← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 28 OF 247

Sashe 28

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

*Daga Al alamin Boss Bature *Littafin kurkukun addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 13 Complete Novels Elite Admin May 29, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~ BOSSLADIESWRITERS ~Takun arshe An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ Cikin muryar kuka taci gaba da cewa"Idan ba ku son ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta sun sanyaya zuciyoyin wasu daga cikinsu, Hakika unaisah ta tafi da imanin wasu daga cikin su, Har mamakin ta su ke yi yarinya arama ga iya tsara kalami uwa uba gata kyakkyawa da ita, ba karamin jan hankalin su Captain yasir tayi ba, sun kafe ta da idanun su kamar za su ha iye ta. Fashewa da kuka Jemimah tayi muryarta da gunjun kuka ta ke fadin "wallahi babu inda zamu je, don baku san wahalar da mu ka sha ba mu ka yi gayu hada gyaran gashi saboda mu nuna maku, shi ne ma zaku kore mu, to wlh ba zamu tafi ba... " a fa a ce ta fa a tana nuna su da yatsan hannun ta, Hankulan su gaba aya ya koma kanta, arama da ita sai masifa, idanun ta sun yi jawur da su, ta harzu a, dama ya lafiyar giwa, tsana da tsangwama da zuluncin da akayi masu arayuwarsu ya an ta6a lafiyar kwalwarsu, silar maganganun da ake fadi ayanzu ne ya fara motsa haukan kansu, da sauri Unaisah ta janyo jamimah ta ameta a jikin ta cike da fargaban kada ta ja masu jaraba. Dafe goshi Azeeza tayi da hannun ta dake kerma kerma cikin wani irin yanayi na jin tsoro da fargaba ta soma magana muryarta da shesshe ar ku ka "Inna... lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ni dai mu koma gida, ku mai dani gida, ba su san mu, ba su son ganin mu, za su iya cutar da mu....' ba ta are maganar ba, Sajeed yai hanzarin janyota tare da rufe mata fuskarta jikin laps dinsa. Sautin shesshe ar kukan su ya cika hall din, mazan cikin su ne kadai ba su karaya ba, sai dai hankulansu ba a kwance ya ke ba, Mom Turai sarkin tausayi zuciyarta ta karaya ita da Hajjaty har sun fara sharar kwalla saboda tausayi ne da su, ga kaunar yaran da ta ar su a zuciyoyin su, da ace suna da damar da zasu ja su a jiki su rungume su da kuwa sunyi hakan. A hankali unaisah ta aura idanunta akan chief owais, mutumin da bata jima da sanin fuskarsa ba, duk da babu kwanciyar hankali atattare da ita sai da taji ya kwanta mata arai saboda jajircewarsa akan su. Kamar yarda take kallon shi haka shi ma yake kallon ta, har cikin zuciyarsa bai ji dadin zubar hawayen su ba. "ba laifin ka ba ne, abun da akayi mana, sai dai inaso ka sani bakowane zai fahimce mu ba ko ya kaunace mu kamar yadda ku kayi mana, zamu tafi kawai....." ta arasa maganar ananun la66anta na kerma ta ru o hannun batool da na jemimah har zasu juya muryar Sir mubarak ta dakatar da su. "Duk da bansan su wanene ku ba, ni dai kun kwanta min araina, kun sace min zuciyata, don haka ban gaji da ganin ku ba, ina yi maku maraba da shigowa family din mu...." a ru e su hajiya saratu suke kallon Sir mubarak, wanda fuskarsa take auke da murmushi yayin da yake kallon su. Pravin dake ta faman mazurai, jin maganar sir mubarak yasa shi jin bakin ciki da takaici tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, kwata kwata babu kwanciyar hankali a tare da shi, duk ya rasa sukuninsa kamar wanda yayi ma sarki arya, burin shi a kore su daga hall din. Sheikh Imam dai lamarin nasu ba karamin mamaki yake ba shi ba, kallon su kawai ya ke yi, Sam baiji dadin halin da su ka jefa yaran ba. "Meye ribar ku idan kun 6ata ran wadannan bayin Allahn? Farin ciki ku ka yi ko bakin ciki da kuka sanya su zubar da hawayen su? Idan ya'yan ku ne a irin halin da ku ka jefa su za ku ji dadi ne? Daga ni har ku bamu da tabbaci akan abunda muke zargin su da shi, don haka yakamata mu kyautata masu zato, sannan shiekh imam yayi mana bayani, babu wanda baisan wanene sheikh imam ba, kuma mun yarda da maluntarka sa, bai kamata mu musa ma maganar shi ba, bayan haka owais jinin mune bazai ta6a kawo abun da zai cutar da ahlinsa ba, idan ma saboda kuna fargaban kada su cutar da ku ne to ku sha kuruminku owais shi ya ke da alhakin da duk wani abu da zai faru" cike da warin gwiwa Mai girma sharafuddeen yayi maganar babu wasa akan fuskar shi, tuni wasu sun fara shan jinin jikin su. Matsawa Chief owais yayi kusa da baba obie wanda tun azu bai tanka ba, ru o hannunsa yayi acikin nashi, a hankali Ya ago suka ha a ido da juna In a calm voice ya furta"banji kace komai ba baba, umarninka kadai nake jira, In har ka nuna bakason su zauna zan koma da su, Idan kuma ka amince babu wanda ya isa yasa subar wajen nan, sai dai mutun ya tafi" ran shi yakai ma ura awurin 6aci Lumshe idanu baba obie ya yi yana nazari, na an lokaci yana yanke shawara da zuciyarsa kowa ya agara yaji ta bakinsa domin kuwa shi ka ai ne zai zartar da hukunci kuma dole ayi biyayya...... Komai dake faruwa akan idanun zahra, tsoro duk ya cika ta ganin rikicin dake shirin 6allewa, tun azu ta 6oye kan ta a bayan su hindu dake a tsaitsaye, jikin ta sai kerma ya ke yi saboda batason tashin hankali arayuwarta... Pravin Allah Allah ya ke baba obie yaki amincewa da zaman su a hall din ji yake tamkar ya shiga zuciyarshi don ya samu damar tunzura shi akan kada ya bar su, jikin shi sai tsuma ya ke yi. Chief owais dake kallon shi amsar shi kawai yake jira, cike da fargaban kada Ya kunyata shi a bainar jama'a duk da yasan abune mai wuya baba obie yayi mashi hakan saboda baya son 6acin ransa. Gyaran murya yayi hankali gaba aya ya dawo kan shi, kafin ya soma magana yana duban kowan nan su "Bana son abun da zai cutar da ahlina, sannan bana son duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a zuri'a na...." tunkafin ya kare maganar, munafuki pravin ya soma sakin shu'umin murmushin farin ciki don yasan karshen zancen zai ce ne a kore su. "Bawai don bana son yaran bane, a na kowa ne, sai don ina son mu are dinner din nan lafiya, zaman su acikin mu, ba lallai ya zama alkhairi ba, tun da wasu sun nuna basu bu atar ganin su,......" da tsantsar mamaki chief owais ya ke kallon fuskar baba obie, hajiya saratu da su laura har sun fara sakin fuskokin su sai kace akan su za su zauna.... Chief bai tsaya jin karashen zancen ba, saboda zuciyarshi ta karaya, a raunace Ya sakin hannun baba obie, ya juya ya kalli prime minister wanda tuni ruwan hawaye sun kwanta luff a idanunsa... Cikin sanyin murya ya furta"am sorry uncle, banyi tsammanin abun zai kai haka ba, dana san ba za a kar6e su ba da banyi gigin zuwa da su dinner din nan ba, dama nayine saboda farin cikin ka" ya fa a yayin da yake mayar da idanunsa kan baba obie "zan tafi tare da su....' yana arasa maganar cikin takun sauri Ya nufi su unaisah, wani irin murmushi ne ya bayyana akan fuskar pravin da su hajiya saratu. "Owais"!! Har Ya kusa kaiwa bakin kofar muryar Baba obie ta katse shi, Cak ya tsaya da tafiya, dama da biyu yayi hakan don yasan baba obie bazai iya jurar 6acin ranshi ba. "Meyasa ba zaka tsaya kaji karashen maganata ba"? A hankali Ya juyo yana duban fuskarshi, Nan take murnar pravin ta koma ciki. Matsawo yayi kusa da shi, fuskarshi dauke da murmushi yace"kamar yarda kayi saboda farin cikin Uncle dinka, Ni kuma saboda farin cikin ka, na amince su shigo ayi shagalin dinner din nan tare dasu, sannan bana so na sake jin wani ya fadi abun da zai 6ata ransu, Umarni ne wannan!! Yana arasa maganar shi, Chief owais ya nufeshi, gaba aya yayi huggin dinshi. rai a6ace hajiya saratu ta nufi hanyar fita daga hall din. "Karki kuskura ki fita! Dawo ki zauna" muryar Sir mubarak Ce ta katse ta, tana faman ha e rai ta dawo ta tsaya hannunta dafe da ugu. o hannun hajjaty pravin yayi, yana faman fitar da huci Yace mata ta biyo shi subar hall din, sam ya manta da hajiya saratu dake kallon shi, ga alama ya fita hayyacinsa, jikinshi duk yayi zufa sai kace babu a.c a hall din Muryar hajjaty da tsantsar tashin hankali ta furta"pravin meke damun ka ne? Agaban mutane kake ru e hannu na? ina zaka kaini ne? bayan ba agama dinner din ba, dan Allah ka kyale ni" ta fada tana kokarin cire hannunta daga mugun ru on da yayi mata. Da karfi hajiya saratu ta furta sunansa"pravin!!" ko kallo bata ishe shi ba, ari kawai ya ke yi yaja hajjaty don su bar hall din, ita kuma ta dage akan bazata bi shi ba, gaba daya hankulan mutane ya dawo kan su. "Nashiga uku pravin, dan Allah ka kyaleni, nace maka bazan bika ba....." gigitacciyar tsawa hajiya saratu ta daka mashi da kakkausar murya mai ha e da zafin kishi ta furta"ka fara haukane? Agabana kake ru e hannun ta? Anya kuwa kana acikin hayyacin ka" agowa ya yi da idanunsa wa anda suka ka a jawur ya dubi hajiya saratu da masifa ya furta"Bai shafe ki ba!" har sai da taji gabanta ya fadi, Su hajiya laura sun saki baki
Chapter 28 · 0% Book details