← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 139 OF 247

Sashe 139

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne. auko bowl aya ta juyo tare da kallon Gabriella "Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta are maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta mi a mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu ano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta aga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta bu e wani kwano mai auke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta auki gorar ruwan ta mi a mata, ta kar6a ta sha. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji an dama dama a cikinta. Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ru e na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake? "Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki al awarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba. Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel "Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki etare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta fa a tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita. "Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta aga sandar hannunta tayi mata nuni da wata Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta fa a still da murmushi akan fuskarta. Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve in ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su. "su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data auka a coma.. e hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh. "Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a "Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki" "Toh," "Good girl" ta fa a tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta. "Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta bu e su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata. ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta bu e ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala. ta mi e tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet ta cika kwamun da ruwa mai umi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske. Ta da e acikin ruwan tana umama jikinta kafin tayi wanka ta maida rigarta, ta fito ta zauna kan kujerar, ta dauki storybook ta fara karantawa. Murmushine ya bayyana akan fuskarta, da alama labarin da take karantawa ya faranta ranta, babi hu u ta karanta, ta fara jin kasalar bacci, mi ewa tayi tare da kwashe books din ta nufi book shelves din dakin inda taga khala ta dauko mata su, tana kokarin ajiyesu ta hanka e wasu jerin littattafai dake a shelves tana kokarin tallabe su biyu suka rikito asa, wani irin faduwar gaba ta ji, tsoro ya kamata tunawa da gargadin da tsohuwar tayi mata akan kada ta ta6a komai na dakin, jikinta na kerma ta zu unna tana kokarin tattara books din kamar diary suka an kulle su da makulli tayadda baza'a iya bu e su ba. Akan laps dinta ta daura books din kamar ance ta kalli covers dinsu karaf tayi tozali da hoton abunda ke akan diary na farko, zanan kananun yara ne su uku sanye da jajaye kaya, mata biyu sun sanya namiji a tsakiyar su, kayan matan rigace dai dai gwiwa launin ja, shi kuma namijin riga da wandone jajaye, abun da ya aure mata kai da hoton cover din, duka yaran an daure masu hannayensu da igiya, an toshe bakinsu da jan kyalle, ga hawayen jini kwance kan fuskokinsu, da rubutun larabci aka rubuta sunan books din kokarin karantawa tayi A hankali ta furta sunan shi *sijill al-sujn * bata san menene ma'anar sunan shi ba, janye na farkon tayi ta dubi sunan ayan diary din *t kh sijnil qadar* mi ewa tayi da sauri ta maida su gidan da suka fadowa, ta gyara su dakyau ta yadda ba azagane dun fa o ba, da sauri ta nufi matakalar gadon ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta. ___________________________ *HAJJATY* Safa da marwa takeyi atsakar dakinta, Hannun ta ru e da wayarta, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita, saboda fargaba da tashin hankalin ciwon marwa jiya taga abunda ya rikitar da ita, kusan kwana tayi adakin marwa tana kokarin shawo kanta saboda kukan da takeyi abun yayi yawa kamar zata kashe kanta, hajjaty ga tsoronta da take ji amma ahaka ta daure ta zauna adakinta har saida ta shawo kanta ta hanyar kunna mata karatun kur'ani kafin ta samu jikin marwa yayi sau i har bacci ya auke sannan ta dawo daki, yau tun da safe ta buga ma sheikah imam kira awaya ta sanar da shi halin da marwa take aciki, tace mashi ta kasa gane meke damunta, sheikh imam in yace zai shigo in sha Allah. A yanzu haka shi take jira, ta kasa shiga dakin marwa saboda bata jin dadin ganin ta a mawucin hali, yarinyar ba karamun tausayi take bata ba. Kira ne ya shigo wayar da sauri ta duba screen din wayar ganin sunan sheikh imam ne yasa ta daga da hanzari ta daidata nutsuwarta gurin yi mashi sallama bayan ya amsa mata yace"na iso gidan" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta dauki mayafi ta rufawa kanta, ta zura flat shoes a kafarta, ta fito ta nufi main falo din gidan tasan anan yake tsayawa idan ya shigo. Tunkafin ta karasa ta hango shi zaune kan sofa as usual cikin shiga ta magadan annabawa.. masu aikin gidan dake ta kai komo cikin girmamawa suke gaishe da shi, har abunsha sun kawo mashi da snack, har ya fara shan lemun ya hango hajjaty, mikewa yayi tare da tunkararta, da fara'a tace"barka da safiya malam, ya gida ya iyali" murmushi yayi jin ta tambaye shi ya iyali. bayan sun kammala gaisawa tayi gaba yabi bayanta har zuwa dakin Marwa saida ta fara shiga kafin tayi mashi iso ya shiga daga ciki, a lokacin marwa tana kwance kan katifarta, bacci mai nauyine ya dauke ta sai faman jan numfashi take yi, daga gani awahalce takeyin baccin. "Malam, ni dai narasa gane kanta cikin kwanakin nan, in ta fara kuka kamar ranta zai fita, kuma wlh ina kiyayewa gurin bata maganin kamar yadda ka ce.." tay maganar tana kallon shi. Matsawa yayi daga gaban mattress din Ya zu unna Yana kallon yatsun hannayen marwa da fatar fuskarta,
Chapter 139 · 0% Book details