Sashe 244
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta aukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata aukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a fa uwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......" Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su. Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa ha i da rudanin al'ajabin maganarta. Baba Obie dake a zu unne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan ba ar ranar, gaba daya ya imauce ji yake kamar ya ha a rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya i tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji. Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta fa a tamkar tana yi masu tambaya, aura da cewa, "To wa annan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta fa a a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta. Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh al alamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa." Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka aryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata a bunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasi i bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka aryata tsohuwar nan....!" Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafa unsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya i bata ha in kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa.. "Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu, baba ka yi magana, na ro e ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......" Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan ka ai ya isa yasa ku gasgata magana ta..." Ta fa a tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ru u ru u, jikinshi ya auki wani irin mahaukacin zafi. "Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke auke shi daga gare ku, da ha in bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...." "Zaku haifi a ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su auke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a abari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta fa a cike da takaici, a Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasi in mutumin nan ya da e yana aikata luwa i da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi ka ai ba harda sauran fasi an da suke aikata fasadi a bayan asa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma an naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so ari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...." Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba aramin aga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba.. Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na fa a maku ba arya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...." Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta ji e sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta... "Kamar yadda na fa a maku, bashi ka ai bane Elder, akwai mu arrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da da ewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...." Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar wayar zasu fa asa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo. "Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun addara..." Tunkan ta arasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar ki imar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi.. Runtse idanunta ta yi ru u yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, bu e idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi... Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun addara, mugun fasi i ne....." "Bayan shi sai ba in shaidanin da ta adarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba, shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants in kurkukun addara, baida imani ko mis ala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi mu amin Elder...shish.. Shish..... Kasa arasawa ta yi saboda abun da ya sar e ma oshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata fa i, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin arasa maganar take yi amma ta kasa... Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta ji e jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta fa a, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar wara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi.. Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita asa, ya aura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya. "Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsun ule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..." Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya fa a yana kallon His excellency Deen da ya ha a uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga azafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya fa a yana nuna Obie.. Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta fa a akansa ba arya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....." "In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......" Senate Lateef da ya auko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya fa i a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi ha i da bubbuga jikin shi don ya tashi.. "Ruwa, tana bu atar ruwa..." Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai araso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya mi a masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya bu e su. Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji. Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci aya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi. Kamar mahaukaci haka ya dam i gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan