← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 98 OF 247

Sashe 98

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa "Sannunku da dawowa, ya mai jikin"? Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"? Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba. wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi. Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci. *EX-PRISONERS* Around arfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta, Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet Murmushi tasaki ha i da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., aya bayan aya ta fara farkar da su "Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta mi e tana an soshe soshe "Wuce kije daki" ta amsa mata da toh, "Praveen ku tashi..." cikin magagin bacci ta bu e ido bakinta cunkushe da apple din da bata karasa cinyewa ba, bacci yayi awon gaba da ita, mi a tayi tare da yin hamma ta nufi dakin su, ganin tana tangal tangal kamar zata fadi ne Yasa ummi yin saurin cafko hannunta, a lokacin ta samu hannah ta mike, ta ruko hannayensu a cikin nata har aki takaisu, sai da taga sun kwanta kan gadonsu kafin ta dawo falon Taci gaba da tada su"sajeed! Naufal ku tashi dan Allah, Mubeen Haris! Javed! Wai baku ji ina magana ne"? da wata irin kasalar bacci kowan nan su Ya mike har kwara mazan da kwarin su, suka nufi bedrooms dinsu Wurinsu jemimah ta nufa, sun cunkushe kan sofa mai mazaunin mutun biyun yadda kasan kifin gwangwani, hannu biyu tasa ta dauki jemimah, ta daurata a kafadarta, kafin ta sa ayan hannun ta ago Azeeza, ta daurata a dayar kafadar ta, ahaka ta nufi dakin su, ta kwantar da su kan gadon su, sai da ta kashe masu switch din dakin kafin ta fito ta koma falon, "Sarah! Wake up, rubina! Hibba! Pls ku tashi! Mana, Yasmin"! Har ta fara gajiya da tada da su, mikewa sukayi kamar babu laka ajikinsu, raka su tayi bayan sun kwanta ta dawo tana kallon wa anda suka rage, Eve ce kwance kan rug tare da Deeja..Sai unaisah dake a na e kan sofa, "Deejatun haris, Ta shi muje ki kwanta..." cikin magagin bacci ta fara sambatu tana fadin"wai meye haka ne? Ni ku kyaleni wallahi kada wanda Ya ara min magana..." Hannu ummi takai da niyar ta dago da ita, aikuwa ta daddage takai mata naushi a gefen bakin ta, tsabar zafin da ummi taji ne Yasa tayi saurin dafe bakin, ta lalla6a ta koma kan sofa ta zauna tana faman yarfa hannunta, ranta ya 6aci taji haushin naushin da khadeeja tayi mata, hakan yasa ta yanke shawarar barin ta a falon ta kwana, gudin kada ta lahantata garin tada ta daga bacci Mikewa tayi ta nufi hawwa ta dan bubbuga kafafunta, cikin sa'a ta farka "Ki je daki ki kwanta" amsa wa tayi da toh, bayan tafiyar hawwa ummi ta nufi unaisah Bata tada ta daga baccin ba, daukarta tayi akan kafadarta, ta nufi bedroom dinsu da ita, tana shiga ta kwantar da ita akan gadonsu, ta kashe mata switch dakin, Bayan ta fito falon, Ko kallon inda deeja take akwance batayi ba, don ranta Ya 6aci, kaitsaye ta nufi hanyar komawa dakinta, har ta kusa shiga taci karo da Batool kwance kan matattakar benan sai faman sharar baccinta take Yi da alama zamewa tayi awurin ta fa i cikin magagin watakil tayi azan gadone shiyasa taci gaba da baccin ta aukarta ummi tayi da hannu biyu ta cucci6eta, ta haura da ita upstairs, bayan ta shiga dakin, ta kwantar da ita kan gadon su kafin itama ta haye ta kwanta tare da rungumota a jikin ta.... UNAISAH ANGEL Around arfe 1:30 na dare, ta farka da matsanancin ciwon mara mai azababben zafi, hannayenta dake kerma ta aura su akan cikinta, sai faman murzarshi take yi, sai faman yin birgima take akan gadon, da yar ta bu e idanunta wa anda suka ka a jawur da su, cikin mawuyacin hali ta kai hannu jikin bedside lamp ta kunna fitilar haske ya gaure zagayen gadon da take, wani irin gumi ke tsastsafowa ta jikin ta, hatta pajama din dake a jikin ta sun manne ma fatarta, urawa tayi da yar ta sauko daga kan gado ta shiga toilet, ta haye kan toilet seat, tayi fitsari anan taga jinin da ya dawo mata jawur yana gangarowa ta tsakantsakin cinyoyin ta, runtse idanunta tayi da karfi duk irin aukin da take na son ya dawo mata sai da taji abun ya fita ranta saboda ra in da mararta ke yi mata Bayan tayi tsarki ta fito, babu wandon ajikin ta, can ta baro shi a toilet....a gaban drawer chest na wardrobe din kayan su ta zukuna ta bu e tare da sura hannu ta auko pad daya, ta ha o da pant, akan mattress ta aura su tana faman sakin nishi kamar mai na uda, "Can I give you a hand ."! kamar daga sama ta tsinkayi muryar mutun a kunnanta, sai tayi tsammanin gizo muryar shi keyi mata...kwatsam hasken akin ya dauke uff duhu ya gauraye ko'ina, a firgice take kallon duhun daya mamaye idanunta, gashi bata arasa sanya pad din ba, cikin duhu tafara laluban gefen gadon don ta kunna fitar, ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun akan mararta, a matu ar firgice ta zare gray eyes dinta, muryarta na kerma ta furta"de...deeja? deeja? Shiru ba'a amsa mata ba...tasan su biyu suke kwana dakin shiyasa ta ambaci sunanta, tunani tayi kadai batool ce "Batool ke ce? Shiru ba amsa,"dan Allah wanene? A tsananin tsorace tayi maganar. "Daddy...." bata kai ga arasa maganar ba, Taji gaba aya anjayota, ta fa a kan kirjin shi, farat aya ta gane koma wanene namiji ne kuma kakkarfa, Kware baki tayi zata fasa ihu yayi saurin ha e bakinsu guri guda, jikinta ya fara kerma tafara kiciniyar kwace kanta, kamar yar dambe ta dinga uma masa dundun da hannayenta wa anda ke abayanshi, tayi kuka tayi haukan ko gizau baiyi ba har gartsa mashi cizo tayi wuri uku a kirjinshi amma babu alamun yaji zafinda zai sake ta Fashewa tayi da matsanancin kuka"wayyo Allah daddy na, Aunty ummi, my man kana ina? Kana gani za'a cutar dani, na shigo uku wayyo Allah..." da iya karfinta na karshe ta bangaje shi gaba aya ta kife kan floor, bata iya ganin komai da rarrafe tana laluban hanyar fita daga akin, afafunta taji ya ru o da hannayensa biyu ya ago bai direta a ko'ina ba sai akan gadon ta Ta yunkura zata gudu Ya hambareta da gwiwar hannunsa, kanta ya daki pillow, kafin tayi yunkuri sake mikewa, mutumin ya toshe mata baki da tafin hannunsa gaba daya ya sakar mata karfi, ta yadda ko yatsan hannunta bazata iya motsawa ba, numfashinta dakyar yake fita, wani iri danshi danshi ta fara ji agabanta kamar ana zu e jinin dake fita ta farjin ta, runtse idanunta tay zufa ta fara tsastsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, ga wani azababen zafi da matsananciyar kasala da suka rufeta a lokaci aya, ta fara jan numfashi tana nishi, hawaye masu umi suka wanke fuskarta, gaba daya ta zauce ta rasa tunaninta, lamarin kamar a amafarki take jin afkurwarsa, ta kasa ta6uka komai, sunan danish dana daddynta da aunty ummi kadai take iya ambato cikin zuciyarta a karshe raci gaba da ambton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Shin wanene Yayi ma unaisah wannan aika aikar _____________________________ A zaune Yake kan darduma, Cikin shiga ta farar jallabiya, Hannunsa ru e da qur'ani Ya nutsu Yana karanta shi, "Assalamu alaikum"! Cikin kunnanshi Ya tsinkayi muryar abbansu, sai da yakai aya kafin daura kur'ani kan prayer mat din Ya dago da ita Ya dube shi, Yana asanye cikin kakin shi, zama yayi daga gefen gadon shi Yana duban fuskar dan nasa dakyau, "Ina kwana daddy, Kun tashi lafiya"! "Meke damunka"? Kai tsaye Ya jefa mashi tambayar, Sunnar dakai kasa yayi kafin ya furta me ka gani daddy"? "Abubuwa da dama! Na farko kwata kwata baka acikin nutsuwarka, tun zuwanka Nigeria na lura da akwai wani abu dake damun ka! Bayan haka me ya hana ka komawa bakin aikin ka!? Shiru yayi ba tare sa ya furta kalma ba, baiso daddynsu Ya fahimci halin da yake aciki ba, saboda baya son Ya aga hankalin shi, "Kada ka 6oye min komai, duk duniya baka da kamata, kasan tsakanina dakai babu sirri, Idan wani abune ke damunka, ka sanar dani, in sha Allah zan taimaka maka mu sami mafita atare..." Ya fa a cikin nuna kulawa Bayajin zai iya 6oye mashi damuwar shi,tun da harya riga daya gano da kan shi, kwara kawai ya fada mashi gaskiya, Cikin sanyin murya ya zayyana mashi komai, tun farkon haduwarsu da Benazir, da irin rayuwar da sukai har izuwa rabuwar su..." dagowa yayi idanunshi jawur cike tab da hawaye ya kalli daddyn nasu "Daddy ka tayani da addu'a, Allah Ya jarabceni da sonta, ko baccin kirki bana iya yi saboda rashin ta
Chapter 98 · 0% Book details