← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 19 OF 247

Sashe 19

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 6 min read

ga wasu jerin Crystal glasses an uban su masu aukar ido, bayan su kuma akwai Silverware and napkins with table ware a kowani dinner table hada menu card ajiye bisa tables din, komai fa ya tsaru ga wasu Crystal Sparkling chandiliers masu haskaka tsakiyar akin taron da wani irin twinkling lights hakan ba aramin awata akin taron yayi ba, ga wata ni'ima dake kur owa ta cikin na'urorin A.c mai ratsa sassan jikin mutun, idan muka koma 6angaren abun da za'aci hohoho duniyar dadi wato daga can 6angare guda dinner buffet ne jerin nau'ikan abincine da aka killace su a cikin chafing dishes wato wani irin aroma ne ke tashi na dadda an kamshin abinci mai cika makoshi, ga jerin large glass bowls na kayan marmari da zungura zunguren glasses na Juice masu sanyi komai fa an tanada, babu ce kadai ke babu a dakin taron, anyi 6arin dollar, naira kuwa ta raina kanta a wurin, dukiyace aka narkar wurin awata ko'ina, idan kuwa nace zan fayyace komai dake a hall din tabbas zamu are takun karshe ne wurin kwatanta haduwarshi shiyasa na takaita da bayani don mu shiga kaitsaye cikin taron. Sannu a hankali dan ara dan aran motocin su na alfarma zubin Mercedes benz S. Class suka soma shararowa izuwa cikin garden din a jere suke tafiya yayin da jami'an sojojin dake take masu baya suke bin motocin da kafafuwansu suke tafiya gefe da gefen su, hannayen su ru e da jibga jibgan bindigu ga wasu kuma soke a qugunansu sai faman mazurai su ke yi, tamkar a filin daga. arasowar motocin ke da wuya A hanzarce Sojojin suka bu e back seat na motar farko, A hankali sheikha mujeedat ta zuro kafarta dake asanye cikin hadaddun takalman alfarma wadanda kudinsu kadai ya ishi wani talakan jari, kafin ta arasa fitowa tabarakallahu ahsanun khalikin gaba aya sojojin dake a wurin saida suka saki baki kamar lehen sakarai saboda tsabar kallon ta a fakaice. Embell ished abaya ce a jikinta launin royal blue anyi mata adon stones work, fuskarta tana asanye da Gold chain mask, adon dake akan fuskarta ka ai abun kallo ne, tayi masifar haduwa, daga asa har sama ta ca6a ado nasu na sarauta tamkar awisu a fagen ha uwa, bata jima da fitowa ba, jami'an suka budewa Prime minister hateem other side din motar ya fito tamkar tauraro a cikin taurari yayi shiga na mutunci, hadaddiyar shadda ce a jikin shi gezna launin blue anyi amshi senator style abun ka ga dogon namiji ga kira kayan sun zauna mashi kamar a jikin shi aka dinka su, wata expensive watch ce a hannunsa sai kyalli take tana daukar ido, Yatsun hannunsa na sanye da zoben azurfa mai shegen kyau, sumar kannan tashi tasha gyara har ta gaji da haduwa, Bayan fitowarsu motar dake abayansu tasu Yazrin da Nazli ce, Lokacin da suka fito Kiris Ya rage zuciyoyin wasu su buga saboda tsabar haduwar wankan dasuka dauka na emirati abaya launin Silver, kowaccensu ta manna glasses a idanuwanta, ga adon gold knucles rings dake a yatsun hannayensu, sun yi rolling veils a kansu yadda kasan asace su saboda kyau. Bayan fitowar su Nazli, sojojin suka cigaba da bu e ma sauran motocinsu, gaba aya zaratan samarin family din maza da iyayensu ankon shadda gezna su ka yi, matasan an matan kuwa arab abaya suka sanya masu kyau da tsada na alfarma na kuma kece raini da fita tsara, wasu sun sanya lace abaya, wasu embellished abaya wasu open front abaya, wasu kaftan abaya, wasu egyptian abaya kowa da kalar nashi wankan, kowaccen su tayi lagin gyale akanta, wasu ma babu gyalen zallar sumar kansu ce har gadon baya kamar indiyawa, duk wadda ka kalli wuyanta zaka ganshi manne da ziririyar sarka ta diamond wasu kuma ta zinari, gayu mutanan Allah, Hajiya saratu fa ta dauki kur adakanta rantsastsiyar dubai abaya ce a jikinta tsadaddar gaske launin maroon rigar harta gaji da haduwa abunka ga manyan mata masu dirin jiki kayan sun ladabtu a jikin su kamar donsu aka kera su, kwansu da kwarkwatansu suka jera izuwa cikin hall din, iyayen su maza kowannansu yana ruke da hannun matarshi, wani irin dadda an sautin ki e ki e da raye raye ne ya kara e ko'ina na akin taron, Hada wani irin busa tamkar na sarewa Suna tafiya suna taka rawar dattako, cikin nishadi da raha, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki da annushuwa. Prime minister Hateem ne yafara shiga hannun shi ru e dana gimbiya mujeedat, daga bayan su Nazli da Yazrin ne, bayan su sai Mai girma sharafuddeen shima ya shiga hannun shi ru e dana gimbiya malikat, ayan hannun nashi ya ru o hannun uwargidansa Hajiya laurat daga bayan su Chief Owais ne wanda zan iya cewa shine farkon haduwa saboda kyawun surar shi, Shaddar jikin shi ta bayyana zazzafan kyanshi kamar shi ya era kanshi, hannun shi yana a ru e dana kanwarshi Hindu itama ta dauki wankan abaya. Bayan wucewarsu Sir mubarak Ya shigo hannun shi ruke dana Mom turai, daga bayan su Zaki ne tare dr Jazz sai Ibad. Fuskar kowan nan su da fara'a, bayan shigarsu Senate lateef ya shigo shima tare da Mom madina hannun su ru e dana juna, Yayin da zulaihat da Ziyad suke abiye da bayan su. Abun gwanin ban sha'awa, bayan suma sun shiga His excellency abdul Razak ya shigo tare da her excellency Muhibbat, suma sun dauki nasu wankan, atare da ya'yan su suka shigo Captain Yaseer da Yusra. Daga su sai His excellency Deen Ya shigo fuskar nan awashe da annuri yayin da yake a ru e da hannun her excellency Hajiya Jameela, daga bayan su Dr nawaz ne da an uwansa justice Nadeem sun dauki nasu adon. Basu jima da wucewa ba, Hajiya saratu tamu ta mutunci ta shigo hannunta ru e dana Pravin sunyi matu ar ha uwa abunka ga ba'indiye shaddar tayi mashi kyau. Daga bayan su Twins ne zayn da zayn wohoho wanka Yabi jiki, na madina masu kamshin zamzam tsayawa fasalta kawunsu a cikin shadda 6ata baki ne, Hannayensu na ru e dana kanwarsu Faryat, ta ca6a uban ado ciki riga red colour duk matasan wurin babu wadda tayi shigar fitsara irinta, abayar jikinta ta matse kirjinta, ko arzi an kwalli babu akanta sai zallar kitson kalabarta, gaba dayan amshin turaren su ya gauraya da na iskar A.c wata irin ni'ima ke tasowa. Har sun nufi inda aka tanadar masu kowa ya nanna e rigarsa zai zauna, kamar daga sama muryar Mc ta katse su da cewa"ban bada iznin a zauna ba"! Gaba aya suka kai idanunsu gare shi don ganin wani isasshen ne mai walkin Sa, Ruke yake da mic can saman step fuskar nan ta shi a murtuke tsoro tukuf da shi, gashin kanshi duk hurhura hatta jagirarsa da gashin bakin shi hurhurar ce ga wani dogon gemu har kan cikin sa, daga ganinsa an drama ne, ganin shi bakuwar fuska yasa suka soma tunanin wanene wannan? Hajiya saratu har ta fara karkata baki zata fara zabga mashi masifa muryarshi ta katse mata hanzarinta Kirari ya soma korowa yana nuna hanyar shigowa hall din da mic din hannun shi, gaba aya suka kai idanunsu don ganin mai shigowa Obinna ne Ya shigo Cikin shiga ta alfarma tare da Babban amininsa Jan kunne.
Chapter 19 · 0% Book details