke da shi, bayan wannan sai Unaisah! Hankalin ta bai kwanta da ita ba, saboda wani kallo da taga sun jefa wa juna a tsakanin ta da chief owais nan take taji bata son ganin yarinyar, Nazli tana da zafin kishi, izzarta ce ke hanata bayyanawa. Fuskarta babu annuri ta kai hannu ta dauki wayarta dake kan floor, da wani irin takun qasaita ta juya tabar wurin su. Mom turai da ke ta kallon su tun azu take son tunkararsu ganin babu dama ne yasa ta yi shiru tana kallon bada alar da ake yi, yanzu kuwa da ta samu dama, Da sauri ta nufi wurin Azeeza saboda sun bata tausayi da suna kuka, hanky ta zaro daga purse dinta, ta zu unna agaban ta tare da sanya shi kan fuskarta ta shiga share mata hawaye Cikin kulawa tace "Stop crying kin ji ko? everything is over now, we are welcoming you to our family" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyinsu har sun fara an sakin jikin su. A hankali Sir mubarak Ya nufi Jemimah dake a ma ale da Angel ta cukuikuiye mata rigarta zukunna yayi agabanta, ya ru o hannayenta a cikin nashi yana rarrashinta ganin har yanzu tana shesshekar kuka. "Sorry baby girl, share hawayen ki...." muryarta na rawa ta furta"wlh baku son mu, shiyasa ku ke korar mu, ni dai gida zan koma Allah" a fadace ta fa a tana faman zabga masu harara, an kumatunta sunyi jawur da su. Ba zato ba tsammani Taji Sir mubarak Ya dauketa dungurum Ya daurata kan kirjin shi, wu i wu i tayi da idanunta. "Sai mu ga da wasu kafafun zaki koma gida, ay tun da ki ka shigo wurin nan sai mun ci abinci dake, idan kuma mutun yace zaiyi min rigima zan sanya bindiga ne in har be mashi tsakiyar kan shi" Ya fada Yana daura yatsan shi akanta, Murmushi kowan nan su ya dan saki. "Bismillah ku shiga daga ciki mu zauna, ko baku gaji da tsayuwa bane" Zaki ne yayi maganar Yana nuna masu cikin hall din, su kansu so suke su zauna kafafuwansu har sun fara ru ewa kawai suna fargaban shiga ne. Ganin hakan yasa zaki matsawa ya ru o hannun Sajeed Dana Naufal Ya shiga da su cikin hall din, Da sauri Dr Jazz Ya matsa Cikin su ya ru o hannun javed dana haris yayi ciki da su. Bayan mom turai ta gama sharewa azeeza hawayenta, ru o hannun ta tayi suka nufi table din su. babu wanda yayi tsammanin Hajiya malikat zata tanka, don tunda aka fara rikicin bata sanya baki ba, sai yanzu data matso kusa da su ta an saki fuskarta tana fadin"naga kowa dan uwansa yake dauka nima bari na dauki nawa" ta fada tare da ru o hannun Unaisah, ta ha a dana batool dake a gefenta"mu shiga ciki an mata," wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da sauri suka bi bayan ta, chief owais dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa sai kallon su ya ke yi, hankalin ya kwanta babu sauran damuwa.