Sashe 143
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
tare da ru o hannun bra in ta sa ala mata shi, ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta koma gaban mirror tana kallon kirjinta, Yau ne karo na farko data fara sanya bra, tayi mata cuf cuf yadda kasan wadanda suka auko bras din sun san size din ta. Unaisah dake kallonta ji tayi dama ita, yamutsa fuska tayi"idan kin kammala kallon madubin ga kayan da zaki saka nan na zabo maki" ta fa a tare da daura mata su kan gado. Batare da bata lokaci ba, kowan nan su ya sanya kayan shi, tsayawa sukayi agaban mirror suna kallon tsantsar kyan sukayi gaba ayansu Long sleeved gown ce a jikinsu launin Ice blue sai kyalli take da aukar ido, ga wata hadaddiyar Silver necklace da suka saka a wuyan su, yayin da wrists din hannunsu ke asanye da Beaded Bracelets, sun saki curly hair dinsu ya lullu6e gadon bayan su, yadda kasan wadanda zasu halacci gasar miss word su kansu sun jinjina ma ha uwarsu, sun tasa madubi gaba sai jujjuya jikinsu sukeyi. Saida suka gama kallace kansu kafin unaisah ta dauko masu fragrance set suka fara barin ruwan turare ajikinsu saida kamshin ya gauraye dakin su tukunna su ka dakata da shafa shi. "Wlh munyi kyau, Allah Ya zuba mana ruwan kyau sister" batool ce ta fada tana yarfa hannayen ta, murmushi unaisah tayi tana kallon kanta ta cikin mirror "Sai yau na kara ganin kamanninmu Allah, dukanmu tubarkalla dogaye ga dogon hanci, an bakin mu heart shaped, gaskiya mungode ma Allah..." proudly ta fa "Bari na dauke mu hoto" da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan pillow, ta dawo kusa da batool suka hada kai ta fara daukar su pics har kusan kala ashirin.. "Bari inje in nuna ma aunty ummi wankan dana dauka nasan zata ru e da kyawuna" da gudu ta fuce daga akin hannayenta ruke da bazar rigarta kamar wata amarya, har ta fuce daga dakin unaisah bata daina kallonta ba har saida phone dinta ta fara ringing kafin ta kau da idonta, screen din wayar ta duba ganin sunan My man yasa ta an yi murmushin gefen fuska kamar yasan jiran kiran shi takeyi girman kai ne ya hana ta fara neman shi, zama tayi daga gefen gadon ta aga kiran tare da kara wayar a kunnanta Tayi shiru bata ce komai ba, tana jiran jin me zaice mata. "My Angel..." bai are maganar ba ta katse shi da cewa" azu na tura maka message, nace ka sauko down muyi breakfast why didn't you come?" Ta fa a tana ha e fuska kamar tana agaban shi. Softly ya furta"Naga sakon da kika tura min, amma ban fahimci me kika rubuta ba, shiyasa ban zo ba" jikinta ne yayi sanyi lakwas duk sai taji ba dadi "Meyasa baka kira ka tambayeni me na rubuta maka ba? Shiru yayi bai bai tanka mata ba. "I have no answer,"? Still baice mata komai ba. "Okey, kayi breakfast dinka"? Sai lokaci taji ya an sauke ajiyar zuciya"nayi, Haris ne ya kawo min adaki" Lumshe idanunta tay, wani irin yanayi take jin kanta, Sautin muryarshi ba karamin rikita ta ya ke yi ba, A hankali ta kwantar da bayanta jikin pillow, dadin muryar shi take ji, idan suna yin waya har bata son suyi sallama da juna ______________________________ Lokacin da motar dr shureim Ta biyo kan titin Obie Estate tun kafin su karasa Benazir take bin ganin da kallo yau ne karo na farko da ta fara zuwa, ta ru u da ganin ha uwar katafaren entrance gate din dake abu e ga wasu fusatattun sojoji dake tsaron ofar cikin taku na majiya karfi suke kai komo abakin gate din sun kasa sun tsare babu mahalukin daya isa ya etare kofar batare da an basu izni ba. Hatta dr shureim bai ta6a zuwa ba, ya dai san estate din amma bai ta6a shiga ciki ba. rage gudun motar yayi slowly yayi parking dinta gefe guda, don yasan ba lallai su barsu su shiga ciki ba. ."Anila kina ganin zasu barmu mu shiga"? Benazir ce tay mata maganar tare da dubanta "Eh, amma dole saida iznin wani daga cikin mutanan gidan," ta fada tare da daukar wayarta daga cikin handbag, A hankali ta kwantar da baby junaid kan seat ta dubi dr shureim"bari na kira daddyn azeezaty din" amsa mata yai da toh, ta bude murfin motar ta fito daga waje ta danna ma shi kira, bayan ya aga ta kara wayar a kunne. "Taj, munzo yanzu haka muna a bakin entrance gate na estate din" On the other hand taj yace"tare da wa kike zo"? Lokaci daya taji gabanta Ya fadi, tunawa da gargadin da sukayi mata sam ta manta. Dakyar tay karfin halin ce mashi"tare da Benazir, sai yayanta dr shureim shine ya kawo mu..." bata kare maganar ba taj ya furta"why Anila? Why? Kin manta kashedin da chief yayi maki? Akan me zaki zo da su gidan nan? Ke kadai fa nace kizo saboda Angel tana son ganin junaid" Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba duk tabi ta rude, ta fahimci ranshi ya 6aci "Kina atare da su ne"? "A'a na fito daga cikin motar ni kadai ce, Zanyi maka bayani, nasan zaka fahimce ni"! Shiru yayi yana sauraron ta cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri idan na bata maka rai, nasan ban kyauta ba, amma ba yadda zanyi ne, bazan iya jure ganin Benazir cikin mawuyacin hali ba, wlh baka ga yadda ta koma ba, saboda rashin Unaisah bata da kwanciyar hankali, ko abincin kirki bata iya ci duk ta rame, Kai kace min da zarar ta dawo hayyacin ta, in sanar da ita cewa yarta ce, yanzu tasan komai..." bata kare maganar ba, Taj yace"kina nufin kin fada mata har abunda ya faru da mu"? Yamutsa fuska tay tamkar zata saka mashi kuka tace"na fa a mata, amma na gargadeta akan kada ta bari kowa yasan kuna araye, sannan nace mata kada ta bari unaisah ta gane itace mamanta kamar dai yadda kukayi mana bayani haka itama na sanar da ita, kuma tayi min alkawarin ba zata sanar da kowa ba" "yayanta fa kin fada mashi? Shiru tayi gabanta na faduwa Har saida ya sake maimaita tambayar da yayi mata kafin tace"A'a bai sani ba, mun dai fada mashi zamu zo gurin Azeezaty ne, kuma kasan dr shureim bai son ka ba, bazai iya gane komai ba, balle shi da bai cika shiga sabgar da bata shi ba wlh baida matsala, mutunne mai kamun kai" saida takai aya kafin yace"Anila na fahimce ki, amma Bana so Benazir ta yi wani abu da zaisa unaisah ta gane cewa mahaifiyarta ce, pls komai ya tafi yadda muka tsara shi, idan kika bari aka samu matsala ke da chief ne" "In sha Allah baza asamu matsala ba, zamu kiyaye" Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar shi"okay, zanyi magana da chief, ku ara hakuri," amsa mashi tay da toh, bayan sunyi sallama ta bu e murfin backseat ta shiga daga ciki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, atare dr shureim da anila suka kalle ta "Ya ake ciki"? Murmushi ta danyi tare da kallon benazir tace"yace mu jira, za'a bamu iznin shiga" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke. Dr shureim yace"junaid har yanzu bai farka ba, ko dai kin bashi sleeping pill ne" yar dariya tayi"a'a wlh, nima nayi mamakin baccin shi kamar wanda yasha waya, may be ko dan jiya bai samu isasshen bacci bane..." ta fa a tare dakai hannu ta shafa gefen fuskarshi. Benazir tace"Allah nafara gajiya da jira, Allah yasa kada su shanya mu awaje, nifa na osa naga babyna" cike da zolaya dr shureim yace"bari maman babyn taji kina kiran sunan arta da sunan taki, kotu ce zata rabaku" dariya sukayi gaba dayan su. Kafin wani daga cikinsu Ya ara furta kalma, Suka ji anyi knocking window glass din motar da sauri dr shureum ya sauke glass din Wani soja ne tsaye fuskar shi a murtuke ba annuri ya furta"Who is Anila?" Yawu ta hadiya muryar ta na dan rawa tace"I am sir" "Okay, ku shiga daga ciki, an baku izni" kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, dr shureim ya tada motar ya nufi drive way din da zai sada su da cikin estate in, Anila ce ta dinga nuna mashi hanyar da zai bi har suka karaso gidan chief, basu sha wahala ba, motarsu na karasowa bakin gate din jami'an dake tsaron shi suka basu iznin shiga ciki bisa umarnin mammallakin gidan hakan na nufin an san da zuwan su, tun da motarsu ta shiga benazir ta ke ta jinjina kai wato sunyi mamakin haduwar katafaren villa din, daga gefen wani stunning fountain dr shureim ya tsayar da motar. Rungume baby junaid anila tayi akan kirjinta, ta bu e murfin motar ta fito, kafin dr shureim da Benazir suka fito daga ciki, A hankali suke karewa tamfatsetsen ginin kallo, ba su ta6a zaton za'a samun daular data kai ta Alhaji musa haduwa a birnin abuja ba, sai gashi yau Allah ya ha asu da gidan director general Of Isod. Jikin motar suka jingina bayan su, kowa da abun da yake sakawa aran shi, musamman Benazir ta kosa ta ga taj da Angel dinta murmushi kawai take saki ita kadai tasan dadin da take ji "Bani junaid din in ruke maki shi" mi a mata shi anila tayi bayan Benazir ta kar6e shi ta rungume a kirjin ta, Jami'an dake kai komo sai kallon su suke yi. "Ina zamu nufa"? Benazir ta fada tana kallon Anila, tayi shiru saboda batasan ina zasu dosa ba, har ta yanke shawarar kiran Taj, kwatsam Horn din mota Ya kara e kunnuwan su, kusan atare suka dubi hadaddiyar motar dake tunkaro kirar black Mercedes Agaban su motar tayi parking, sun ura ido suna jiran ganin wanene mamallakin ta. Ta ciki aka bu e car door din, gently ya fito daga ciki gaba daya suka bi shi da ido, yana sanye da kayan kakinsu na isod ya rufe fuskan shi da mask, zagayawa yai ta other side in motar ya bu e murfin, slowly chief ya fito daga cikin, hannun shi ru e da wayar shi, fuskarshi sanye da face mask, gaba daya dr