← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 148 OF 247

Sashe 148

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ya fa a tare da age mashi gira, arfin halin mutum ya aure mashi kai ko kunya bai ji ba Ya kure karamar yarinya kan gadon ta. "Amma dai baka da hankali, Don ubanta Ya kiraka ka duba kafiyarta sai yace maka ka shigo har dakinta saman gadon ta? meyasa ba zaka tura me aiki ta kira maka ita ka dubata a falo ba? Hakan da kai ka kyauta? Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. Ganin dr shureim zai raina mashi wayau yasa shi saukowa daga kan gadon Yana wani bu e kafadunshi Ya tsaya agaban shi"meye naka aciki huh? Yakamata kasan irin kalaman da zaka furta min, Ni ba sa'an yin ka bane, kada kace zaka shiga hurumin aikina, ba yau na fara ba! kuma umarnin mahaifinta nake bi" A harzuke dr Shureim yace"oh shi uban natane Yace ka shigo dakinta har kan gadon ta don kayi mata allura kuma haka ake allura abi a danne mutum"? Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma. "Malam ka tsaya a iya matsayinka, nima in tsaya a nawa, tun wuri ka fuce daga dakin nan tun kafin na 6ata maka rai"! A kausashe Ya fa a Yana Huci saboda baya aukar raini, daga gani yana ji da karfi, juyawa yai da niyar ya koma kan gado saboda kunya bata ishe shi ba, a zafafe dr shureim Ya dam i Strong Arm dinsa, a sukwane dr mark yai mashi wani kallo mai nuni da kashedi "Sakar min hannuna! Karka kuskura ka bari na maimaita abunda nace"! Girgiza kai dr shureim yai duk da ya an sha jinin jikin shi amma baya jin zai iya bari dr mark Ya koma kan gadon zeenatu da sunan zai mata Allura, ko ba dan kishinta da yake ba hakan bai dace ba kwata kwata Hankalin Zeenatu ba karamin tashi yayi ba jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda sanyi ya kama cikin shesshekar kuka tace"yaya shureim ka yale shi dan Allah, wlh idan daddy ya ji ka hana ya dubani ranshi zai 6aci, ni allurar ce bana so tun da akwai magani ya kyale ni in sha" idanunta sun ka a jawur Wata irin zufar 6acin rai ce ta wanke fuskar dr shureim Ido cikin ido suke kallon kallo tsakanin su, Taurin kan dr shureim da kafiyarsa sunyi matu ar daure mashi kay, mutane da dama suna jin shakkar shi sai gashi yau Allah Ya hada shi da shureim "Yaya shureim na ro e ka, ka sake shi, bana son tashin hankali" "Wallahi ba zaka dubata ba! Muddin ina numfashi, wannan wani irin yahudanci ne? Daga kai sai yarinya adaki saboda rashin ta ido har kan gadonta"? Dr mark ya gama hasala Har yayi wani yunkuri Zai kai mashi naushi Zeenatu tay saurin saukowa daga kan gadonta, ta fa a tsakanin ta riqe dr shureim tana kuka. Da ace Zeenatu bata yi gaggawar raba tsakanin su ba, da Allah kadai yasan me dr mark zai yi mashi saboda ya fusata shi. Sassauta fushin fuskarshi yayi, tare da kallon zeenatu da ta kankame shi, hankalin shi ya an tashi da jin zafin jikin ta Ganin mayen kallon da mark ke binta da shine yasa shi juyawa da zeenatu suka bashi baya. Shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da zaro wayar shi ya danna ma Alhaji musa Kira bugu uku Ya aga. "Sir, Wannan balaraben na gidan ka ya hana in duba lafiyarta saboda kawai Ya iske ni akan gadon ta ina kokarin yi mata allura shine ya rufe ni da fa a yana gaya min magana mara da i" ya fa a yana kallon bayan dr shureim, sarai yasan sunan shi amma saboda girman kai Ya kira shi da sunan balarabe on the other hand Alhaji musa yace"Dr shureim Ya dawo gidan ne"? "Yeah, shi nake magana akai, Yanzu haka muna adakinta" "Okay, mark ka tafi kawai, i will call you later" ba don yaso ba ya amsa mashi da Okay" duk suna sauraron shi abun da ya ara bata ma dr shureim rai jin ya fada ma alhaji musa yadda ya iske shi adakin batare da jin nauyin hakan ba, hakan na nufin dama ya saba zuwa dakin zeenatun ya hau gadon kuma da sanin Alhaji Musan. Harara dr Mark Ya watsa ma bayan shi, tare da jan Tsoki ya fuce daga akin. Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, tallabo fuskarta yai da tafukan hannayen shi, idanunta amarairai ce ta kalle shi wani irin tausayinta ne ya kama shi, kumatunta sunyi ja, pink lips dinta sun kumbura daga gani ta jigata taji jiki ba ka an ba "Me ke damunki"? Muryarta da shagwa6a tace"ciwon ciki, daga fitowana daga wanka, na fara jin ciwon ciki yaya shureim nasha wahala kamar zan mutu har fadowa nayi daga kan gado, sai da Tani ta shigo ta iske ni kwance kasa ina murza cikina.. Shine ta kira daddyna awaya ta fada mashi shi kuma ya kira mark don ya dubani ni, ni kuma bana son allura" Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. Calmy yace"amma zeenatu why baki ce ya jira ki fito falo ba? Hakan ya dace ya shigo har dakin ki kan gado zai duba ki"? La66anta na kerma tace"yaya shureim ni banma san lokacin daya shigoba, ina kwance kawai na gan shi akaina, dama haka yake yi min in dai zaizo dubani baya tsayawa falo aki yake shugowa, kuma daddy da mommy sun sani..." Girgiza kai yai sha'anin rayuwar gidan uncle nasa sai du'a i, yafi jin haushin Tani da ta kira Alhaji musa, sai kace mami bata agidan ay da ta sani ta tada ta daga baccin da duk hakan bata faru ba. Ganin kamar damuwa akan fuskarshi yasa tace"ya shureim ranka ya 6aci ko"? Dakyar take magana saboda cikinta dake mata radadi, Girgixa mata kai yai"bakomai, ina maganin naki" da hannu ta nuna mashi kan mirror Juyawa yai ya nufi closet dinta ya dauko mata abaya ya mi a mata, hannunta na kerma ta kar6a tasaka a jikin ta. "Kin ci abinci" "Bana jin yunwa azu da safe na cika kina" "Okey, ki zauna ki jira ni" make mashi kafada tay"dan Allah kada ka tafi kabarni ni kadai" "Ba tafiya zanyi ba, ruwa zan dauko" amsa mashi tay da toh ta zauna gefen gadon tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannun shi ruke da Cup din ruwa ya zauna ya taimaka mata tasha maganin ganin yadda hannunta ke kerma bayan ta kammala sha, yasa Yace ta kwanta ta huta, marairaice mashi fuska tay da shawaga6a tace"so kake inyi bacci donka tafi kabarni ko" Yanayin yadda takeyi mashi magana ba karamin kashe mashi jiki ya ke yi ba, ba zai juri kallon ta ba. "Ba tafiya zanyi ba, zan koma falo," mi ewa tay"nima zanje falon" "Pls ki kwanta ki huta, babu lafiya a jikinki" Kuka ta saka mashi"haba ya shureim nagaji da zama ni kadai, ya kake so nayi da raina? nasan tafiya zakai kabarni..." lallashinta ya farayi"ya isa haka ki daina zubda hawayenki bana so, Idan saboda ni ne muje falon tare saiki kwanta kan sofa, in har hakan zai kwantar maki da hankali" ajiyar zuciya ta sauke ya zaro hanky daga aljihu ya share mata tears din fuskarta, ya ru o hannunta suka fito daga dakin ________________________________ A bangren su Aneeleerh har wuraren biyu na rana suna agidan, Sun Mori lokacin su tare da su Unaisah sallah kadai ta tadasu, sun sha fira da su kamar awayansu, sun ebe masu kewa ba kadan ba, musamman Aneelerh taji dadi tayi farin cikin ganin yadda Junaid Ya saki Jiki da Unaisah in a short time su ka shaku da junan su, wasan doki suka dinga yi mashi ita da Batool, akan bayanta ta aura shi ta dinga rarrafe tana zagaye sitting room din batare da gajiyawa ba, Sai murna yake yana fadin doki sukuta sukuta. Aneelerh tasha ruwan mamaki Ganin Yadda Yake ti ar dariyar, yaushe rabon da ta ga dariyar Junaid tun ranar da Ana ta 6ace ko murmushi bayayi ga iwuya amma yau ya sake kamar bashi ba, har ta fara tunanin in suka koma gida zata lalla6a shi cikin lallami ta tambaye shi meya faru da ana aranar watakil ya fada mata tun da taga bakin shi ya bu Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. har video Benazir ta auke su da wayarta saboda sun burgeta taji da in walwalwar da su ke yi cikin nisha i bayan sun gama yi mashi wasan dokin, Unaisah ta daure idanunta da mayafinta ta dinga zagaye dakin tana neman su, Batool taja hannun junaid suka dinga garata sai da suka wahalar da ita dakyar ta cafko baby junaid ya dinga ihu Yana tsalle yace mata shima ta aure mashi ido yayi wasan, ta cire mayafin ta aure mashi idanunshi yadda bazai ji zafi ba, kamar makaho haka ya rin a mi a hannu ya na laluban su da gangan Unaisah ta je gaban shi ta tsaya don kada su wahalar da shi, cafko rigarta yai da hannayen shi ya ankameta yana fadin ya kama ya kama. Duba agoga Aneelerh tayi kafin ta kalli Benazir"yakamata mu tafi, kada mami taji na dade" sai lokacin Benazir tace"yanzu abun hawa zamu hau mu koma? nasan ko na kira dr shureim ba lallai yazo ba saboda rashin lafiyar zeenatu..." ta fada tare da ta6e baki Murmushi Aneelerh tay saboda ta gano me take mawa "Pls ki kira mijina ya maida mu gidajen mu" cike da zolaya tace"ki dai iya bakinki, Kada babyn naki taji kina kiran sunan ubanta da sunan mijinki, Yanzu ki tada mana 6alli" murmushi Benazir tay tare da kallon su Unaisah dake a zaune kan rug sun gaji da wasan hutawa suke. Waya ta curo ta danna ma Taj kira tana fara ringing yai picking, Tunkafin tay magana Yace"Aneelerh ykk ya su Unaisah, Ina fata kunji dadin kasancewa da su"
Chapter 148 · 0% Book details