← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 211 OF 247

Sashe 211

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

da take kwa ayin ta hada ido da shi. Har yanzu Danish Yana aranta sai dai ta rage damuwa da rashin shi, ta dauki dangana tama fidda rai da shi, saboda ya taba fada mata bazai iya tafiya yabarsu ba, tabbas da ace yana a raye da tuni ya dawo gare su amma yau har one month shiru babu alamun shi. Abu daya da bata fashi shine yi mashi addu'a har yau bata fasa tashi tsakar dare tayi nafilfili saboda shi ba A bangaren yan uwanta dake a part din Taj Har yau basu san meke wakana ba, abu biyu ne ke damun su, Kulle su da akayi a part din taj da kuma rashin dawowar su Unaisah Part din, amma saboda yawan kiransu video call da sukeyi Yasa hankalinsu Ya dan kwanta In suka bukaci suna son yin magana da Danish ita keyi masu wayau ta gyara muryarta ta koma irin tashi da yake ta kware gurin iya kwaikwayon muryar Danish Ba zaka taba gane ba shi bane, Ta hake take shawo kan su, ko da sun nuna suna son suyi video call da shi sai tace masu sun manta Danish baya kallon camera? In ta fadi hakan sai suce eh sun tuna fa. wani sa'in kamar zasu saka mata kuka su dinga mata magiya akan su dai suna so su dawo nan su zauna atare da su, tace su kara hakuri suma suna jirane sai su Danish sun tafi sai su dawo nan. Alhamdulillah duk da suna a kulle part din Taj suna samun kulawa chief bai barsu hakanan ba, ya sanya masu duk wani abu na more rayuwa da zai shagalar da su ya kawar masu da damuwarsu, Basu da matsalar komai, Hutu kawai suke sha, rana ta farko da Unaisah tayi video call da su saida ta yi mamakin ganin yadda Kumatun parveen suka cuccuko, sunyi kiba sunyi haske kamar ya'yan turawa, Duk in zasu yi waya sai sajeed Ya tuna mata akan ta fada ma Danish Yar uwarsa dake a prison dan Allah kada su manta da ita su taimaka su auko ma shi ita... __________________________________ Idan Muka Koma Obie Estate tuni sun fara shirye shiryen Bithday din Owais da family meeting kasantuwar saura kwanaki kalilin ya rage, prime minister harya kira baba Obie awaya ya fada masa ranar da zai shugo Nigeria yakuma ce su fara shirin tarbarsa. saboda gabatowar ranar Baba Obie Yasa aka fara gyara Estate Din tare da awatasa yadda kasan Masarauta saboda kayan alatun da aka wadatasa da su. A bangaren Hajjaty tuni tayi watsi da maganar Marwa, kuma tayi blocking contact dinta saboda bata bukatar ta karajin koda muryarta, tun da tayi ma Praveen kazafi taji ta fita aranta. BENAZIR A Zaune take kan Mirror chair, Hannunta ru e Da wayarta, hotunan Unaisah take kallo Idanunta sun cuccuko tab da kwalla, Baiwar Allah Hankalin ba akwance yake ba, ta damu da rashin samun su awaya, In ta kira Unaisah kiran baya shiga, shi kuma, Taj ko ta kira baya picking sometimes rejecting call din yakeyi har sako ta tura ma sa tace dan Allah idan ma bazai kula ta ba, ya hada ta da Unaisah tana son yin magana da ita, shiru bai kirata ba kuma bai mayar mata da reply ba, ta rasa ina zata tsoma ranta taji dadi! Gashi since last da sukai waya da Unaisah Bata kara bacci Cikin kwanciyar hankali ba, saboda munanan mafarke mafarken da ta ke yi akan ta da kuma tana ji aranta wani abu na faruwa da su, Har tunanin zuwa estate din ta yi sai dai tasan Ba lallai ta samu hanyar shiga ba ko da taje, tunda ba wani gareta ba, Taj da take takama da shi baya kula ta amma tasan indai ta nemi Anila da maganar zata taimaka mata suje tunda dama ita ta hadata da su kuma ta san Taj yana ganin girman Aneela. Kifa kanta ta yi gaban mirror tana shesshekar Kuka. "Aunty Benazir" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu, Kasa dagowa tayi saboda bata son yanayinta ya jefa zeenatu a hali na damuwa Shigowa dakin zeenatu tay, jikinta sanye da jallabiya fara. Ganin Benazir zaune ta kife kai gaban mirror yasa ta nufe ta. "Aunty Benazir, lunch is ready, we're waiting for you" ta fada tare da karasawa gaban ta. Jin shiru bata dago ba yasa zeenatu tayi tunanin ko bacci ta ke yi. Dafa bayanta tayi"aunty Benazir, Wake up pls, " taji tayi shiru bata tanka mata ba. tasan in har ba magana ta yi mata ba, ba tafiya za ta yi ba, a yanzu bata son kowa a kusa da ita tafi son kadaici. "Zeenatu! Pls ki kyale ni, basai kun jira ni ba, Ki tafi kawai ku ci abincinku," ras gabanta ya dan fadi jin yadda Benazir take magana cikin shesshekar kuka arude ta furta"Aunty Benazir! Meke damunki? Baki da lafiya"? Bata san sa'adda ta daka mata tsawa ba"bansani ba, Zeenatu! Nace ki kyaleni, Ki rabu dani, bana son ganin kowa akusa dani..." zazzare blue eyes dinta tayi, abunka ga shagwababba ta fashe da kuka ta juya ta fuce da gudu ta nufi dining area. A lokacin Mami da Hajiya sarah tare da Dr shureim da Alhaji Ubaida suna azaune kan dining Chairs har sun fara cin abincin, Kukan zeenatu ne yaja hankulansu ga dubanta, azabure suke mike suna kallonta, Ta na karasawa ta fada jikin mommynta tana ci gaba da kuka, Hankali atashe suka dubi juna kafin suka maida idanunsu akanta. " Zeenatu meya faru? Ina Benazir din? Wa ya tabaki"? Alhaji ubaid ne ya tambaya. Mami tace"ki bude baki kiyi magana mana! Wani abunne Ya hadaki da Benazir dinne"? Dago da ita Hajiya sarah tayi"Daughter, Daina kuka, Fada min meya faru"! Cikin kula tayi maganar tana share mata hawayen fuskarta Cikin shesshekar kuka tace"Ah.. an.. aunty Benazir ce take kuka, Nace tazo muci abinci shine ta daka min tsawa tace in tafi bata son ganin kowa a tare da ita" Dr shureim bai tsaya ya karasa sauraron maganar Zeenatu ba, Ya zame jiki Ya nufi dakin Benazir tunkafin Ya karasa shiga Ciki yajiyo sautin kukanta, gabansa na faduwa ya afka ciki Ta cikin madubi Ya hango fuskarsa sharkaf da hawaye ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa gata a duniya, da sauri ya nufe arude ya furta Benazir! Lafiya kike kuka? Meke damunkin ki ne? mikewa tayi ta nufe shi ta kwantar da kanta saman kafadar shi tana kuka, bubbuga bayanta ya somayi da hannunsa cikin sigar lallashi yace"pls ki fadamin damuwarki, Zan taimaka maki mu nemi mafita, amma kukan nan bazai amfane ki da komai ba, saima yajaza maki ciwon kai" dakyar ta hadiye kukan tace"yaya shureim ina ma mutuwa zata zama hutu agareni wlh dana mutu na huta, nagaji nagaji da azabtarwar da zuciya keyi min akan rashin mijina da yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar.. Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali.. Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi. "Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana" Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya. Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi. "Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..." gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su.. A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa. Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..." ta fa a tana matse kwalla. Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take. "Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce.. Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta. Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata. Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou" "Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya. Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ru e da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki. "Ki je ki ci abincin ki" Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh. Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"? "Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta." "Da yaushe"? "Ko yanzu kace
Chapter 211 · 0% Book details