Sashe 184
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
kofar shiga falon part dinsa, Ya danna Password din ofar, ta bude kafin Ya shiga da ita ciki, adai dai Lokacin Yan uwanta sun kabbara sallar La'asar da ake ta kira, anan falo Danejo ta shimfi a masu prayer mat sun daidaita sahun su. Kwatsam su ka jiyo kukan Unaisah hakan Ya aga hankulansu a rude suka katse sallar, gaba daya suka kai dubansu ga Taj, sun firgita da ganin yadda Ya daukota a saman kafadarshi, sai hauka ta ke yi mashi, har suna hada baki gurin tambayar Taj meya faru da Unaisah. bai bi takansu ba, Ya nufi bedroom dinshi da ita, adai dai lokacin Ummi da danejo sun sallame sallamarsu kusan atare suka mike tare da bin bayan shi. Sai dai kafin su araso Taj ya datse ofar akin. A saman gadon shi Ya wurgar da ita gaba aya ta kife kan mattress din gashin kanta ya tarwatse Yana huci Yace"shashasha, wlh kin bani kunya, wlh badan kaunar da nakeyi maki ba da yau saikin yabawa aya Zakin ta, bugun tsiya zanyi maki, wawuya kawai, ban ta6a zaton za ki min haka ba, har yanzu kina nan da kafiyarki ta kuruciya, saboda soyayya bakya ganin kowa da gashi, shi kadai kike tsoron ki rasa, na fahimci ma kinfi damuwa dashi akaina, nima fa hadani za'aje kurkukun, amma kwata kwata bata ni kike ba..."! yar ya arasa maganar saboda ululun ba in cikin daya tokare makoshin sa. A hankali Hawaye masu umi suka wanke fuskarsa. Dagowa tayi agalabaice tana kuka ta girgiza mashi kai muryarta ashake ta furta"daddy ba haka bane, ka fahimce ni, kaifa mahaifina ne, wallahi na damu dakai, har abada bazan ta6a samun madadinka ba..." bata kare maganar ba, Ya juya zai bar dakin yana huci, durowa tayi daga kan gadon da gudu ta nufe shi harya ruke handle din ofar, tay saurin rungumeshi ta baya ta zagayo da hannayenta kan stomach dinsa, ta ma yleshi cikin shesshekar kuka take lallashin shi tare da bashi hakuri.. su ummi sai bugun kofar sukeyi don ya bude masu. Hakan da tayi masa ba karamin sanyaya zuciyar shi tayi ba, tuni ya sauko daga kan dokin zuciyar da ya hau, A hankali Ya ruko hannunta tare da janyo ta ya dawo da ita ta gaban shi, Yayi hugging dinta tightly, a hankali yake shafa sumar kanta, duk da halin damuwar da take a ciki sai da taji sau in radadin da take ji a cikin zuciyarta. cikin sanyin murya yace"komai ya wuce Unaisah, na daina fushi dake, raina ne ya 6aci amma yanzu na fahimce ki, kiyi ha uri dukkanmu addu'arki muke bukata, amma kukan nan da kike yi da sanya damu aranki bazai ta6a canza mana kaddararmu ba, saboda addu'a ce kadai take canza kaddarar bawa, Ki yi mana addu'a Unaisah In sha Allah, zamu dawo cikin koshin lafiya.." cikin kwantar da murya yakeyi mata nasiha, su Ummi dake tsaye bakin kofar dakin sunyi shiru suna jiran ya bude masu ofa.. daga bisani ya ru o hannunta suka shiga toilet, Ya wanke mata fuskarta, suka fito daga toilet din still hannun shi ruke cikin nata suka zauna kan gadon shi.. "Daddy, bazan kara kuka ba, zanyi maku addu'a, Allah ya kare min ku ya dawo min daku lafiya" tsananin tausayinta ya kama shi damuwar shi a haka zai tafi yabarta gashi yaji alamun zazza6i a jikin ta. "Yawwa my daughter, yanzu kin share min kokwantona akanki, ni dama nasani, ata mai biyayya ce, zatayi abunda daddyn ta yake so.." ya fa a tare da shafa gefen fuskarta data kumbura jawur, wlh shi kadai yasan irin yadda yakeji azuciyarshi duk in ya tuna inda zasuje da kuma yarsa tilo da yake da ita, bayason wani abu ya faru kawai dai yayi imanin komai zai faru da su mai kyau ko mara kyau mukaddari ne daga Allah, Bawa bai isa ya guje ma kaddararsa ba. "Banaso sauran Yan uwanki, su gane wani abu, pls kija baki kiyi shiru, ko da sun tambayeki me yasa kike kuka, ki fada masu wani abun daban, nasan kina da wayau basai na maki bayani ba " jinjina mashi kai tay, Rungumota yayi akan kirjinshi, ya fara janta da fira Yana tariyo mata kuruciyarta duk da halin damuwar da take aciki saida taji sanyi aranta. "Nan dakina ne, Zaki Iya zama aciki kafin mu dawo, ga toilet ki shiga kiyi wanka.." amsa mashi tayi da toh.. Sumar kanta yaci gaba da shafawa, yadda ya sabayi mata tuntana yar kankanuwarta, ahaka yake samu tayi bacci, aiko cikin sa'a yaji alamun bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke a hankali Ya kwantar da ita kan gadon, sai da yayi mata addu'o'i kafin Ya mike da baya da baya yake tafiya yana kallon ta idanunsa cike tab da kwalla. Jiki asanyaye yajuya tare da bu e room door in Ya fito su ummi na ganin shi suka kewaye shi kamar yan jarida suka tsare shi da tambayar meya faru da Unaisah... "bata Jin dadin jikinta ne, zanyi magana da dr, zai zo ya duba ta, yanzu bacci takeyi pls idan ta farka ummi ki taimaka mata tayi wanka taci abinci sannan ki sanya mata ido sosai.." basu kawo komai aransu ba, Ummi tace in sha Allah zanyi duk abunda kace. Kallon Danejo yayi"My wife, Pls ki taimaka ma Ummi, Ku kula da su, " fuskarta dauke da murmushi tace"toh, daddyn Angel, kaima ka kulamin da kanka" sallama yayi masu, kafin fitarshi daga part din a alla ya shafe mintuna biyar yana tunani kafin Ya fuce.. _______________________________ *CHIEF OWAIS* A Hankali Motar shi ta kunno kai cikin wani katafaren Resting Home na mai girma sharafudeen, tun kafin SA din dake driving dinsa yayi parking ta window glass din motar Ya hango Jami'an DSS kewaye da Courtyard din gidan dama kafin su shigo yaga sojoji tsare da gate din gidan hakanna ya dinga jin faduwar gaba. Motarsu nayin parking bai jira an bude mashi car door ba saboda sauri da kanshi ya bude ya fito, with respect Dss din dake tsaye suka sara mashi, ko kallo basu ishe shi ba Ya nufi main door din falo. Walking quickly ya haura Uptairs a gaban ofar katafaren Master suite na mai girma sharafudden ya an dakata da yin tafiyar. "Come In" daga cikin akin Ya juyo muryar daddynsa Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing. Madaidaicin table din gabansa na auke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya. Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa "have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba. Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi.. Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka auka kasha naka ne" yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.." iris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ru e yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa. "Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"! Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..." Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi. "hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"? ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi. "Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Ya i ne? "Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi "Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine a namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada. Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala. "Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya fa Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko aya, dan leken asiri nane ya fada min" "why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"! Ya fada rai abace "Naji Ubana Obinna, zan dakatar da an leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ru e hannayensa acikin nashi. "Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice. "pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...." Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta. Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba. "Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda an le en asirin nawa