Sashe 166
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
times kafin ta bu e mashi kofar yaci sa'a ita kadai ce a ciki. "Ya salsabeel yau kai ne adakin mu" dakyar ya kakaro murmushi kan fuskarshi yace"ni ne Unaisah, tun da kika ganni kinsan abune mai mahimmanci ya kawo ni gurin ki" cike da mamaki tace mashi toh, daga gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna, ta tsare shi da idanunta cike da agarar son jin wata magana zai mata "Unaisah Kin san meya faru lokacin da chief ya shiga da Danish Questioning room a headquarter wanda yayi silar fusata Omar har suka samu sabani..." a an ru e ta girgiza mashi kai"ba komai na sani ba, ka an na fahimta daga furucin ya omar" Nan take Salsabeel Ya labarta mata abun da Ya faru tsakanin Danish da Chief,shi ma abakin big guy yaji komai. ranta ya sosu da jin abunda Danish yayi ma chief, babban abunda ya fi bata takaici daya ce ma chief ba gaskiya ya ke fa i ba, they've never hurt him Suna sona shi kuma sune iyayen shi, bayan su bashi da wasu iyaye a duniyar ranta yayi mugun 6aci ba ka an ba, sam ta kasa magana sai jinjina kai take. "Unaisah babu irin magiyar da banyi ma Danish ba, akan ya amince ya basu hadin kai yakiya, nayi lallashin nayi ro on duk abanza wlh da raina ya baci kamar in rufe shi da bugu saboda ya bata min rai..." ya fa a rai a6ace ya an dakata Yana kallon unaisah dake kallon fuskarshi "Wallahi da ace zan iya jagorantarsu zuwa gidan kurkukun kaddarar da tuni nayi hakan Unaisah, sai dai ni yanzu bani da wani karfin ikon da zan iya yin hakan, bayin Allahn nan sun shirya tsaf sun tanadi rundunar sojoji da makaman ya in da zasu farmake su abu aya ne zaiyi masu cikas wanda zai yi masu rakiya zuwa gidan kurkukun kaddarar, Unaisah basu san hanyar da zasu bi ba, ba su san a daidai ina ginin yake ba! Shin akan asa Yake ko karkashin kasa Yake? Bayan haka ke kinsan yadda ginin yake wani irin kurman ginine mai rikitarwa da tsoratarwa in har mutun baida ilmi akan shi wlh tuni zai zauce, Danish shine makamin da zamu iya tunkararsu da shi ..." da yai wanann maganar bakomai ta tuna ba face lokacin data saci hanya ta fita matakalar bene ta dinga mayar da ita baya, ga wannan rudin mai rikita kwakwalwar mutun ya dinga ganin abun da babu azahiri. "Kinyi shiru baki ce komai ba, yakamata Mu ne mi mafita Unaisah, In ba haka ba elders zasu cigaba da aikata zalunci, kwara muyi amfani da wannan damar kada muyi gangancin da zata kubce mata..' tsantsar damuwace akan fuskarta cikin sanyin murya tace"Yaya Salsabeel menene mafita? Kafi kowa sanin halin Danish, Yana da taurin kai da kafiya, Idan ya fadi abu babu wanda Ya isa Ya canza ra'ayin shi...." bata are maganar ba, Salsabeel yai saurin furta"akwai mafita Unaisah" a kagare tace"menene mafita" shiru yayi jim yana jin shakkar yadda zata dauki abun amma daya tuna irin burin da take dashi na son ruguza kurkukun kaddara sai ya samu kwarin gwiwar ce mata"Unaisah, duk duniyar nan mutun aya ne kacal zai iya tursasa mashi Ya bashi umarni kuma Ya bi shi sau da afa..." da ru u akan fuskarta tace"wa kenan"? Nuna ta yai da index finger din shi waro idanu waje tayi kamar wadda taji wani mugun abu "Ke Unaisah! Basai nayi maki dogon bayani ba, kin riga da kinsan irin tsantsar kaunar da Danish ya ke yi maki, wanda ko sauran yan uwanshi da suka taso atare bai ta6a yima kwatankwacin shi ba, wlh nayi imanin in har kika bashi umarni yaje zai je..." da matukar tashin hankali ta girgiza mashi kai labbanta na rawa tace"I can't... I can't change his mind Danish won't listen to me ya Salsabeel kai fa ka fadamin wasu lokuttan ba shi bane zai iya wuni baya a hayyacinsa taya kake tunanin zan iya bashi umarni ya bi"? Ta fada idanunta azare take kallon shi, ita babban tashin hankalinta a ha a ta dashi don ta shawo kanshi bataso su sake samun sabani bayan haka tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar masoyinta cikin ha ari, da alama soyayyarshi na nema ta rufe mata idanunta.. "Unaisah Zaki Iya, Ko ba don saboda son da yake yi maki ba, idan ba zaki manta ba na ta6a fada maki dalilin dayasa suke kiranki da kaddarar kurkuku" kura mashi ido tayi batare da kyaftawa ba. "Ma'anar hakan shine ke ka aice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun addara! Kamar yadda yazo a allon tsafin su, duk da bamu da tabbaci Allah kadai yasan gaibu amma In Allah Yasa hakan ya zamana gaskiya ne kinga kenan wannan wata hanyace da zaki yi amfani wurin kawo karshen su, Ki zamar masu mummunar addarar da zatayi silar tarwatsa su. maganar salsabeel ta farfado da tunaninta na son kawo karshen kurkukun addara amma bataji zata iya tursasa danish don ya yi masu jagora. Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"ya Salsabeel na fahimce ka, amma bana jin zan iya tursasa ma Danish, Ina matu ar jin tsoron in jefa rayuwar shi cikin hadari, in har wani abu ya faru dashi bazan ta6a yafe ma kaina ba, idan ma zuwan ya zama dole sai da shi to ku ha a da ni. kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya tokare makogwaronta nan hawaye suka dinga zarya kan kuncinta. Zuciyarshi taso ta karaya da maganarta, Shesshekar kukan tane Ya fargar da shi, Cikin sigar lallashi yace"in har kin yi imanin cewa Allah shi ke tsare bawansa bai kamata kina tunanin Zai rasa ransa a gurin Yaki ba, ay bashi kadai zaije ba Unaisah baga mu ba ko mu baki damu mu mutu ko muyi rai ba? Wlh Unaisah jininmu akan akaifa yake babu gudu ba ja da baya ko da zamu rasa ranmune sai mun yi ya i da dukkan karfin mu, mun dogara da Allah kuma munyi imanin shine zai bamu nasara akan kyakkyawar niyar da muke da ita na ganin mun kawo karshen zaluncin kurkukun kaddara...." Kwata kwata bata gane me yake cewa ba, ita fa damuwarta akan Danish ne cikin karyayyar murya tace"ni abun da nafi jimawa har yanzu shi ba musulmi bane, I don't want him to lose his life as an unbeliever! ya makomarsa zata kasance?..." ta fa a tana kallon fuskarshi da idanunta wadanda suka ka a jawur da su shi kanshi abun na damun shi, baida burin daya wuce Danish ya musulunta ko dan ya tsira da imaninsa, amma yasan bamai yiwuwa bane in ba wani iko na Allah ba, saboda wadannan evils din na jikin shi. "Mu cigaba da taya shi addu'a in sha Allah zai musulunta, ni dai yanzu damuwana ki yi kokari kisa ya amince mana..." kifa kanta tayi jikin pillow, sam bata son maganar gani take k amar tursasa mata yakeyi don ta ingiza danish ga fadawa halaka.. Sarai ya fahimci daga ita har Danish din Giyar soyayyace ke dibarsu, shiyasa har suke neman su bijire.. Gwiwar shi ta sage, cike da rashin kwarin jiki Ya mi e ba tare daya kauda idanun shi daga kallon ta ba Yace"banzo nan donna bata maki rai ba, kodan na tursasa maki nazo ne don mu hada hannu gurin cimma burin da muka dade muna jiran ranar da zamu aiwatar da shi, kada ki manta nayi ma mahaifiyata alkawarin zan kawo karshen zaluncin Elders bayan haka kema kin min alkawari watakil Yanzu kin manta nasani..." wani irin radadi take ji acikin zuciyarta tana maijin bakin cikin gaza amsa mashi bukatar shi "Zan tafi Unaisah, ki zauna kiyi nazari da hankalin ki, Zan jira har zuwa lokacin da zaki aiwatar da abun da na sanyaki, bana so kiyi danasani mara amfani..." ya fada tare da juyawa ya nufi kofar fita daga dakin Harya ruke handle din Ya dan dakata tare da juyawa ya dube ta, still bata dago da kanta ba sai kuka take yi "Kina tunanin zaman Danish agidan nan shi zaisa Ya tsira da ranshi? Abunda baki sani ba dokar elders ce duk wanda ya san sirrinsu dole su kashe shi, in har baije Ya farmakesu ba, to su zasu farkama ke shi ne akowani lokaci" ya na fadan hakan yasa kai ya fuce Fitar shi keda wuya ta kuma fashewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, maganar salsabeel ta fara tariyowa farkon haduwarsu agidan kurkukun addara _inaso ki aurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo arshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matu ar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ru o a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka_ _"NAYI MAKA AL AWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo arshen su, Bi'iznillahi_ Tuna wannan yasa ta ara sautin kukan nata. A bangaren Salsabeel bayan ya koma backyard din kamar yadda yabarsu Chief haka ya taras da su zaune suna jiran shi. Bawan Allah duk Ya rasa kuzarin shi, su Unaisah sun bata mashi rai ba ka an ba.. Hankalin su baya akan shi har saida yai masu sallama kafin su ka dube shi, zama yai kan kujera ya sunkuyar da kan shi asa tun daga yanayin shi suka fahimci akwai damuwa.. "Salsabeel ka yi shiru baka ce mana komai ba! Ya kuka are da shi"? Cikin kulawa Taj yai maganar.. Cike da jin nauyin su ya girgiza kai, "Danish ya bani kunya, ban ta6a zaton zai bijire min ba..." tun da suka ji hakan damuwa ta bayyana akan fuskokin su don sun riga sun hasaso karashen zancen na shi.. Rai a6ace Omar