Sashe 243
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
broad chest dinsa, ya ameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da a kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya ha u da na juna. "Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta fa a a ru "Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen. "In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar . Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya fa a tare da nuna baba Obie "Saboda na fara kokwanto akan shi! kuma dama shi borin kunya da hauka ake na e shi, in ba haka ba meyasa zai aga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya fa a yana jifar shi da kallon tuhuma. Bai arasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya mi a hannu da niyyar ya dam o ta, Sharafuddeen ya yi saurin dam o hannunsa ya jefar da shi gefe aya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi. Gabansa ne ya yanke ya fa i jin yadda Sharafudeen an cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!" "Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka aga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya fa a yana kallon cikin idanun shi. Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face, Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi. nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya fa a yana dafe kanshi da tafukan hannayensa.. "Baka ga komai ba Obinna...." Tsohuwar ce ta fa a tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani antaccen kallo mai cike da tsana.. "Dama bana fa a maka ba akwai ranar in dillanci? Shin ban fada maka duk min daran da ewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana aya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...." Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun ka a jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.." Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na ro e ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da a na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...." Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi. Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun aga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona. "Lokacin da na dinga ro onka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ashe babu igon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?" Ta fa a tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ru afafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki al awarin zan shiryu..." cikin jin unar rai ta ha iyi yawu mai aci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta da e tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma ya i ji yanzu wa gari ya waya? "Dan Allah ki fa a mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki fa a mana, kun aga mana hankali, Kun ru ar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki fa a mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki fa Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta fa a su da farin ciki har abada, watakil ma ba in cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su. Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba. Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi ha uri! ku yi ha uri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan fa a, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...." Ta fa a da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala ha ika sun jefa shi a ru ani. "MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ADDARA? ANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina aya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu le en asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....." Bata arasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, " aryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...." Bai are maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai sha e wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar dam e wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma azafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? an kungiyar asiri???" Ya fa a yana zare idanunsa da suka ka a jawur. Cikin jin unar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai umi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...." Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu azafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya fa a yana nuna su Hateem. Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai ha e da fa uwar gaba ce ta arsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka ha ikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi. Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa fa ar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya da e yana munafurtarku...." an dakata tana jan numfashi, sai arin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba aramin da i ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana. "Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa