← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 105 OF 247

Sashe 105

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ma ganinta, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshinta, hankalin ta yayi mugun tashi, zuciyarta ta karaya jikinta yayi sanyi, ta gaza yarda da abunda take zargi!! dagaske danish ne ya aikata mata rashin imanin nan? babu tausayi babu imani Yana ganin tana fama da azabar radadin ciwo ahaka Yayi abun da yakeso yayi? Tunawa tayi da lokacin daya wurgar da ita kan gado, Ya sa hannu Ya hambareta har kanta Ya daki pillow, abun ya tsaya mata aranta. Fitowa yayi daga toilet din, ya ago suka hada ido, wani irin faduwa gaban shi yayi ganin kallon tuhuman da take jefa mashi, tuni yasha jinin jikin shi "My man, kaga zoben"? La66anta na kerma ta furta maganar Girgiza mata kai yayi"ban gan shi ba, bansan a ina Ya fa i ba..." Murmushin takaici ta sakar mashi, kafin tace"Ni na ganshi"! da mamaki Ya kalle ta, hannu ta zura cikin aljihun gown din, ta zaro zoben ta mi a mashi "A ina kika gan shi"? ya fa a tare da matsowa kusa da ita, ya mi a hannu zai karba, daddagewa tayi da iya karfinta na karshe ta ware yatsu biyar ta wanka mashi zazzafan mari kan kun cin shi, tashin hankalin da ba asaka mashi rana! lamarin ya gigita shi da sauri ya dafe kun shi, jikinsa na 6ari ya ago amatu ar ru e ya kalli fuskarta...la66ansa na kerma ya furta"my.. Angel? Kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kika mara"? Harara ta watsa mashi da kakkausar murya ta furta"idan akwai abun da yafi mari zanyi maka shi! Mugu Azzalumi, fasiki an iska... " waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata fado asa He was completely confused "Danish me nayi maka dana cancanci haka daga gareka? Danish kaida kanka? Sai yanzu na gane dalilin dayasa ka tsareni jiya akan in fa a maka idan na fara period, dama abunda kake jira kenan, Ina fata yanzu hankalin ka Ya kwanta, tunda ka samu abunda kakeso ...." rushewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai, bawan Allah Yama rasa bakin magana, har yanzu baisan kan me take magana ba, ko ka an baiji zafin marin da tayi mashi na, babban tashin hankalin shi miya faru da ita a daren jiya "Kiyi min bayanin meya faru dake"? Tsawa ta daka mashi kamar zata rufe shi da bugu tace"kana nufin kamanta abunda kayi min? Saboda ba damuwarka bace in rayu ko in mutu ko"? Ta fada tana cije la66anta da hawaye suka ji a su. "Idan ka manta bari na tuna maka, jiya ka shiga dakinmu da daddare...." zayyana mashi komai tayi tunkafin ta karasa gabansa yayi wani irin mugun bugu na tashin hankali, mi a mashi zoben tayi"a jikin zanin gadonmu na tsince shi, ina fata yanzu ka tuna komai....." Runtse idanunshi yayi, wani irin unci yaji aran shi, jikin shi ya hau yin kakarwa kamar wanda Sanyi ya kama . shirun da yayi ne ya ara tabbatar mata da zarginta akanshi.....amsar shi kawai take jira.. Duk da bata bukatar wannan "Bani bane! Bazan Iya cutar dake ba Angel! bansan ya akai zobe na Yaje dakin ku ba..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wlh yafi ta jin radadin abunda akai mata, yaji zafi kamar ya fasa ihu! Wai Angel dinsa ce wani yayi ma wannan aika aikar? "Danish baka ta6a min karya ba sai yau, baka da wata hujja da zaka kare kanka awurina, zoben ka ba afa gare shi ba, balle kace shi yakai kan shi dakina...Danish meyasa kayi min haka? Ko amafarki ban ta6a tunanin zakai min haka ba? A zato na kai garkuwane agareni mai bani kariya a duk lokacin da wani yayi yunkurin cutar dani sai gashi kai da kanka ka cutar dani, saboda idonka Ya makance burinka kawai ka samu abunda kake so ko"? Dafe kanshi yayi da hannu aya saboda wani irin sara masa da yai, afafunsa sungaza daukarsa baisan sa'adda Ya zube kan gwiwowinsa ba. Ya rurru afafunta da hannayen shi, hawaye na fita ya furta"Unaish ki yarda dani! Ban ta6a maki karya ba, bani bane! Bansan wanene yayi maki aika aikar nan ba! Garkuwarki bazai ta6a cutar dake ba, ni aikina shine baki kariya kamar yadda kika fa a" ya fa a yana fitar da huci mai zafin gaske "ki tausayama rayuwata, kada ki yanke min hukunci akan laifin da bani na aikata ba! nayi maki alkawarin zan gano koma wanene yayi miki hakan ..." cikin rauni na murya ya are maganar, yana kallon cikin idanunta. cike da jin tsanar shi ta sa kafa ta buge hannayenshi daya ruke kafarta da su, ta soma ja da baya tana fadin"wallahi bana son ganinka! Ka fita araina Danish! Na tsaneka! Ka 6ata komai, kullum burina in faranta maka rai ashe kai ba haka bane awurinka, abin da baka sani ba ni nema nake na nema mana hanyar da zamu mallaki juna na har iya tsawon rayuwarmu, sai dai kash gajen hakurin ka da son zuciyarka sun ja maka wurga mashi zoben tayi kan kirjin shi, da gudu ta juya ta fuce daga dakin. Jiki amace ya kwanta kan floor, hawaye suka cigaba da sintiri kan kuncinshi, ga wani azababben ciwon kai da yake ji, tuni zazza6i Ya lullu6e jikin shi, aukar zoben yayi a hannunshi Ya kura mashi ido yana kallon shi, ya rasa ya akai zoben yaje dakin su?wa ya kai shi? Wanene Ya cutar mashi da Angel dinsa? sambatu ya fara yi"bani bane! Bazan iya cutar dake ba! Ni garkuwa ne agareki mai baki kariya, kada ki juya min baya, bana jin zan iya rayuwa batare dake ba, Angel kada ki fushi dani bani bane Gaba aya kalamansa acikin kunnanta, tana a durkushe bakin kofar dakinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin lamarin take kamar a mafarki! wai Danish dinta ne yayi mata haka? Wlh ya karya mata zuciya! Ya kunsa mata kiyayyarshi, duk irin burin da taci na son ganin sun rayu a karkashin inuwa aya ya ruguza komai.... Jin motsin mutun yasa tayi saurin share hawayen ta, jiki ba kwari ta mi e daddynta ta hango yana shigowa, da alama Ita Yake nema... Sai da ta fara daidaita nutsuwarta kafin ta sauko down ta nufe shi, sam baiji takun tafiyarta ba, sai dai Yaji ta fa a kan bayan shi ta rungumeshi, bata san sa'adda ta sake fashewa da wani kukan ba, duk yadda taso ta shanye shi takasa har saida Taj yaji, gaba daya yabi ya rikice, kafin yayi yunkurin ruko ta da gudu tabar jikin shi, ta nufi dakinsu ta shiga, a lokacin Batool ta jima da fita, kan gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita. da gudu Taj Ya fa o dakin, Ya hau har saman gadon, jikin shi har kerma yakeyi tsabar rudu da tashin hankali, janyota yayi da karfi ya rungumeta sosai a kirjin shi, muryar shi na rawa ya furta "Unaisah! my Angel! Meya faru? Waya ta6a mun ke? baki da lafiya ne? fuskarta tayi sharkaf da hawaye, hatta temperature din jikinta ya dauki zafi rau. "My Angel meke damunki? Dan Allah kiyi min bayani? Ko baki da lafiyane?" sai da tayi kukan mai isarta kafin ta raba jikinta daga nashi ta sauko daga kan gadon, ta nufi toilet ta shige, jim ka an ta fito da alamun ruwa akan fuskarta...tsayawa tayi nesa da shi tana faman sauke ajiyar zuciya. "Zonan Unaisah" Ya kirata fuskarshi babu walwala, kamar babu laka a jikin ta ta karasa tare da zukunnawa ta zauna kasan gadon, saukowa yayi ya zauna suka fuskanci juna Ya ruko hannayenta a cikin nashi"fada min meke damunki? Meyasa kike kuka? Shiru tayi jimm har cikin ranta bata jin zata iya tona mashi asiri, koda zuciyarta zata buga saboda bakin cikinsa, ta wammace tabar abun aranta. "daddy dan Allah kada ka tambayeni meke damuna, ka tayani da addu'a, in sha Allah zanji sau i.." ta fa a tare kwantar da kanta saman kafadarshi, aura hannun shi yayi akan bayanta yana dan shafa shi cikin sigar lallashi yace"kiyi hakuri duk da bansan meke damunki ba, tun da kin nuna bakison in tambayeki dole in hakura, amma dan Allah kada ki sanya damuwa aranki! Ki kai kukan ki wurin Allah, Nima zan tayaki da addu'a in sha Allah.." lumshe idanunta tayi har yanzu bata daina jin kukan ba... "Daddy, Inaso nayi nesa da gidan nan, na wani lokaci..." tun da yaji wannan maganar Ya fahimci akwai wanda Ya 6ata mata rai, a sannu zai gano koma wanene. dagowa tayi a hankali suka kalli juna, idanunta sun ance sun ka a jawur saboda kukan da ta sha.. "Daddy, Ka kaini part dinka, in zauna gurin Aunty danejo, ko kuma ka kaini wurin aunty Aneelerh dan Allah" marairaice mashi fuska tayi kamar zata fashe da kuka, kallonta kawai yakeyi gwanin bantausayi, arayuwarshi yatsani duk wani abu da zai ta6a lafiyar yarsa, bai son damuwarta. "Daddy kayi shiru bakace komai ba"? Numfasawa yayi kafin Ya furta"magana nakeso nayi dake, shiyasa na shigo gidan nan, sai kuma na taras da abunda Ya 6ata min raina..." "Ka yi hakuri daddy, na daina kukan ay, ba zan kara sanya damuwa araina ba..." ta fa a tare da aro murmushi akan fuskarta. Kwantar da ita ya kuma yi ajikin shi don ta samu relief din abunda ke damun ta.. Calmly ya fara zayyana mata maganar da suka tattauna da su chief "Ita mara lafiyan yar uwarsa ce, kuma kawar auntynki Aneelerh, tana a kwance gadon asibiti kwata kwata bata acikin hayyacinta tun lokacin data rasa yarta da mijin ta, likita yace idan har ba asamo yarinyar da zata iya acting kamar yartaba, to zata rasa ranta ne..." agowa Unaisah tayi a hankali ta kalle shi da alama taji tausayin matar. "Muna so kije a matsayinta Unaisah, nasan zaki Iya!" "Daddy na amince muje asibitin, dama najima ina neman hanyar da zan kyautatama chief, na ji dadi data kasance yar uwar shi, Allah yasa in zama silar samun warakarta .." murmushi taj yayi "Ameen, amma akwai abunda nakeso in ja maki kunne akai! Idan har muka kaiki asibitin kada ki kuskura ki fa a ma wani ina raye! Ko ki bayyana wacece ke! Saboda har yanzu rayuwarmu tana acikin hatsari akwai masu bibiyarmu unaisah!
Chapter 105 · 0% Book details