← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 49 OF 247

Sashe 49

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 6 min read

"Zan kaiki in sha Allah, amma ba yanzu ba, ki ara hakuri" tur6une mashi fuska tayi, bakinta cunkushe da abincin daya tura mata, yar dariya yai tunawa da kuruciyarta. "Banji kin tambayeni danejo ba"! Sakin fuskarta tay, "tana araina daddy, bazan ta6a mantawa da halaccinta agareni ba, ni dai ba abun da zance sai dai inyiwa Allah godiya saboda Ya hadani da mutanan kirki masu sona tsakani da Allah' ta fada fukarta da an murmushi, "Yaushe zaka kaini Wurinta in ganta"? "Ko zuwa anjima idan kika kara jin sauki sai muje ko"? Daga mashi kai tay alamar eh. Shiru suka dan yi kafin ta kuma cewa"daddy mommy adama fa? da uncle abdallah!! Suna nan suma"? Daga mata kai yai alamar eh, "Alhamdulillah Ya Allah" ta furta da matsanancin farin ciki, ashe da rabon in sake ganin yan uwana. "Ina granny ina da sauran mutanan buzaye" Jiki asanyaye ya ajiye cokalin dake a hannun shi, nan take ta fahimci babu lafiya, muryarta adan rude tace"daddy menene"? Cikin sanyin murya yace"unaisah sun riga mu gidan gaskiya, mahaifina da mahaifiyata, da kuma kakata kusan duk a lokaci aya suka rasa rayukansu nima sai daga baya naji labari..." Cikin sanyin murya tace"ubangiji Allah Yajikansu ya gafarta masu, Allah ya jaddada rahama agare su..." amsa mata yayi da ameen Shiru suka danyi na wani lokaci batare da ya cigaba da bata abincin ba So take ta tambaye shi dangane da mahaifiyarta sai dai takasa saboda zuciyarta taki bata hadin kai, Har yanzu bata daina jin acin radadin abun da tayi mata ba, ta tsani mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan, tana son ta ha u da ita ba don komai ba sai don taji dalilin dayasa ta yi watsi da ita, idan ba ta son ta meyasa ta haife ta *HAJJATY A zaune take gaban dressing mirror, fuskarta dauke da murmushi bakomai take tunawa ba face fuskar Naufal, ta kasa mantawa da shi, Yaron ya kwanta mata aranta, daren jiya data kwanta bacci har mafarkinsa tayi, da alama bata jima da fitowa daga wanka ba, duba da towel din dake daure a chest dinta Tun dazu takasa tabuka komai gaba daya ta shagala da tunanin naufal, ta osa pravin ya shigo donta nuna mashi hoton naufal tasan zaiyi mamakin ganin me kama da ita. Wayar ta dake ajiye kan mirror din ta dauka ta budo hoton shi tana kallo har zooming din fuskarsa take yi Jin motsin shigowar mutun yasa tayi saurin juyawa don ganin wanene Pravin ne ya shigo sanye da farar jallabiya, fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin kamar wanda aka fada ma sakon mutuwarsa Sam bata lura da yanayin shi ba, cike da zumudi ta mike ta nufe shi tana fadin"honey, ina ka shiga tun jiya bansaka a idanuna ba"? Fadawa tayi kan kirkinsa tai huggin nasa kafin ta ago da fara'arta tace"ka yi shiru baka ce min komai ba"? Wani kallo ya soma jefa mata mai kama da harara, da alama ta manta abunda tayi mashi jiya shiyasa ta za e tana shige mashi Ganin baida alamun yi mata maganane yasa tace"fadamin baby, ko dai hajiya saratu ce ta 6ata maka rai"? Banza yai da ita baice uffan ba.. Murmushi tadan saki"nasan itace ta bata maka rai, bari na nuna maka wani abu nasan zakayi farin ciki idan ka ganshi" ta fada da sauri ta nufi mirror Goya hannayensa yai akan kirjinsa yana jiran karasowarta. "Baby, duba ka gani, jiya a wurin taro bayan tafiyarka naga wannan yaron mai kama da an mu Naufal kyakkyawan gaske" cikin annushuwa ta mika mashi wayar don ya kar6a ya gani, rai amatu ar 6ace yakai ma wayar bahagon naushi tayi sama ta undumo kan tiles ta bada wani sauti mai karfi. idanunta azazzare ta dago tana kallon shi, Huci yake yi tamkar mayunwacin zaki Ya furta"kin manta abunda ki kai min jiya"? Dafe kai tayi da hannu daya idanunta tuni sun cuko tab da kwalla, ranta abace tace"pravin! Meyasa zaka jefar min da wayata? Laifin me nayi maka? Saboda kawai naki bin umarninka? Wai meke damunka ne pravin? Agaban mutane fa ka ruko hannuna kaja ni zaka fitar dani daga hall tayaya bazan ki binka ba? Ko so kake afara zargin mu ? Kafin ta are maganar Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, nuna ta yai da yatsan hannun shi"yi min shiru! Bana son jin komai daga gare ki, ashe harni ban isa in baki umarni ki bi ba! Hankalin ki ya kwanta Kin kunyata ni a idon jama'a..." hawayene suka soma sintiri akan fuskarta, muryarta na rawa tace"pravin ka fahimce ni mana, kasan bazan ta6a kin bin umarnin ka ba, hakanan batare da kwakkwarar hujja ba! Ni nayi hakanne saboda bana so wani ya tuhume mu..." yatsansa ya daura kan la66anta, shiru tayi tana kallon shi Can kuma ta fashe da kuka tasa hannu ta ture yatsan nasa tana fadin"baka kyauta min ba, Tun jiya nake zumudin in nuna maka hoton sajeed Yaron dake kama da danmu amma shine ka fasa min waya..."? Ta6e la66ansa yai kafin ya furta"ki yi hakuri rainane ya 6aci, " ya fada tare da zukunnawa ya dauki wayar yana fadin"zan siya maki wata" "bana so, ni dai ka gyaramin tawa, saboda bana son na rasa hoton sajeed" Harara ya watsa mata tareda cewa"meye alakarki da shi ne? Kawai daga ganin yaro yana kama dake? Mutun nawa kika sani suna da masu kama dasu a duniya? Kamar kanki farau" "Ni wannan bai dameni ba, Ina son shi saboda inajin shi kamar ana dana rasa" Rai a6ace ta fada kafin ta juya ta koma kan gado ta zauna, tana cigaba da matsar kwalla Murmushin gefen fuska pravin yasaki Yana dubanta, Komawa gefenta yai ya zauna bayan ya ajiye wayar ya ruko hannunta acikin nashi "Look, bana so ki sanya damuwa aranki, idan har rashin naufal ne ke damunki, nayi maki alkawarin nan bada jimawa ba zaki haifi wani babyn, sai ki sanya mashi sunan naufal din" Wani kallo ta jefa mashi batare da tace mashi ala ba, lallashinta Yacigaba dayi duk don ya samu yashawo kanta. HAJIYA SARATU _safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abunda Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanu arta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu warin gwiwar yi mata haka? ru e qugu tayi da hannu aya fuskarta babu annuri_ *Daga Al alamin Boss Bature *Littafin kurkukun addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 18 Complete Novels Elite Admin June 12, 2024 Novels Elite English _*~ BOSSLADIESWRITERS
Chapter 49 · 0% Book details