Sashe 203
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
bayyana kaina agurinki da nima na samu gurbi acikin zuciyarki, sai dai kash na makaro amma har yanzu ina da sauran dama Unaisah, nasan kun shaku da juna ke da shi, kun sha wahala a tare, kun yi rayuwa a guri aya, kun san sirrin juna, nikuma bansan komai dangane dake ba, amma idan kika bani dama nayi maki alkawarin zan canza maki rayuwarki...." da wata irin siga ta jan hankali yai mata maganar, har saida taji wani irin yanayi atare da ita, kalamansa sun ta6a zuciyarta. agowar da zatay keda wuya karan hancinsu ya gogi na juna razanar da ta anyi ne yasa ta aga afa zatay baya aikuwa gaba daya ta tafi zata kife kasa saboda rashin kwarin jikinta. Cikin zafin nama yai hanzarin damko waist dinta Ya janyota gaba daya ta fada kan broad chest din shi, wani irin faduwar gaba taji, She could feel his heart beating rapidly, lumshe idanunta ta danyi sam ta kasa motsawa daga jikin shi, ta rasa gane me take ji? Amma tabbas taji wani irin sanyi da kwanciya hankali yana ratsa zuciyarta. har ga Allah bai janyota da wata manufa ba, gudun kada ta fadi yasa shi rukota sai kuma abun ya nemi ya jefasa a wani yanayi mara misaltuwa, nutsuwa yai yana kallon fuskarta tay lamo a jikin shi kamar jinjira. Damuwar rashin Danish ta fara affecting brain din ta, komai ya faru Danish take gani a yanzu haka ji take kamar a jikin Danish ta fa a shiyasa ta kara narke masa. abunka ga mabukacin dake bukatar duk wani abu da zai sanyaya mashi zuciya. "Unaisah" shiru bata amsa mashi ba. "are you sleepy? Ya tambaya yana leken fuskarsa. Still bata motsa ba, Batool ce ta fara mutsu mutsu kamar zata farka, hakan yasa shi raba ta daga jikin shi ya an jijjigata dakyar ya samu ta bu e idanunta wadanda suka ka a jawur kamar an watsa masu barkono. "Muje ki kwanta" kamar gunki tay shiru babu alamun zata aga afarta, kamar bata jin me yake cewa. Sungumarta yai kan Shoulder inshi Ya nufi bed da ita, Cikin kulawa ya kwantar da ita.. "Kada Ki kwana Da hijab a jikin ki, Ki cire sannan ki yi addu'a" sai lokacin ta dan jinjina ma shi kai. Ajiyar zuciya ya sauke kafin Yai hanzarin juyawa ya fuce daga dakin. Sai bayan daya fitane ta samu kanta, maganganunsa ne suka dinga yi mata yawo akai a haka har bacci mai dadi yai awon gaba da ita. "ANEELEERH ba ita ta tashi farkawa ba sai wuraren arfe hu u na dare dayake tasa abun aranta har mafarki saida tayi, idanunta biji biji ta bu e su ta dubi agogo, kafin ta curo wayar daga chargy harta cika, Kunna wayar tayi Haskenta na kawowa taga abunda ya karya zuciyarta hoton Ana ne da baby junaid akan wallpaper dinta sunyi murmushi a hoton. Bata samu wayar da password ba, lalube ta cigaba dayi mata ta shiga whatsapp dinta, tana tsaka dayin scrolling ta fada Archived anan taga wani Group da Ana ta bude ita da sisters dinta,, Shiga ciki tayi ta soma karanta firarsu. _sister, ke da kike zaune cikin rufin asirin Allah, meyasa kika ce kin gaji da zama gidan? Bayan irin sabon da kikayi da Aneelerh, gashi muma ta silarki mun samu taimako a gurin ta_ _ba zaku gane ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, bawai don son raina nakeso In bar gidan ba, kawai hankalina ba akwance Yake ba, ni dai kawai inaso nabar gidan ne_ _kinga in wani abu ke damunki, ki fada mana, mu nemi mafita a tare_ _kada ku aga hankulanku, babu komai, kawai inaso nadinga ganinku kullum akusa dani, saboda kuka dai ne dangin da kuka rage min a duniya_ _idan kina so mu dawo kusa dake, toh ki sama mana aiki anan abujan mana, sai mu dawo, muma munfiso mu zauna kusa da ke_ _bazan bari ku dawo nan ba, sai ni kusa ma min aiki in dawo nan_ _meyasa_ _nafison zama a Jos din fiye da nan_ Dakatawa Aneelerh tayi da karanta sakon, aranta ta ayyana meyasa Ana take gudun zama abuja? Bayan kafin zuwansu tafi kowa daukin zasu dawo nan"! Girgiza kai ta danyi kafin ta yanko wata firar tasu ta ci gaba da karantawa.. _janet tace"Ana! Kina cikin hayyacinki kuwa? Meyasa kike magana kamar wata musulma"? esther tace"Na fara zarginta, cikin kwanakin nan kullum in zakiyi magana a group chat dinmu sai kin sanya mana abun addinin musulunci bayan mu ba musulmai bane_ _Voice note ta tura masu"nagaji da 6oye maku da nake yi, ku yan uwana ne babu wani sirri atsakanin mu, nasan zaku goyi bayana" su kace muna sauraronki"Na musulunta, Yau wata biyu kenan, amma babu wanda ya sani, ko Aneelerh ban fada mata ba, A boye nake yin sallah ta"_ _"Dagaske kike ko wasa" janet ce ta fada_ _"Na ta6a maki wasa irin wannan"? Janet tace"a'a"_ _Ana Tace"toh, Dagaske nake Ana inku Yanzu musulmace ni, na yi imani da Allah kuma nayi imanin cewa Jesus da muke bautamawa bawan Allah ne kuma manzon sa ne"_ Esther tace"nagaza yarda Ana, kamar dai kin haukace, taya zaki bar addinin iyayen mu da kakannin mu"? _Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta ka aitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_ wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta ra a masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi. Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar. taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi. yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala. Bayan ta sallame sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta. Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta mayar da hankali akan videon.. wani irin fa uwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati... tsabar ki imar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi. Yana bu e idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun ka a jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..." Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba. "Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe. lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin. da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da an mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya oke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye. Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka" Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito" gaban faucet taje ta wanko fuskarta