← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 93 OF 247

Sashe 93

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

kada ya manta da junaid karfe shida Yaje ya daukosa" amsa mata aneelerh tayi da toh Bayan ta katse kiran, fuska A yamutse ta kalli ummi dake tambayar ta lafiya meya faru taji ta ambaci sunan benzair Girgiza kai tayi kafin ta kwashe komai ta sanar da ita, hankalin ummi ba karamun tashi yayi ba. "Yanzu zanje asibitin, ki zauna ke inyaso gobe sai kije kada abar gidan ba kowa, duk da Ana tana nan ba lallai junaid Ya yarda da ita ba kinsan shi da rigima." Amsa mata ummi tayi da toh, cike da Alhinin abun da Ya faru, da sassarfa mami ta dauko hijabi ta zubla ta fito daga daki, ummi tayi mata adawo lafiy sanna tace agaishe mata da mai jiki, kafin taje goben Mami na fitowa daga gidan saiga motar abie ta shigo, hakan ba karamin dadi yayi mata ba, dama abun hawa zata tsayar akaita can, sai gashi Allah ya dawo da shi, Agabanta Yayi parking motar bata jira Ya fito ba, ta bude motar ta shige sai da ta zauna yake tambayarta ina zataje yaga kamar bata acikin nutsuwarta, nan ta sanar da shi abun da ya faru na rashin lafiyar benazir, har fa a sai da yayi akan fada matan da aneelerh tayi mami tace bafa laifin ta bane, itace ta matsa mata, kuskure daine an riga anyi sai dai ayi fatan Allah Ya tashi kafadunta.... Karya kwana yayi da gudu motarsu ta fuce daga gidan kai tsaye suka nufi asibitin. _________________________________ Slowly motar dr shureim ta kunna kai cikin gidan, bayan yai parking ya dago ya kalli zeenatu da ta kifa kai bisa gwiwa tana ta shesshekar kuka "Bazan gaji da lallashinki ba, dan Allah ki hakuri ki jure ya shurem bayason ganin hawayen babynsa, na fada maki addu'armu take bukata, kuka ba abunda zaiyi mata...." tun da yafara maganar bata dago dakai ba Fitowa yai daga motar ya zagaya dayan bangaren da take ya bu e mata"fito mu shiga" still bata tanka mashi ba, dama dakyar ya rabata da asibitin. Ba karamar badakala suka sha da ita ba. Kuka tadinga yi akan bazata koma gidan ba, dakyar suka lalla6ata. Ganin zata bata lokaci Yasa shi kai hannayensa ya tuttu6eta kamar yar tsana Yai mata irin daukar da ake ma jariri Ya nufi cikin gidan da ita. Tana kuka tana fadin yaya shureim bazanje ba ni ka sauke ni, wurin aunty benazir zan koma...bai saurareta ba har ya karasa katafaren falon, Alhaji musa na azaune kan sofa ya daura kafa aya bisa aya, idanunsa na akan laptop dinsa, hada mug din coffee a gefe yana sha babu alamun damuwa akan fuskarsa hankalinsa kwance Shigowarsu ne Yasa shi dago da ido Ya kallesu Fuskar shureim a daure Ya dira zeenatu, ransa Ya baci da ganin uncle din nasa kamar baisan halin da suke aciki ba. "Shureim..." har ya kusa Fita ya dakatar da shi waiwayowa yayi babu walwala Ya ke kallonsa, shi kanshi alhaji musan Ya fahimci fushi Yake da shi "Ya jikin benazir din? Kamar bazai tanka masa ba ya furta"da sauki" "Menene sakamakon abunda ke damunta"? Sai da ya anyi jim kafin yace"It's depression and panic attack...." bai kare maganar ba yai hanzarin fucewa daga falon don baya jin zai iya jurar kallon uncle musa tsaf zai Iya gaya masa magana Har ya kusa fita daga entry hall din kwatsam sautin muryar zeenatu Ya dakatar da shi Ya kasa kunne Yana sauraronta Cikin muryar kuka take fadin"Wallahi daddy baka da tausayi, kowa ya damu da halin da aunty benazir take aciki ban da kai! Jiya kana gani haka ta kwana akulle kaki taimakawa ka bu e mata kofa, har sai da ta kwana, why daddy? Baka sonta ne? Ko tayi maka wani laifi ne da yaja har kake nuna halin ko'in kula akan ta, ni wlh ka 6ata min rai daddy tun da har baka damu da rashin lafiyar aunty benazir ba, hankalinka kwance kana agida sai kace ba iyar yayanka ba,....." kamar daga sama dr shureim yaji saukar mari ji kake tasss A matu ar furgice ya ware dara daran idanunsa, jikinsa na 6ari a sukwane Ya juya cikin takun sauri Ya nufi falon Har zai shiga wata zuciyar ta gargadesa akan kada Yaje Tsayawa yayi yana sauraron su daga inda yake yana iya hangen zeenatu wadda tunda daddynta ya kwasa mata mari gaba daya ta jirkice ta kife kan hannun sofa, jikinta yadinga bari kusan wannan ne karo na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ta....baiwar Allah gaba aya ta furgice ta kasa dagowa ta dinga tsala kuka tana fadin na tsane ka daddy, da kanka ka sa hannu ka buge ni? Daddy ka makance ne? Wlh sai dai ka kashe ni daddy..." masifa ta dinga zazzaga mashi Zeenatu bata ta6a bashi mamaki ba irin na yau, duk irin shakkarshi da take ji hakan bai hanata fadan ta cikin ta ba, hakan ya tabbatar masa da taji haushin abunda yayi Yatsun Hannunsa Ya zubawa idanu cike da jin haushin marin ta da yayi, Duk da ita taja ma kanta, shi fa ba'ay masa fada ana aga masa murya balle ita da take yar cikinsa... Walking slowly Ya nufi sofa din da take Ya zube kan gwiwowinsa agabanta. dr shureim dake la6e Yana kallon shi har saida Ya an ware idanunsa cike da mamakin Yadda Alhaji musa Yai kneel down agaban zeentu mutumin da ko uwarsa baya tunanin Ya ta6a zukunna mata, wannan wani irin sone ya ke yi mata? Kamar zai mata sujjada haka Ya fara magana"i'm really sorry my daughter, kurkurene ba da son raina ba, kece kika fusata ni zeenatu, banso na mareki ba..." yadda yake yi mata magiya ba karamin aure kan dr shureim yayi ba, har tafin hannu yasa ya shafa fuskarsa don Ya tabbatar in ba mafarki Yake Yi ba Cikin shesshekar kuka take fadin"Dad ..dy dama ka daina bani hakuri, don bayi zanyi ba, ni bana son ganin ka, tun da bakason Aunty benazir dina..." bata kare maganar ba, Yai hanzarin furta"waya fada maki bana sonta? benazir kamar a take awurina..." To amma meyasa jiya kaki bude mata kofa "Saboda bani na kulleta ba, itace ta kulle kanta .." "Daddy ni ban yarda kana sonta ba, tun da kaki zuwa asibiti dubata..." Hannu yakai tare da janyo zeenatu ya kwantar da kanta saman broad chest dinsa Ya daura tafin hannunsa abayanta yana lallashinta..."ki daina kuka bana so, indai akan benazir ne zanje na dubata hope hakan yayi maki" Tana faman matse kwalla tace"daddy dr yace in har ba'a bemo mata yarta ba, zuciyarta zata buga ta mutu, dan Allah kasa a nemo mata yar babynta, daddy nasan zaka iya..." yamutsa fuskarsa yai kafin yace"naji zanyi kokarin sanyawa a nemo mata ita, Yanzu ki kwantar da hankalinki, Muje daki ki kwanta ki huta, zan sa tani ta kawo maki abinci nasan kina jin yunwa..." yai maganar tare da mikewa ya ru o hannun zeenatu acikin nashi, suka nufi bedroom dinsa gauran numfashi dr shureim Ya sauke aranshi yana mai al'ajabin irin son da Alhaji musa yake ma zeenatu Sai dai baiji dadin marin da yayi mata ba, yaji zafi aranshi, saboda yaga shatun yatsunsa sun fito ru u ru u kan kuncinta yasan dakyar in zazza6i bai kamata ba, saboda zafin hannu gare shi, ya ta6a marin zainab mai aikin gidansu lokacin dayaje joss kawai saboda ta ha a hanya da shi har ta bangaje shi cikin rashin sani, tun da ya kwasa mata mari sai da tay 1 week tana jinyar fuskarta.... sai dai yasan ba lallai ya bari zeenatu taji jiki ba, tunda yana sonta zai mata maganin abunne Da wannan tunanin Ya fuce daga gidan Ya shiga mota Yaja Ya nufi asibiti. ______________________EX-PRISONERS A tsaye suke su biyu suna fuskantar junansu, tunda batool ta sanar da ita game da wayar da tajiyo aunty ummin su, tana yi a tsakar dare cikin toilet, taji hankalinta Ya tashi zuciyarta harta fara raya mata ko dai aunty umminsu da wata muguwar manufar take atare da su? "Taya za'ay insan dawa take magana"? Ta jefa wa kanta tambayar "Wai hada cewa ay bani da wayon da zan iya sanya mata ido..." acewar batool "Anya batool ba zaki daina kwana dakin ta ba? "Saboda me"? "Indai zaki cigaba dayi mata la6e duk ranar da ta gano ki, wlh zata Iya hukunta ki, tun da bamusan me take ullawa ba! Girgiza kai batool tayi"ni dai bana Yi mata mummunan zato, kuma bana so na daina kwana dakinta..." fuskarta ayamutse tayi maganar "Nima ina kyautata mata zato, amma meyasa take abu kamar mara gaskiya? Waya a toilet kuma a tsakar dare? Sannan har tana fadin baki da wayon da zaki iya sanya mata ido? Ruko hannun batool tayi"bazan hanaki kwana dakinta ba, amma kiyi takatsantsan, kada ki ara yi mata la6e kibarta kawai, In sha Allah ba abun da zai faru watakil ma bata son ki farka daga bacci ne shiyasa ta shiga toilet tanayin wayar don kada ta takura maki' jinjina kai batool tayi alamar gamsuwa da maganar unaisah Kafin wani ya ara yin magana a cikin su, suka ji an turo door room din, kusan atare suka dago suna kallon mai shigowa har saida gabansu Ya an fadi ganin matar da suke gulmarta Tayi gayu abunda cikin riga da wando sun kama jikinta, head din data daura ba karamin kyau yayi mata ba, tuni kamshin turarenta Ya bu e hancinansu Ganin yadda suka tsareta da ido ne Yasa tace"lafiya naganku atsaye? Ko dai gulma ta kukeyi ne"? Har suna hada baki wurin fadin"A'a" kashe masu ido tay tare da sakin murmushi tace"ku fadamin gaskiya ba abunda zanyi maku, meyasa da kuka ga nashigo kukayi shiru? Bayan kafin na shigo naji kuna magana cikin ra "Wlh ba gulmarki mukeyi ba..." ta6e baki tayi"shikenan tun da kunki fadamin gaskiya, Ku zo mu tafi dining, it's lunchtime. Yan uwanku suna jira..." Amsa mata sukayi da toh, a tare da ita suka fito daga dakin...tunkafin su Isa suka hango su Haris zazzaune kan dining chairs an cika masu table da lafiyyayan abinci Wuri suka samu kowa Ya zauna har sun fara cin abinci unaisah ta tuna da danish, har ta fara gajiya da halin shi, sam bayason zuwa dining cin
Chapter 93 · 0% Book details