← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 67 OF 247

Sashe 67

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

baya son mommynsu tayi silar jefa ta cikin wani hali wayar dake a kan side drawer din su, Yakai hannu ya dauka Ya danna wa landline din kitchen tana fara ringing maid ta auka, ya bada umarnin akawo masu breakfast dinsu, Kafin Yai cutting kiran ya ajiye wayar kan drawer Badajimawa ba, Abla ta shigo dakin da tray mai dauke da kayan abinci, ta ajiye masu kan drawer bayan ta gaishe da zaid ta juya ta fuce.. ________________________Dattijon Arzi A zaune yake kan lallausar darduma, hannunsa ru e da cazbaha, a hankali Yake motsa la66ansa, kusan rabi da kwata na hankalinsa na akan chief owais dake kwance saman dardumar ya aura head insa akan laps din baba obie, kyawawan idanunsa suna a lumshe tamkar na mai jin bacci, su duka biyun daga ka kalle su zaka shaida tsantsar nishadin da suke aciki, musamman baba obie, ransa fari fat tunda owais ya kawo mashi ziraya yau kusan wuni yayi awurinsa duk inda zasuje atare suke tafiya, ba su jima da dawo daga masallaci ba suka shigo garden don su sha iska, sai faman satar kallonsa yakeyi kamar ya ha iyesa haka yake ji tsabar kaunarsa da ya ke ji. "Grandpa, wannan kallon na menene"? Idanunsa a lumshe Ya jefa mashi tambayar. Fuskar baba obie da fara'a Yace"Kallon so da kauna ne rabin raina, wallahi yau ka faranta min rai, gaba daya ka debe min kewar hateem dake damuna...." A hankali chief Ya an bude idanunsa Ya saci kallon fuskar baba obie karaf suka hada ido cikin na juna "Baba...." Ya fada ba tare da ya arasa maganar ba "Na'am sanyin idaniyata, Naji ka kira sunana kuma ka yi shiru" gyara kwanciyarsa yayi batare daya bashi amsar tambayar sa ba. "Duk cikin jikokina babu wanda Ya more ni kamar ka, kaga cinyar nan tawa tun kana arami kake tumurmusarta, gashi har yanzu baka daina taushe min ita ba' murmushin gefen fuska Chief yai masa har chin dimple dinsa Ya dan lotsa. "Meya fi raina"? Ya fada Yana kallon fuskarsa. "Ni fa idan ina atare dakai, sai naii kamar an mallaka min komai na duniyar nan, ni dai Allah Ya jarabce ni da sonka kakana ina fata Allah ya dawwamar da farin ciki atsakanin mu zan cigaba da tayamu addu'a Allah Ya Ya ara mana tsawaicin kwana ko dan na cika maka burinka akaina......." tun da yafara magana baba obie ke kallon shi da wani irin matsanancin farin ciki akan fuskarsa, dakatawa yayi da jan cazbahar Ya aura tafin hannunsa kan sumar Owais a tsanake Ya soma shafata kamar yana yi masa susa. "Kalamanka sun sanyaya min zuciyata, Owais kai na dabbanne, wallahi yadda nake jinka bana jin ko iyayanka, kai tamkar bugun zuciyana ne, wallahi bansan Yadda zan misalta maka kaunarka da nake yi ba....." kafin Ya are maganar, ruwan hawayen da suka taru cikin idanunsa suka gangaro kan fuskar chief, lokacin da yaji saukar su a ru e Ya zabura ya mike daga kwancen da Yake, Idanunsa akan fuskar baba obie da alamun ru ani Ya furta"baba meyasa ka zubar da hawayen ka? shiru yayi batare daya iya furta masa wani abu "Fadamin mana, ko dai maganar da muke yi ce ko kuma akwai wani abu dake damunka"? Girgiza kai yai"a'a owais kada ka damu babu abun da ke damuna, kawai bana son duk wani abu da zai shiga tsakanina dakai, Ina jin fargaban duk wani abu da zaisa ka juya min baya, ni dai bana son 6acin ranka......' ru o hannayen baba obie yai acikin nasa yatsun hannunsa har kerma sukeyi"baba bazaka iya boye min komai ba, idan har kana da damuwa kallo aya nake yi maka na fahimta, Ina ji araina da akwai wani abu dake damunka dan Allah ka fadamin habibi na, nayi alkawarin zanyi iyakar bakin kokarina wurin kawar maka da damuwarka...." da warin gwiwa ya furta maganar Yana kallon idanun baba obie da suka kada jawur gray eyes dinsa sunyi ja tsufansa duk Ya ara fitowa. Wani murmushi yayi mai ta6a zuciya kafin yace"Idan na fa a maka abun da ke damuna zaka 6oye min sirri na ba zaka fada ma kowa ba sannan zaka rufa min asiri" jinjina kai owais yai da alamun rudani akan fuskarsa kamar baison furta maganar Yace"najima inason sanar dakai, sai dai inajin fargaban yadda zaka dauki abun aranka, ka yi min alkawarin ba zaka fusata ba" ya fada la66ansa na kerma, ba karamin rikita tunanin chief owais Yayi ba, gwiwarsa harta sage In a low voice Ya furta"ni mai rufa maka asiri ne babana, bazan bari kowa Ya sani ba, tona maka asiri tamkar tonawa kaina asirine da zuri'armu" jinjina kai baba obie yai sai da yafara kallon garden Din Ya tabbatar babu mai kallon su kafin Ya matsa gab da chief owais Yayi masa ra a a kunnansa. Lokaci aya chief ya an janye kunnansa da tsantsar mamaki Yake kallon baba obie wanda tuni yasha jinin jikinsa, ba zato ba tsammani a lokaci aya suka tuntsire da dariya kamar wasu zautattu, Yaushe rabon da inga chief yayi dariya irin wannan ni kaina namanta, komai nasa mai jan hankali ne. dariyar tayi matu ar tafiya da imanina, saboda gaba aya ta bayyana zunzurutun kyan fuskarsa, dimpla dinsa duk sun lotsa, fararen hakoransa kamar auduga tsabar hasken su, sun au lokaci suna ti ar dariya kafin daga bisani chief ya kifa kansa bisa kafadar baba obie, hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba, da farkon yai tsammanin wani mugun abunne zai fa a masa ashe ba haka bane Muryarsa tamkar tame jin bacci Ya furta"Grandpa are you kidding me"? Baba obie na murmushi yace"Wasa nake maka owais, Ni ina ni inayin aure, tsofe tsofe dani, ga tarin ya'ya da jikoki" "Wannan ba hujja bace, Indai Kana son Yin auren ka fadamin, in sha Allah I will try to find a righteous life partner for you." Da zolaya baba obie yai masa dundu akan bayansa tare da cewa"Owais wlh wasa nake maka, kawai don inga reaction dinka ne, kuma nagani tunda gayanan na sanya ka yin dariyar da ka dade baka yi taba" Sauke ajiyar zuciya chief yai kafin ya sake furta"please ko da nan gaba kaji kana bukatar abokiyar rayuwa ka sanar dani, zan goyi bayanka kuma zan nema maka dattijuwa dai dai da kai" dariya baba obie yayi "Allah ya kiyaye In auri tsohuwa, Haba owais Ina laifin Yar sha takwas mai jini a jika, wadda zata sangarta ni, kasan mu tsoffi munfison adinga tarairayarmu kamar irin new born baby, Yanzu ni owais idan na auri dattijuwa kamana me zata min"? da mamaki chief ya ago yana kallonsa kai kace ba daga bakinsa kalaman suke fitowa ba. Kafin Ya bashi amsar maganarsa, Wayar baba obie Ta fara ringing, da sauri ya zarota daga aljihu tare da picking call in ya kara a kunnansa. Chief owais sai kallonsa Yake yi har yau yana mamakin tsufan kakan nasa, kwata kwata babu rudin tsufa atare da shi, yana da karfi ga kaifin basira, idanunsa kuwa kona matashi albarka saboda yadda yake gani da su ko bai sanya glass ba, harta sandar da yake rukewa ta gayu ce ba dan ya gaza taka kafarsa ba. "Alhamdulillah Alhamdulillah, almost 3 time baba Obie Ya furta hakan, Hannunsa aya dafe da saitin zuciyarsa alamar Yaji sanyi aransa. "Ina fata kun sauka lafiya, Ubangiji Allah Ya huta gajiya, Ina an jikokin nawa da surukar arzikin Ina fata duk suna lafiya"? Ya tambaya yana sauraron muryar wanda suke magana da shi. "Madallah, naji dadin jin hakan, Hateem ka kula min da kanka, tun da ka haura kabar kasar nan nake ta zullumi duk bayan yan mintina saina duba Onn news inga ko kun sauka lafiya don nasan sune nafarkon da zasu fara buga labarin yadda jirginku yayi landing sai gashi cikin ikon Allah Ka kirani...' yai maganar fuskarsa dauke da murmushi "Muna atare da owais, watakil Ya manta wayarsa agidane, wuni yayi awurina yanzu haka muna a garden. a ma owais wayar yayi"uncle dinka ne ke son magana dakai, kar6i kuyi magana kai masa bangajia jirginsu Ya sauka lafiya...." da sauri chief Ya kar6i wayar tare da karata a kunnansa "My uncle, Ykk Ina fata kun sauka lafiya"? On the other hand muryar prime minister ta amsa da cewa Alhamdulillah Myson, tafiya tayi kyau yanzu haka Ina a bedroom dina dakyar na samu jama'a suka yale ni" "Sunyi kewarka ne, Kai dinne badai farin jini ba, Yar dariya hateem yai kafin ya numfasa Yace"Ina yarona? tun ina a cikin jirgi nake ta tunaninsa, owais Yanzu haka da nake maka magana zazzabi nake ji a jikina saboda kewar sa, ina ta kiran layi ka donka bani shi mu gaisa bana samu" dagowa yai ya saci kallon baba obie Ganin sun ha a iso yasa shi saurin canza yare zuwa larabci saboda baison Yaji me zai furta. "Uncle, zazza6i saboda shi"? "Hmm ba zaka gane ba, dan Allah Ka hadani da shi" Hankalinsa adan tashe Yace"pls uncle, ka daina sanya damuwa aranka, bana jin dadi, na manta wayana agida ne shiyasa baka same ni ba, amma in sha Allah idan na koma zan yi kokarin hada ka da shi ko hankalinka Ya kwanta amma kafin nan pls ka sha magani kada zaza6in yai yawa" "Owais babu wani magani da zai warkar da zazza6in nan kawai ka hadani da shi, saboda shi kadaine warakana" baba obie dake kallon owais ya kura masa ido ba tare da ya fahimci me suke cewa ba. "Okey uncle, zanyi abun da kake so" "Nagode owais, and pls abashi kulawa ta musamman, bana so ya nemi wani abu ya rasa, na yarda dakai kuma nasan zaka Iya min abun da nake so" cikin girmamawa ya amsa masa da toh uncle. Sun an jima suna waya kafin sukai sallama Ya mika ma baba obie wayar, harara Ya galla masa"fadamin me kuke tattaunawa ne naji ka canza yare don kada naji ko" Girgiza kai owais yayi"ba haka bane....." bai are maganar ba, sallamar Hajjaty ta katse su, ba karamin dadi owais yaji ba saboda bay da amsar da zai ba baba obie akan tuhumarsa da Yakeyi Tuni kamshin turarenta Ya gauraye hancinansu, Hannayenta ruke da tray ta shigo garden din, Tea set ne akan tray din tare da fresh
Chapter 67 · 0% Book details