Sashe 229
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta. "Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ato abinci?" Ya fada tare da age mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa. "Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi. "Yakamata ki tafi suna jiranki." an bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?" "Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini al awari?" Jinjina mata kai ya yi. "Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya an yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi. ________________________________________ Around arfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ru e da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya auracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta fa a masa abunda ta kasa sanar da su azu, sai dai tana matu ar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin u ubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji wara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yun urin kashe ta ba. Tana arin juyawa ta koma aki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta fa a bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga le en shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar akin. A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gya a kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma aya da zata furta ne. aura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar san a ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya. har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet. Gaba daya kanta ya aure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta da e da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba. Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking. Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi. Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a an 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi. Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa. Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?" Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.." Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani," Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi. ( Allah sarki tsohuwar Zuma har wani ara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.) "Ina babynmu?" "Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci" "Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?" Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..." Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah" Calmly Ta soma ba shi labari. "Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe aya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga akina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya asa kasa kamar baya son wani ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan aya daga cikin kujerun sha atawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin san a na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi. "Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin ha a ramin ku auko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba asusuwan shi a cikin ramin" Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi. "Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran," Ya fa a tare da yin rejecting call din ganin ya mi e yasa na yi saurin zu unnawa asa da rarrafe na dinga tafiya cikin san a sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse. Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a ha a ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba asusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?" A lokacin gaba daya na ru e, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana. Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi. Benazir ta aura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ulla mata makirci a asar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka fa a mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma aki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce. Amma abun da ya aure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne arsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba? Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi. Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya