← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 56 OF 247

Sashe 56

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature ____________________________________ ANEELERH Bakinta auke da sallama ta shiga dakin abie, yana daga zaune gefen gadon shi sanye da farar jallabiya, idanunsa a manne da farin glass, yayin da hannun shi ke a ru e da kur'anin da yake karantawa, sai da yakai aya kafin ya ago yana dubanta tare da amsa mata sallamar da ta yi A tsanake ta shiga ta zauna daga kasan gadon kusa da kafafuwan shi, cikin girmamawa ta gaishe da shi Fuskar shi dauke da murnushi yace"oum junaid, kin tashi lafiya" sunnar da kanta kasa tayi fuskarta da murmushi tace"lafiyalou abie" "Ina jikallan nawa? Maimakon ki tafo min da shi? ko dai rowar an za'ay min ne" cike da jin kunyarshi tace"a'a abie, ni na isa in hana ka jikanka" Murmushi yayi kafin ya Mi a hannu ya auko wayarsa dake ajiye kan side drawer ya mi a mata "Kar6i nan, Ki duba sakon da aka turo miki" da sauri ta sanya hannu ta kar6a, kafin ta aura idanunta kan screen ta soma karanta sakon _Assalamu Alaikum, barka da rana abie an wuni lafiya, ya iyali, awar Aneelerh ce benazir matar tajudeen, Ina son yin magana da ita sai dai bani da contact dinta, dan Allah a hadani da ita, nagode sosai, ku huta lafiya__ Lokacin da ta kai arshen Sakon Idanunta azare, baki a bu e da tsantsar mamaki take kallon screen din wayar, sam takasa gasgata abun da aka rubuta mata, Muryarta asa asa take maimaita sunan Benazir Benazir! Abie dake ta kallon ta, ganin tayi kasa e babu alamun zata motsa ne yasa shi yin gyran murya, kamar wadda aka zungura da sanda a an firgice ta dube shi tana faman zare idanu "Lafiya? Ko bakisan ta ba ne"? Muryarta a harmutse tace"abie, na kasa yarda ne da abun da gani, wannan sakon da aka turo min daga benazir ne aminiyar nan tawa, matar da yau tsawon shekara goma sha wani abu da 6atan ta...." kafin ta are maganar abie yace"kina nufin Benazir yar gidan Alhaji ubaid? Wannan awar taki ta uruciya" jinjina mashi kai tai alamar eh. "To ki kira layinta mana sai ki ji idan itace da gaske" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta mi e ta fuce daga akin a falo ta tsaya kafin ta danna call, jikin ta har kerma yakeyi tsabar zumudin taji idan banezir ce take neman ta. ...... *DAULAR ALHAJI MUSA* Gaba ayan su sun Hallara a kan dining chairs, Tani da lami ne suke dawainiyar yin serving din su, an shake masu table da lafiyayyan abincin breakfast. Tun da suka zauna babu mai magana acikin su, zeenatu da benazir abayane a jikin su, sun daure kansu da head scarp, yayin da Hajiya sarah ta sanya fitted gown ta atampa, kayan sun bi shape din jikinta, sam babu ankwali akanta sai zallar gashin kanta da ya sauko har kan kafadarta, mom layla ma atampar ce ta sanya, Alhaji Ubaid da shureim jallabiya ne a jikin su, Alhaji musa ne kadai ya auki wankan tsadaddiyar shadda launin blue sky, kayan sun zauna mashi abunka ga namijin duniya, yayi kyau sai dai babu annuri akan fuskarshi kamar kullum Ya ha e rai kai kace bai ta6a murmushi ba, tsabar yadda ya aure fuskarshi yana faman shan kamshi kamar wanda iska ke yi ma wari. Abinci yake ci kamar baisan tauna shi, hajiya layla dake kallon shi ji take kamar ta sha e shi saboda haushin shi da take ji. Dr shureim dake cin abinci a tsanake ranshi ne ya bashi cewar Ana kallon shi a hankali ya dago da idanunsa kai tsaye suka shiga cikin na zeenatu, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido aya, da an mamaki akan fuskarshi Ya zaro mata ido da sauri ta sunnar dakai kasa tana cigaba da sakin murmushi, girgiza kanshi yayi kafin ya maida hankalinsa akan abunda Yake yi. Gaba aya Hankalin benazir baya atare da su, ta tasa plate din abinci agaba ta kasa ci saboda tunanin Yarinyar da ta kira ta a daren shekaran jira, tun washe garin jiya take ta kiran layin baya shiga hankalin ta ya i kwanciya. "Benazir Lafiyar ki kuwa? ko wani abu na damunki ne? Tun dazu na lura dake kin kasa cin komai" cikin kulawa mom sarah tayi mata magana. Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace"ba abu nda ke damuna mommy, lafiyana qalou" "Okey, ki fara cin abincin kada ya huce, ba lallai yai maki dadi ba" Amsa mata tayi da toh Spoon ta auka ta soma cin abincin zuciyarta cike fal da tunanin Unaisah Wayar dr shureim ce ta soma ringing daga cikin aljihunsa, Hannu ya zura ya curo ta yana duban me kiran nasa. "Ka tsaya ka kammala cin abincin, Inya so daga baya sai ka yi picking call din" Muryar Alhaji ubaid ce ta katse masa hanzarinta. "Daddy, kira ne mai mahimmanci," "Shikenan je ka daga" mikewa yai a hanzarce yabar dining din Tafiyarsa keda wuya Hajiya layla ta dubi Alhaji Ubaida dake a zaune gefenta tace"ya maganar da mukayi dakai jiya"? Murmushi yadan saki Yana duban fuskar Alhaji musa Yace"ay na fada maki, Ki ara hakuri" girgiza kai tayi"bazai yiwu ba, ni bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba! Wannan ay abun kunyane ace muna zaune gidan kaninka....." maganar na dira kan kunnan Alhaji Musa Ya ajiye spoon din hannunsa, fuskarsa a murtu e Ya ke duban Hajiya layla, yasan tayi maganar ne don Yaji ta. Gaba daya hankulansu mom sarah ya dawo kanta. "dan Allah ki yi shiru ya isa haka! Muje aki mu yi magana" galla masa harara tayi"wallahi babu inda zanje, ko na bika bai wuci ka bani hakuri ba, Ni nagaji da zama acikin gidan nan, gaba aya a takure nake, Kai ko gudun surutun mutane ba ka yi? tsawon kwanaki kana zaune agidan kaninka tare da Iyalinka"? Hankali atashe mom sarah tace"dan Allah kiyi hakuri, mu kammala cin abincin sai muyi magana...." kafin ta are maganar Alhaji musa Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tuni taja baki tayi shiru. Jikin zeenatu harya fara yin kerma saboda batason tashin hankali arayuwarta, abun ka an ke rikitata, ita dai benazir ba ta ce komai ba ta zuba ido tana kallom mommyn nasu dake ta faman tada jijiyoyin wuya. A gadarance Alhaji Musa Yace"Bana son haniya" Harara ta watsa mashi"ay idan baka fita harkar mijina ba, hayaniya yanzu ka fara jin ta, wallahi bakaso zaman lafiya ba, akan me zaka dinga juya mutane son ranka sai kace wasu bayin ka, komai sai dai ka bada umarni abi, to wlh bazan lamunta ba! Hakuri na Ya are, idan shi ka rufe masa baki to ni baka isa kayi galaba akaina ba!" ta fada tare dakai hannu ta bugi gaban table da karfi, kafin ta yunkura ta mike tare da kallon Alhaji ubaid. "Ni zan tafi, tun da naga kai baka da niyar barin gidan," mayar da dubanta tayi ga benazir"tashi mu tafi" jiki asanyaye benazir ta mi e, nan take zeenatu ta fashe da kuka tana fadin"Inna lillahi mom layla dan Allah kada ku tafi, wallahi banso, mommy kada ki bari su tafi, daddy kace masu su su yi ha uri su zauna, ko kuma su tafi da ni" Hankalin Tani dana lami ba karamin tashi yayi ba, ganin rikicin dake shirin 6allewa. Wani irin tausayin ta ne ya kama benazir sam batason ta rabu da yarinyar sai dai ba yadda zatai dole tabi umarnin mahaifiyarta. Da sauri Alhaji Ubaid Ya mike muryarshi da 6acin rai Yace"haba layla menene haka? Yanzu abun ki kai kin kyauta? Mutane suna zaman su lafiya kin tarwatsa masu farin cikin su" Dakatar da shi Alhaji musa yai, Cike da isa Ya mike tare da kallon fuskar Hajiya layla dake huci. "Ga hanya nan ki tafi, Allah Ya raka taki gona" bayan ya furta hakan Ya juya azafafe Ya nufi bedroom dinsa Yana shiga ya dauki wayarsa, Call Ya danna tana fara ringing akayi picking Muryarsa akausashe Yace"kada ku bar kowa ya fita daga gidan nan Idan Har bani na baku umarni ba"! On the other hand Muryar wani basamuden mutun ta amsa mashi da cewa "Angama Yalla6ai" sauke wayar yayi "Haba dear, why ba zaka bari su tafi ba, na fa ji kiran wayar da kayi, meyasa zaka rike su? Tun da matar nan ta nuna bata son tafiya to ka yale su su tafi mana," muryar mom sarah a kule tayi maganar tana duban bayan shi... Tamkar tayi magana da bango, babu alamun zai juyo ya fuskance ta balle harya amsa mata, Rai a6ace ta dawo ta gaban shi ta tsaya idanunta cike tab da kwalla ta furta"magana fa nake yi maka....." da bu ar bakinsa sai cewa yai"Toh Uwata Ina sauraron ki" ya fada yana ru e qugunsa, Idanunsa akan fuskarta, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin shakkarshi, sam takasa cigaba da yin maganar. Gefen wuyanta ya shafa da tafin hannun sa"sau nawa zan ja maki kunne akan ki daina shiga abun da ya shafi dangina!" cikin sanyin murya tace"bazan ara ba" Jinjina kanshi yai, kafin ya ara furta wata maganar, Muryar zeenatu ta kara e kunnan su. Shigowarta kenan dakin ko sallama babu, Muryarta da shesshekar Kuka take fadin"daddy dan Allah kada ka bari su tafi, ni ban gaji da ganin su ba, ko kuma ka bari na bi su mu tafi a tare" Juyawa yayi tare da daura idonsa akan ta, fuskarta tayi jawur hawaye na sintiri kan kuncinta. a mata hannu yai da sauri ta nufe shi, hugging dinta yai tare da aura hannunsa kan bayanta yana dan bubbuga shi cikin sigar lallashi. "Ya isa, Ki daina kuka My daughter, ko dan saboda ke bazan bari su tafi ba, dolensu ne su zauna gidan nan ko suna so ko basa so" sauke ajiyar zuciya zeenatu tayi jin abunda yace, Hankalin ta ba karamin kwanciya yai ba, Hajiya Sarah ta kasa furta komai, Jikin ta yai mugun sanyi musamman yadda Taji Alhaji musa Yana magana da gadara babu a'a a kalamansa.... A fusace Layla Ta nufi dakin ta, bayan tace da benazir taje ta ha o
Chapter 56 · 0% Book details