Sashe 6
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 7 min read
Allah baison zuwa kodan gudun a ci mutuncinsa, amma saboda yana son ya faranta ma baba obie yasa shi cewa "In sha Allah tare dani za'a bu e taro" Murmushi baba obie yai masa"Naji dadin jin hakan rabin raina. Jan shi da fira baba obie yai, kamar wani abokinsa, tuni jazz ya saki jikin shi. UMMIN AMERICA Duk Yinin Yau Bata fito daga aki ba, ta killace kanta tun safe bata jin da in zuciyarta, duk ta untata kanta, tayi jiran zuwansu unaisah su shigo don su e6e mata kewa sai dai shiru babu alamarsu, tuntana sa ran ganin su har ta fidda ranta, ta undundune kanta cikin lallausar bargonta, Sallah ce ka ai take tada ta daga saman gado Har ta fara nutsawa cikin baccinta kwatsam wayarta dake ajiye kan nightstand ta soma yin ruri, da wata irin kasala ta ago da kanta, sumar kanta duk ta hargitse babu gyara, laluba Hannu tayi ta kamo wayar batare data duba sunan mai kiranta ba tayi picking tare da kara wayar a kunnanta. Sautin Muryar NATASHA ne ya Daki Dodon Kunnanta"nayi fushi Kin manta dani ko"? ta fa a cikin harshen turan ci. Muryarta da kasala Ta furta"ba haka bane Natasha, Kina araina, dake nake kwana dake nake tashi" "Ban yarda da kalamanki ba Ummi, Idan Dagaske kinyi kewata meyasa baki kirani ba? Sai da na kira ki ni da na damu dake ko"? Shiru tayi na an wani lokaci har sai da Natasha Ta furta Naji kinyi shiru tukunna taja numfashi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"bansan yadda zanyi maki bayani ba NATASHA, ni ka ai nasan halin da nake aciki, ina cikin damuwa, Ina cikin ka aici, Rayuwata a untace take natasha, bani da wani an ci, ba wanda Ya damu dani, tun safe bana jin da in jikina babu wanda ya le aki na don Yaga awani hali nake aciki.... "Muryarta na rawa ta are maganar, tamkar zata fashe da kuka, hakan Ba aramin aga Hankalin Natasha Yayi ba, Jin sautin miryar aminiyarta da alamun matsananciyar damuwa.. Cikin saurin mirya ta furta"Ummi, muyi magana ta video Call, Inason naganki ko hankalina Ya kwanta" "Toh, amma kafin nan zan shiga toilet, an mintuna ka an Idan na fito zan kiraki" natasha ta amsa mata da toh, bayan ta yi rejecting Kiran, ta daura wayar kan drawer, kafin Ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6a da shi, Jallabiya ce a jikinta launin dark ash, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet, After Some minutes ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa, Laptop dinta dake ajiye kan desk ta dauko ta koma kan gado ta zauna daga tsakiya ta ajiyeta agabanta, kafin ta bu e ta soma sarrafata, Natasha ta kira video Call nan take ta aga, kallon juna suka soma yi tamkar suna a wuri aya, Natasha tana a kishingi e saman beach chair dake a ga6ar teku, babu suturar mutunci a jikinta, dama ita bata cika son sanya suturar da zata rufe mata tsiraicinta ba, tafi sha'awar ta sanya pant da bra. cikin harshen turanci suke yin magana. "Yanayin fuskarki Ya tabbatarmin da bakyajin dadin Ummi, Ki fa amin meke damunki? Waya ta6a min ke"? Yamutsa fuska Ummi tayi tamkar batason furta maganar tace"kamar yadda na fa a maki bana jin da in jikina, narasa gane meke damuna, amma ina da tabbacin hada ka aici, ban ta6a untataba Irin na Yau, Jin kaina nake tamkar Ina a prison" Cikin kulawa Natasha tace"meyasa ba zaki janye aikin da Commender Ya baki ba? Ummi dama ni nasan bazaki Iya jurewa ba, tuntuni naso In garga eki saboda ba zaki Iya ba, mu da muka saba da yawo kullum sai mun fita wurin abokan harkar mu, taya zaki Iya jure rayuwar kulle"? Ta fa a tana mai dubanta, Dafe kai Ummi tayi da hannu aya"Har yanzu banyi danasanin kar6ar aikin kula da yaran nan ba, Saboda Inaji araina akwai wani alkhairi atattare da zamana da su, shiyasa bana danasani, ni kawai abunda ke damuna rayuwar kullance ke banaso, Yana untata Rayuwana, hada arin Yaran da suke ebe min kewa basu zo wurina ba yau, ni kuma nakasa tashi naje gare su" fuskarta a yamutse tayi maganar "Har Yanzu ba zaki fahimce ni ba Ummi, Ni inaso na kwatarmaki an cinki ne, Inason farin cikin ki, Kina bu atar abokan Harka, kefa ba irin matan da za'a untata ba ne...' tunkan Natasha ta are maganarta, ummi tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Akwai labari mai da i, nasan idan na fada maki zakiyi mamaki" Ta fa i hakan ne don batason Natasha taci gaba da yi mata zancen Ajiye aikin da take Yi. "Na osa naji labarin nan fadamin mana" ta fada tana sakin murmushin sha iyanci. "Mutumin Ya ziyarce ni Har cikin gidan da nake," Waro idanu waje natasha tayi da mamaki ta furta kina nufin Big Boss? Ya ziyarce ki? aga mata gira ummi tayi alamar eh. "Amma ya akai ya iya shigowa gidan Jami'an Isod, bayan kin fa amin acikin sharuddan da suka baki, babu shige babu fuce basu bu atar wani naki yazo inda kike, har zuwa lokacin da kika kammala Yi masu aikin su" ta fa a a kagare da son jin arashen xancen. Dariyar sha iyancin Ummi tasaki tamkar babu damuwa aranta"kinsan mutumin na dabanne, ni kaina bansan tayaya akai ya shigo gidan ba, Har tambayarshi nayi sai yace min idan na yarda dashi indaina tambayarsa.... " dariya natasha tayi cike da nisha i tace"Namijin Duniya, Nayi kewarshi ummi, kullum cikin begen ganinsa nake yi, yayi min nisa yanzu, ba kamar lokacin da nake yi mashi rainon babynsa Pretty ba, tun da Ya kar6i Yarinyar sai nayi dagaske nake ganin shi, ko wayana baya picking... " kafin Natasha ta are maganar Ummi tayi hanzarin tarar numfashinta da cewa"wai ina yarinyar take ne? Na jima ina son na tambayeki ita, nayi missing dinta, tun ranar dana fara Yin tozali da ita naji kaunarta ta shiga raina, duk da bata jin magana amma tana da kyau" Natasha tace"hmmm, Ummi Ya raba ni da ita, tsawon watanni, duk idan na tambayeshi ina baby Pretty na sai yace min ya mayar da ita wurin mamanta, har alfarma na nema awurin shi akan ya amince min inbiyo shi nigeria saboda ina son ganinta amma Ya hanani.... "muryarta na rawa ta are maganar idanunta sun cicciko tab da kwalla. "Ummi Inason yarinyar nan, Ina aunarta, nayi fatan ace ni na haifeta ko dan saboda mu kasance atare har abada, mun sha u da juna, na saba da ita, Amma yayi min yankan auna.... " tunda tafara magana ummi ta natsu tana kallon fuskar Natasha ta cikin screen din laptop tamkar suna awuri aya. "Ummi nasan zaki Iya taimaka mani, tunda Yana kaunarki, Yasha fadamin ke kadaice kike Iya sarrafashi son ranki, please kiyi amfani da damar da kika da ita, Ki lalla6a shi Ya dawo min da baby pretty" cikin sanyin Murya ta are maganar, Ummi dake kallonta tuni tausayinta Ya kamata, bata ta6a ganin Natasha tana zubar da kwallarta akan wani an adam ba sai akan babyn da take mutuwar so, tasan da irin kaunar da take yima yarinyar a lokacin baya. Cikin kwantar da murya ummi ta furta"Am sorry, Kinsan bana son ganin hawayenki, zan Iya yin komai akanki, saboda halaccin ki agare ni, Kin wuce awa a wurina sai dai ar uwa, saboda kin kaunace ni a lokacin da kowa yake guduna, abun da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, zanyi kokarin ganin na shawo kanshi don ya dawo maki da babyn ki" Murmushin farin ciki natasha tasaki tana fadin"thank u ummi, nasan zaki iya yin komai saboda farin cikina, shiyasa nake ara kaunarki, ina nan ina shirye shiryen zuwa Nigeria saboda ke" Martanin murmushin ummi ta mayar mata, "Ina handsome boy din nan, namanta ban tambaye ki shi ba" "Bashi da lafiya, Yana a kwance" Yamutsa fuska Natasha tayi"najiye mashi ba dadi, Allah Ya bashi lafiya, har yau ban manta da fuskar shi ba" Murmushi Ummi tayi mata" dama ke ay bakya mantawa da abu mai kyau, naga kin kirani da layinki Na england, hakan na nufin kin koma gidanki"? aga mata gira tayi alamar eh. Jinjina kai ummi tayi, shiru sukayi na wani lokaci yayin da suke kallon juna batare da yaftawa ba. "Kin tsareni da ido Kina kallona, Kamar akwai wani abu da kikeson fadamin" acewar natasha ta fa a tana age mata gira. Dariya Ummi tayi, Harta Bu e baki da niyar furta magana, Sautin knocking ofar da akayine Yasa ta fasa yi mata maganar, "Zan Kiraki Anjima Ki kula min da kan ki" "Bangaji da jin muryarki ba ummi, amma shikenan zan jira zuwa anjiman inma kin manta baki kirani ba, Ni zan Kira ki, ki kula min da kanki and pls ki daina sanya damuwa aranki" a hankali ummi ta furta mata"toh, nagode da kulawarki agare ni" bayan sunyi sallama, Ta kashe video Call din, ta sauko tare da laptop din a hannunta, ta nufi desk ta aurata, kafin ta shiga wurin closet dinta, mayafi ta daura akanta.