← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 133 OF 247

Sashe 133

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

saukowa ta fuce daga dakin Zukunnawa tayi agaban drawer chest, ta bu e ta karo chocolate da cookies masu yawa ta tura a jakar hannunta, ta dauko shaving set tana tunanin ko zai bukace su? mezaiyi da su, danish bashi da gashin da zai aske cos ta san shi tun a prison haka halittar shi take bai da underarm hair, hatta fuskarshi smooth take ba gashi, hakanan dai ta sanya mashi a jakar, ta auki sport jersey ta sanya mashi, gani take kamar kayan sunyi mashi ka an, sai da ta kara mashi wasu akai, ta curo paper da pen ta rubuta mashi "I'm back, my man. I hope I find you safe. nayi kewarka, ga tsarabarka nan, Take care of yourself for me." acikin shopping bag din ta sanya mashi letter din, sam ta manta bai iya karatu ba, ita a tunaninta ya fara iyawa tunda daddynta ya fada mata chief ya fara koya ma shi, mikewa tayi da sauri ta fito ta nufi upstairs, a bakin kofar dakin shi ta ajiye mashi kayan, ta sanya hannu tayi knocking kafin ya fito ta watsa da gudu ta sauko down ta dawo bakin room door din su ta tsaya tana leken shi. Lokacin daya fito baiga kowa ba, har zai juya yai tuntu6e da shopping bag din da sauri ya dubi jakar, yayi mamakin ganin ta baisan wanene ya ajiye mashi ba. Zukunnawa yayi tare da bu e jakar, ya fara zaro kayan yana kallon su, akan idon shi letter din ta fado asa da sauri ya dauka ya bu e yana kallon rubutun shiru yayi jim ya rasa gane me aka rubuta bawan Allah, Ya shafe mintuna yana harhada haruffan amma ya gaza karantawa, handwritting in ta ya ha u saika rantse da Allah babban mutunne Yayi rubutun saboda warewarta. Unaisah dake a la6e tana le en shi fuskarta auke da murmushi sai dadi take ji amma data fahimci ya kasa karantawa sai taji wani iri aranta, daga inda take ta yi mashi gyaran murya kafin ya ago da ido ya kalleta tayi saurin juya mashi baya ta ruke qugu da hannu, ta yi mashi hakanne don yasan cewa itace ta kawo mashi kayan. Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, nutsuwa yayi yana kallon bayanta har saida ta shige daki kafin ya tattara kayan ya maida a cikin jakar ya mike da sauri ya shiga dakin shi bayan ya daura jakar kan gado, ya auko paper da pen ya daura kan bedside drawer ya fara kokarin yin rubuta, bawan Allah idan yana so ya rubuta Ni sai ya fara daga Na ni no nu ne kafin ya canko wadda ta dace ya sanya.. Dakyar ya samu ya rubuta mata letter in ya mike da sauri ya fito ya sauko down Yaje bakin kofar dakinsu Ya ajiye mata tare da yin knocking in kofar, kafin ta fito yayi saurin komawa upstairs Ya tsaya yana jiran ganin ta Tana fitowa taci karo da letter din daya ajiye mata, zukunnawa tayi tare da daukar takardar ta bu e ta... "Welkam bak hom, i miss yu so much, tanku" hawaye ne suka ciko idanunta wani irin tausayinshi ne Ya kamata da sauri ta dago ta kalle shi hannu ya aga mata, a hankali itama ta aga mashi hannu sai yanzu ta gane ashe shine ya tura mata text message awayarta lokacin da tana a hospital, hartana dariya tayi zaton karamin yarone ya dauki wayar babarsa.. Juyawa tayi da sauri ta koma cikin dakin su, ta dauki wayarta dake kan mirror, ta kwanta kan gado ta fara scrolling ta shiga messages dinta, murmushi tasaki tana kara karanta sakon shi bata san sa'adda kuka ya kubce mata ba...cusa kanta tayi jikin pillow tay kuka mai isarta kafin ta share hawayenta ta dago, ta kalli screen din wayar, yanke shawarar kiran shi video call tay, da number din daya tura mata sako ta danna mashi call yana shiga yai picking"Turn on your Wi-Fi, I'll call you on a video call." ta fa a tare da katse kiran bata jira amsar shi ba, fatanta Allah yasa ya iya kunna wi-fi din, ta kunna na wayarta har zata danna mashi video call, Unexpectedly, taga kiran shi ya shigo via facetime. Picking tay tare da kanga wayar saitin fuskarta ta ura ido tana kallon doguwar fuskar shi abun da ya aure mata kai ya lumshe idanun shi, da alama akwance yake kan gadon shi ya tada kai saman pillow kamar yadda tayi. an yi mamakin canzawarshi, kamar akwai rama ta wurin kwarin idanun shi fatar wurin tayi jajir ga zira ziran eye lashes dinshi da suka awata kewayen idanun, la66an shi sun bushe amas launinsu ya ara ciza wa, ga wani haske da yayi skin dinshi har salki take, gaba aya ta shagala da kallon shi har saida taga ya fara kokarin bu e idanun shi kafin tai saurin kau da nata gefe, kallo aya da yayi mata saida yaji wani irin yanayi atare da shi, ta canza mishi ta ara yi ma shi kyau kamar yaune rana ta farko daya fara ganin ta haka ya nutsu yana kallon soft pink lips dinta, kafin ya maida duban shi ga grey eyes dinta, ta i yarda su ha a ido sai dai ta wutsiyar idonta take satar kallon sexy face dinsa ta screen din wayar.. "Tell me, have you forgotten me? Are you still angry with me? Or have you stopped loving me?" Sanyayyar muryar shi ce ta ratsa kunnanta, har saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta furta"bana fushi da kaina, ban manta da kai ba, kana araina, kana tunanin daina sonka abune mai sau i agare ni"? Lumshe idanun shi yayi, yana jin nutsuwa tana shigar shi, kalamanta sun sanyaya zuciyar shi. "If you're even thinking about that, you should stop" ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kamar yadda nayi maki alkawari bazan ta6a karyawa ba, amma inaso mu dinga yin magana ko da ta waya ne pls give me permission to call you every day" ya fa a yana kallon fuskarta yadda kasan suna aguri aya. "Okay, I give you permission, but you will call me only two times, and you can send me a message anytime, idan na gani I will reply to you immediately. After that, I don't want anyone to know what is going on between me and you, in har muka ha u a falo ko hanya ta ha amu indai ina atare da wani zan iya yi maka magana kaima haka..." tana magana idonta na kallon gefe aya kwata kwata bata son su ha a ido saboda yanayin da yake jefata kuma idon tana kallon shi, sai zuciyarta ta dinga tariyo mata abunda ya faru adaren ranar daya shugo dakin su. Shiru taji bai amsa mata ba, sai ma motsin bu e leda da taji a kunnanta, aranta ta ayyana ko meyake ki? ko dai ya ajiye wayar ne? A hankali ta an saci kallon screen din karaf idanunta suna shiga cikin nashi lokaci aya taji fa uwar gaba. Hankalinshi kwance yake kallon ta, Yana cin chocolate din data kawo mashi, yanayin yadda yake moving lips dinsa, sai taji wani iri zuciya da sake sake sai taga kamar da gangan yake don ya rikitar da ita cos he looks so sexy a yadda yake shan chocolate in har wani lumshe idanun shi yakeyi alamar dadin yana kai mashi karo, sam takasa janye idanunta daga kallon lips dinsa, hatta yanayin fitar numfashin ta saida ya canza lokaci aya ta nemi zaucewa da sauri ta kifa wayar jikin pillow tayi shiru tana jin wani irin abu mara misaltuwa ta rasa gane me yasa take jin hakan? chocolate kawai ya bude yana sha duk ta rasa sukununta har wani shau i take ji a jikin ta. "Hello, Angel? Are you there? Muryarshi ce ta fargar da ita Numfasawa tayi har ta fara motsa lips dinta zata bashi amsa muryar daddynta ta katse ta"daughter! Kina ina? Shi ne kin dawo ko ki neme ni ko"? Cutting din kiran tay, ba don ta gaji da kallon shi ba, ta mi e da sauri ta sauko daga kan gadon, ta nufi door room din ta bu e, yana atsaye bakin kofar fuskarshi dauke da murmushi yake kallonta"welcome back, my Angel" hugging dinshi tayi, fuskarta dauke da murmushi ta zagayo da hannayenta kan bayanshi"daddy ina wuni ya aiki, Ya aunty danejo na, wlh nayi missing dinka, kana araina tunda na dawo nake ta dakon zuwan ka.." dago da kanta yai daga kirjin shi ya dubi fuskarta dakyau"nima nayi kewarki, ay na yi zaton zaki kira ko awaya ne ki fadamin kin dawo gida, ni gaskiya ban yarda kinyi missing dina ba, kina can kin samu uwa kin manta dani ko"! Ya fa a da zolaya Girgiza kai tay"a'a daddy, ba haka bane, ay bani da tamkarka a duniyar nan, mu shiga ciki kaga kayan da chief ya siya min..." Taja hannun shi suka shiga dakin, cike da zumudi ta dauko shopping bags din ta bu e ta fara curo kayan daya bayan daya tana nuna mashi Waro ido ya anyi alamar mamaki yace"Eyeh gayu mutanan Allah, duk ke kadai wannan? Amma naji dadi ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi Allah Ya ara mashi bu i da daukaka" Fuskarta dauke da fara'a tace"ameen daddyna, wlh nima nayi mamakin kayan daya siya min amma fa bani kadai ba hada su Batool yace in daukarmawa inyi masu tsara..". "Kin nuna ma auntynku" "Eh, harma ta dibar mana chocolates da cookies sauran kayan tace mu ajiyesu adaki kafin lokacin da zata raba mana" Murmushi yayi har cikin ranshi yaji dadin jin chief ne ya je da ita mall da alama burin shi Ya kusa cika na ganin Ya kulla alaka mai karfi atsakanin su. "Daddy, na jima banga mutun mai mutunci irin chief ba, yana da saukin kai, ga shi wayayye ni dama can inason mutum irin haka..." ta saki baki tana surutu cikin rashin sani ta zazzago bras daga cikin shopping bag din dake ruke a hannun ta. Waro ido taj yai cike da zolaya ya furta"Subhanallah, daughter wannan fa na wanene"? da sauri ta dube su, wata irin kunyace ta kamata, da sauri ta sunkuyar da kanta kasa
Chapter 133 · 0% Book details