← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 213 OF 247

Sashe 213

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

yun urin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta. Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....." Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ru ani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!! Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan.. "Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min auki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani" Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yun urin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta... Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfa o da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle an-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta" warin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari. "Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.." Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?" Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta fa a mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a." Gyara zama Benazir ta yi, A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma le en asiri? Har suka riki a suka handame uba da a'yansa saboda yayi masu le en asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!" "To baki tunanin ko halin da nike ciki nada ala a da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai. "Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba aya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min." Murmushi suka sakar ma Juna. "Yanzu ya za a yi? Babu bu atar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun arfe, wara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila. Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..." "Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..." Fuskarta a marairaice ta fa a, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba." "Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi." _________________________________ "Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan awaye In aka ha u ba'a gajiya da fira," Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira." "Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ru e cikin na juna. Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba. "To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a aki." Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana." Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne." "Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki." Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba" "Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku da e dan Allah, zan ma kira Abie dinku in fa a masa" "Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba." A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, bu e motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, arar horn din motar da ya ji ne yasa shi an dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan. Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta bu e backseat, ta auko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School. "Yaya Shureim ina wuni?" Ta fa a da fara'a akan fuskarta, Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?" "Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"? "Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school." Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta fa a tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna. Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta. "Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?" Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya." Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo." Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya." Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?" "Yaya Shureim mu je zamu fa a maka." Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi. _____________________Obie Estate Koda suka araso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga. Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa in Owais, Tunkan su arasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta. Officers shidda ne suka yiwa motar tasu awanya, Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" aya daga cikin su ne ya umarta. Bayan sun fito suka fuskance su. "Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?" Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya fa a fuskarsa a ha e don shi baya son abunda zai ha a shi da masu kaki... "Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya aga ba." Benazir ce ta fa a idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta. Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba,
Chapter 213 · 0% Book details