← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 95 OF 247

Sashe 95

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

kwantar da bayansa kan mattress din, ha i da lumshe idanunsa. Nannauyar Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke bayan ta sauka downstairs, Hannun ta aya dafe da saifin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face kalamansa da suka tsaya mata arai, yayi matu ar bata mamaki bata ta6a tsammanin Danish Yana da wayau har haka ba, ko tayaya akai yasan alamomin mace idan ta balaga"!? Ta jefa wa kanta tambayar da bata da amsarta..wucewa dinning tayi zuciyarta cike fal da tunanin sa... _____________________________ Da marece Hajiya saratu tana a gym room na gidan, cikin shiga ta activewear black colour riga da short dai dai gwiwarta, A hankali take running kan threadmill, ta ha a uban gumi kan fuskarta da jikin ta. Maganganun da suka tattauna da su zahra ne suka fara dawo mata akanta, Abun Ya tsaya mata aranta, tun bayan tafiyarsu take ta tufka da warwara, tana matu ar son taimaka masu, but how? Tasan owais mai biyayyane agare ta, komai takeso zaiyi mata, sai dai bata jin girman kanta zai bari ta nemi alfarma agurinsa Kuma bata jin zata iya taka kafarta zuwa gidansa. "Me ya kamata nayi"? Ta jefa ma kanta tambayar, Farat aya ta tuna da hajiya laurat! Ita kadai ce zata Iya bata shawarar daya dace. Fitowa tayi daga gym room din ta nufi part din su. Tana shiga daki, ta nufi toilet ta shiga, within 15 mins, ta fito sanye da bathrobe, ta zauna kan mirror chair, phone dinta ta dauka ta danna ma hajiya laura kira Sai da kiran ya kusa katsewa kafin hajiya laura tay picking "Matar yaya barka da marece?ya kike"? Ta fa a da murmushi akan fuskarta On the other hand Hajiya laurat tace"Amarya kuma uwargida a wurin praving, lafiya lou, fatan kema haka..." jinjina kai ta anyi kamar tana agabanta "naji kinyi shiru? Fa amin meke damun ki? Don tunda naga kiranki a irin wannan lokacin raina Ya bani wani abu na damunki" "Shawara nakeso Ki bani...." ta fa a kamar bata son furta maganar, A hankali ta zayyana mata komai dangane da zuwansu zahra... "Bansan Ya zanyi ba! Nayi masu alkawarin zuwa gobe zasu ji kirana, nasan sun kwallafa rai, ni kuma Allah bana son in nemi alfarma awurinsa, nasan owais yana da biyayya zaiyi min abun da nakeso amma ina jin nauyin zubda ma kaina mutunci..." Sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya cika kunnanta, nan take ta ha e rai"bana son iya shege, Oh dariya ma na baki? tun da bazaki bani shawara ba, zan kashe kiran" Da sauri Hajiya laura tace"Am sorry hajiya, kin bani mamaki ne! Kamar kina jin shakkar tunkararsa, Ki aje wani jin kai gefe aya, Yaron nan an yayanki ne, kuma anki, kina da iko da shi, ba alfarma zaki nema a gurin sa ba! abun da yakamata shine Ki bashi Umarni, kiransa zakiyi awaya kice mashi yazo inda kike Ya same ki, Idan Yazo ki zauna ki fa a masa komai sannan kice mashi gobe zasu zo ganin yarinyar, baki bukatar wani abu da zai sa girmanki ya zube a idon su...." tiryan tiryan hajiya laura ta tsara mata komai, tunkafin ta karasa maganar, Hajiya saratu ta fara sakin murmushin gefen fuska, saboda shawarar tayi mata 100% shiyasa take ji da hajiya laurat, matar karshe ce wurin Iya bada shawara.. "I can't thank You enough, Hajiya ta, nagode da shawararki, shiyasa yayana Yake ji dake saboda kin Iya tsara kalami ga iya bada shawara...." sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya karade kunnanta Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"nima naji dadi da kika dauki shawarata, Yanzu fa a min Ya ake ciki game da hajjaty? Har yanzu baki gano komai ba"? Ta6e baki hajiya saratu tayi"Hmm Matar wayon tsiya gareta kamar dila, yarinyar dana sanya tana yi mata le en asiri, har yanzu bata gano komai ba, amma tace min tabbas akwai wani abu da take kullawa adakinta, saboda bata son kowa Ya shiga...." Hajiya laurat tace"munafuka, ay daga ganin ta zatai wayau, kuma wallahi ba wayanta bane akwai wanda ke aurata akan hanya,..."! "Kamar ya bangane me kike nufi ba.."? "Ina nufin ba ita kadai take shirya plan ba, akwai wani dake taimaka mata..." da tsantsar mamaki hajiya saratu take sauraronta, tabbas Ta yarda da kalaman hajiya laurat saboda matar tana da kaifin basira... Sun jima suna tattaunawa akan hajjaty kafin daga bisani su ka yi sallama. ______________________________ Kusan atare motocin su suka kunno kai cikin estate din, Bayan sunyi parking, Pravin Ya fito cikin shiga, ta suit, Ya jingina bayan shi jikin motar, Idanunsa akan motarsu twins dinsa, fitowa sukayi kowannansu Ya dauki wankan suit, sun kwaso gajiyar aiki sai faman lumshe idanu sukeyi Tunkarar shi sukayi da sauri shima Ya nufe su, gaba aya ya hadesu Ya rungumesu, tare da daura hannayensa abayansu. "Yau mun dawo gida atare, ya gajiyar aiki" dagowa sukayi atare suka dube shi "Daddy Ba dadi, wallahi, na gaji, ni fa kasan bana son wahala.." zayn ne yayi maganar, Zaid Yace"Alhamdulillah daddy, kaima ya gajiyar naka aikin"? Murmushi yayi kafin yace"ay ni bana aiki, ina da masu yi min komai, illa Iyaka in karshen wata yayi in kwashi Albashina...." kallon juna sukayi da mamaki akan fuskokin su, Ko ajikinsa Yaci gaba da fadin"tuntuni naso In wayar maku da kai amma kuka i yarda, Kunfi so ku yi ta wahala akan albashin da bai taka kara ya karya ba, har atm dina na baku don kuyi irin rayuwar da kukeso amma kuka ki kar6a saboda baku yarda dani ba ko.." Shiru sukayi suna kallonshi, kafin Zayn yai kafin halin cewa"daddy ta yaya zamu kar6i kudinka? Bayan ba halal dinka bane!! Baka aiki kuma kana kwasar albashi, hakan na nufin haramun kake ci, daddy kaji tsoron Allah, ka riga da kasan hukuncin wanda Ya gina kansa haram..." bai are maganar ba, Pravin yayi saurin dakatar da shi ta hanyar aga mashi hannu, da kakkausar murya ya furta"Enough! Don't you dare repeat what you just said to me!! Gidan ubanwa nake cin haram? duk wani ku i da nake da su, Hakkina ne ina da goyan bayan wa anda suka aura ni akan mu amin da nake da shi. ..." Yana fa in hakan rai a6ace Ya nufi cikin gidan, da sauri zaid yabi bayanshi tare da shan gaban shi. "Daddy ka yi hakuri, naga ranka ya 6aci, Dan Allah ka yi hakuri da abun da zayn yace maka! ka yafe masa kada ka ruke sa a zuciyarka..." Murmushin gefen fuska pravin yayi"kada ka damu my son, komai Ya wuce" Ajiyar zuciya zaid Ya sauke, Tare da ruko hannun daddyn nasu suka shiga parlour. Zayn dake kallon su har sai da suka 6ace ma ganin shi, kafin ya jingina bayan shi jikin motarsu, kalaman zahra ya fara tariyowa, a lokacin da ta kira shi Yana a office, ya gama watsewarsa tare da abokiyar aikinsa yana akan network shiyasa Ya zazzaga mata masifa son ranshi aranshi ya ayyana ko sun samu shiga estate din? Ta6e la66ansa Yayi irin bai damu din nan ba, Ya wuce Ya nufi cikin gidan "CHIEF OWAIS Yana a cikin Katafaren Office dinsa dake a isod Headquater, office in Ya ha u, an awata shi da high-end supplies komai na cikinsa launin blue sky ne kalar da yafi so, office din Yana da mugun tsaro gaba daya na'urori ne ke sarrafa komai na cikin sa.." Dadda amshin turarensa Ya gauraya da ni'imtacciyar iskar dake ratsa sa o da lungu na office din, a yayin da yake azaune kan wata tamfatsetsiyar Excutive chair ar ubansu, Ya aura kafarsa aya bisa aya, daga gaban shi luxury table ne mai auke da High-end computer da sauran kayan amfaninsa dake a baje kan table din A hankali Ya bu e idanunsa dake a lumshe, Ya cigaba da operating computer din gabansa, Adjusting webcam dinsa yayi, kafin ya danna video call Ya dan dakata Yana jira a amsa mashi. a hankali fuskar commender ta bayyana ta cikin screen din Murmushi suka sakar ma junansa, Cikin harshen turan ci suka fara magana "Commander, good to see you, sir," ya fa a tare da sarah mashi da hannu "Chief, good to see you too," shima ya sarah mashi. "What can I do for you?" Numfasawa chief yai kafin yace"I'm calling to extend an invitation to a high-level meeting in Nigeria, dangane da yaran da kuka dam a mana case din su" Ya are maganar, Cike da sa ran zai amsa mashi Jinjina kai commender din Yayi na an wani lokacin Kafin Ya furta" okey, What's the current situation?...bayani ya fara kora masa dangane da halin da ake ciki na binciken prisoners. Tun da ya fara commender Yake an jinjina kanshi alamar gamsuwa, bayan ya are maganar yace"yanzu wani mataki zaku fara auka"? Chief yace"That's what we'll discuss during the meeting" "Tunani mai kyau, zanyi magana da na sama dani, idan har na samu goyan bayan su, zamu halaccin meeting din, yaushe ne kuma a ina za'ayi"? "Upper week, in Abuja. I'll send over the details. Thank you, Commander..." Ya fada tare da sara ma shi da hannu.. Shima commender din Ya sara mashi bayan sunyi sallama Ya kwantar da kansa jikin kujerar "DDG Is coming" Muryar na'ura ce ta ratsa kunnansa, A hankali Yakai idonsa ga duban Glass door ta office dinsa wadda ke kokarin zuge kanta Big guy ne Ya shigo sanye Cikin kakinsa, Cikin girmamawa Ya sara mashi. "Sannu da aiki Yalla6ai, Na ji shiru baka fito ba, ko baka lura da time ba ne"? Kallon agogon hannunsa yayi arfe biyar na marece, har time din ta shin sa yayi bai lura ba. "Have a seat" Zama big guy yai kan kujerar dake fuskantar chief kamar yadda ya umarce shi "Munyi waya da commender..." a agare big guy yace"ina fata Ya amsa bu atarmu"! Calmly ya zayyana masa tattaunawar da su kai, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar shi"Allah Yasa mu ji alkhairi" Ya amsa mashi da ameen Shiru sukayi na wani lokaci kowa da abunda Yake sa awa aranshi "Ya kamata ka tashi muje in kaika gida, burina ka huta..." murmushi chief yayi"nagode da kulawarka agare ni, Ina boss ko har ya tashi aiki"? "Tun wuraren hu u ya koma gida, kasan mutun mai Iyali, ba kamar mu
Chapter 95 · 0% Book details