Sashe 101
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
hankali taj ya araso Ya tsaya daga bayansu, tare da goya hannayensa bisa kirjinsa. A sukwane hajiya saratu da chief suka mi e tsaye suna kallon su, fuskokin kowan nan su auke da murmushi su kansu da suka sake ha a wannan zumunci ba karamin dadi suka ji ba, farin cikin da suka gani akan fuskar Aneelerh da unaisah ba zai misaltu ba. Yadda Aneelerh ta rungume unaisah, kamar zata mayar da ita cikin cikinta, a kalla sun shafe mintuna goma manne da juna, kafin Aneelerh ta raba jikin ta daga na Angel, a lokacin itama ta dur usa kan gwiwowinta, Aneelerh ta sanya tafukan hannayenta biyu ta tallabo fuskar unaisah da su, itama unaisah ta tallabo fuskar Aneelerh da nata tafukan hannun, suka kurawa juna ido yayin da hawaye ke sintiri kan fuskokinsu, cikin shesshekar kuka Aneeleeh take fadin"Angel dina! Kece nake gani? Dan Allah ki fahimtar dani nagaza yarda da abun da idanuna suke gane min! Wayyo Allahana.." ta fada tana jan numfashi. "inna lillahi Ya Allah Idan Mafarki nake kada ku tada ni, kubarni kawai inci gaba da yin shi, Ya ilahi Angel dina ce..Ina kika shiga? Kika bar auntynki da ciwon rashin ki? Angel wayyo Allah...duk tabi ta susuce Cikin muryar kuka unaisah tace"Aunty Aneeleeh, ni ce Angel dinki, arki, Aunty Aneeleehna, ba mafarki kike Yi ba, ni ce dagaske, Angel dinki abokiyar firarki, mai sanyaki nishadi..." ara rungumeta Aneeleerh tayi. Gyaran murya taj yayi cikin karayar zuciya ya firta"Aneelerh!.." kamar jira take yayi magana, a zabure ta mike ta tsaya agabanshi idanunta jawur ta furta"taj! kasan irin haukan rashin ku da nayi? Me nayi maka dana tsantsanci haka daga gareka?..." kwalar rigarshi ta dam a da hannayenta biyu ta jijjiga shi kamar zata rufe shi da bugu taci gaba da fadin"taj meyasa kayi min haka? Meyasa ka gudu da unaisah kuka barni da kewarku? Taj kasan irin kunci da radadin dana naji a lokacin dana farka naga babu ku"? Kalamanta sun karya zuciyarshi baisan sa'adda hawaye suka wanke fuskar shi ba, Zahra dake kallon su tuni hawaye sun wanke fuskarta ga wani farin ciki da ya lullu6e ta na ganin Unaisah, Jikin chief owais yayi sanyi lakwas tsantsar tausayinsu ne ya kama shi, ba shi ba hatta Hajiya saratu sai da taji tausayinsu duk da bakomai ta sani ba dangane da rayuwar su ba. "Taj Ina mijina? Ina uzair! nasan Yana atare ku? Ka fa a min taj meyasa kuka gudu daga gida? Tsawon shekara da shekaru baku ta6a waiwayena ba? Laifin me nayi maku taj? Idan wani abu ne yasa kuka gudu meyasa baku sanar dani ba? Harga Allah bakuyi min adalci ba taj! dai dai da rana aya baku ta6a nema na ba ko da awaya ne...." Da yar ta are maganar, Lokaci aya ta yanke jiki zata fa i da sauri taj ya tarota ta fa o kan kirjinsa. Da sauri zahra ta karaso gabansu tana kuka, zu unnawa taj yayi a hankali ya kwantar da kanta bisa laps din sa, har lokacin Angel tana a durkushe kan gwiwowinta da karfi take furta"Aunty aneelerh ki tashi! Dan Allah ki tashi wayyo Allahna daddy ka ce mata ta tashi" duk tabi ta rude zahra ma kukan take tana ambaton sunanta, Hajiya saratu ta kasa furta komai, lamarin ne da ta6a zuciya.. robar ruwa mai sanyi chief ya dauko daga kan table, Ya nufo wurinsu Ya bu e murfin tare da mika ma Taj, Hannunsa na kerma Ya kar6a Ya tarfa ruwan a tafin hannu Ya watsa mata kan fuskarta, nan take taja mumfashi tare da furzar da shi... Cikin karyayyar murya ya furta"Anila! dan Allah ki saurareni, wallahi bada son ranmu muka gudu ba, mummunar addara ce ta afka mana wadda tayi silar barinmu gida..., na rasa komai nawa Aneeleeh..." ya fa a yana kallon cikin idanunta, dakyar take kallon shi, wani irin azababben ciwon kaine Ya far mata, ita kadai tasan halin da take a ciki. "Nasan zaki fahimce ni Aneeleerh, har abada kinsan bazan Iya gudunki hakanan ba tare da wani waran dalili ba, dukan mu babu wanda baiyi kewar rashinki ba, kuma ko bayan da muka gudu kina aranmu bamu manta dake ba....." "Taj ina mijina...."! Gabansa ba karamin faduwa yayi ba, kallon chief yayi da sauri ya girgiza mashi kai alamar kada Ya fa a mata, saboda a halin da take ciki muddin suka sanar da ita tsaf zata iya zaucewa. "Aneelerh, bansan Ina uzair Yake ba! Idan ba zaki manta ba, ba atare muka bar gida ba, adaren ranar da abun ya faru kinzo har gida kin same ni kina kuka kika ce uzair bai dawo ba, har na kwantar maki da hankali, tun daga wannan lokacin ban ara sanya uzair a idona na, amma muna nan muna bincike akanshi, in sha Allah shima zamu gano shi. zuciyarta ba karamar karaya tayi ba, tuni ta sake fashewa da wani sabon kukan. Kafin wani ya sake magana a cikin su, wayar Hajiya saratu ta fara ringing, da sauri ta zaro wayar daga cikin handbag dinta, ta duba mai kiran ta, p.a din tace, picking call din tayi"Okey, Gani nan zuwa yanzu nan.." ta fa a tare da katse kiran ta dago ta dubi chief. "My son yakamata na tafi, naso in tsaya amma kirane na gaggawa, duk halin da ake ciki pls ka sanar da ni..." ta fada cikin saurin murya, kafin ta dubi su Zahra. "Zahra, Ni zan wuce, in sha Allah idan na samu time zanzo asibitin in duba mara lafiyan..." tayi masu fatan Alkhairi, godiya suka dinga yi mata, Har bakin mota chief tare da zahra suka rakata, akan idonsu motar ta fice daga gidan. Dawowa sukai wurinsu Taj dake a durkushe asa. "Taj baka fadamin meyasa kuka gudu ba..."? Cikin jin unar rai ta jefa mashi tambayar. Atakaice ya labarta mata abun da ya faru da su, tun farkon da suka fara yi ma Alhazawan nan le en asiri da kuma farmakin da suka kawo mashi atsakar dare harya gudu da Angel....." sai dai bai sanar da ita wayar da uzair ya kira shi ba ya dai ce shi baisan meya faru da uzair ba, har yau suna neman shi ba su gan shi ba, hankalinta yayi mugun tashi jin wannan musifar data afka masu, hatta zahra tayi matu ar firgita jikin ta sai tsuma yake abun ya bata tsoro... "Shiyasa bamu neme ki ba, saboda rayuwarmu tana a cikin hatsari, idan har miyagun suka san muna raye ba za su kyale mu ba, don dole muka killace ce kanmu kafin Allah ya tona asirin su" "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji! taj wannan wani irin tashin hankaline! Ni dama saida raina ya bani ba hakanan kuka gudu ba, Allah Yasa basu kashe uzair ba, nama san mawuyacin abune uzair ya rayu watakil sun kashe min shi...." bai bari ta are maganar ba, Ya fara lallashin ta dakyar Ya shawo kan ta.... Zafafan hawayene suka cigaba da wanke kuncin ta, "Boss!" chief ne Ya kira sunan shi "Na'am yalla6ai" "Ina son magana daku, ban da unaisah" A hankali Ya ago da Aneeleeh, da sauri zahra ta zu unna tare da tallabo ta don gaba aya jikin ta ba kwari dakyar ta samu ta mi Unaisah dake kallon su ta shiga ru ani tunda chief Yace Yana son ganin su ban da ita... o hannunta taj yayi, suka nufi sofas din wuri ya zaunar da ita "Daddy meya faru"? "Kada ki damu, magana ce mai mahimmanci zamuyi, Idan muka gama zamu sanar dake, cike da gamsuwa tace toh azu Kin fa a min kina jin yunwa, ga snacks nan da juice ki sha kafin mu gama magana" yatsun hannunta har kerma suke wurin daukar burger ta fara cin ta. idanunta akan su Aneelerh dake tafiya suna nufar can nesa da ita, zuciyarta cike fal da farin ciki, kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna, bakinta yaki rufuwa sai faman tariyo fuskar aunty aneeleeh takeyi, burinta su gama maganar don ta tambayeta ina anin ta da daddynta ya bata labari ta haifa mata.... Bayan kowan nan su ya zauna kan kujeru suka nutsu suna jiran jin me chief zai sanar da su "Inaso ku fa a masa abun da ya kawo ku neman ar sa"! Ya fa a batare da ya ago ya kalli waninsu ba, a an ru e Taj Ya kalli su Aneeelerh. Baiwar Allah tama rasa ta ina zata fara, saboda tasan ba lallai Ya amince masu ba. "Aneelerh kinyi shiru! Fa a min meyasa ku ka zo neman Angel? Tun jiya chief yayi min bayanin zuwan ku amma bansan cewa ku bane, nayi mamakin ganin ku! Tayaya har kuka gano inda mu ke!? Ya fada cike da son jin arin bayani. Cike da fargaba Aneeleeh ta fara zayyana masa abun da ya faru na bayyanar benazir, bata 6oye mashi komai. tunkafin ta arasa maganar yanayin fuskar taj ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, kwata kwata baiji dadin bayyanar benazir ba, saboda tafi ta aransa baya bu atarta arayuwar shi, wani irin aci yaji aran shi, Aneeelerh ta fama mashi tsohon raunin dake a zuciyar shi. ko sunan ta baison ji, aranshi ya arayyana da ranta da lafiyarta tsawon shekara da shekaru bata ta6a neman su ba? Idan har shi bata neme shi ba ay yakamata ko yarta ta nema baisan wata irin zuciya bace a kirjin benazir ya riga da yasan halinta domin kuwa ba zai ta6a manta irin rayuwar auran da sukai da ita ba, macace mara kunya batasan darajar aure ba, ta azabtar da shi da soyayyarta. gaba aya sun lura da yanayin shi, kamar baya atare da su, Aneeleerh duk tasha jinin jikin ta, dafa kafadarsa chief yayi a hankali ya kallesa idanunshi sun ka a jawu"dan Allah kada kace inyi hakuri, saboda bana jin zan iya yafewa benazir, hasalima ban yarda cewa dagaske ta damu da mu har haka ba, Allah kadai kasan manufar da take da ita akan mu, ba zan ta6a yarda da benazir ba, matar da ta tafi tabar yarta a kwamin wanka, taje can tana yawon bi in ta tsawon shekaru bata ta6a neman mu sai yanzu"? Hawayen dake taruwa a cikin idanunsa tuni sun wanke fuskarshi hakan ba karamin aga hankalin zahra da Aneeerh yayi ba..