← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 182 OF 247

Sashe 182

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

tayi"A'a amma dagaske baki ta6a yin aure ba"? aga mata gira ummi tay, waro idanu waje Danejo tayi da mamaki tace"tab lallai, aradun Allah da a rigarmu kike da tuni Kin aje tatta6a kunne, Ko kina so ko bakisho dole ay maki aure" tuntsirewa sukayi da dariya gaba dayansu, hausarta ba karamin nishadi ta basu ba, kana jin maganarta zaka gane bafullatanar daji ce. Sai dadi takeji ganin yadda ta sanya su nishadi Maimakon ta dauko masu abunsha, sai ta kama basu labarin ha uwar ta da Taj, har zuwanta birni da irin wautar da tadinga yi mashi, sunci dariya kamar zasuyi kuka. Ta za e sai zuba takeyi masu kamar aku, Har saida Parveen ta gaji da zuba na mazurai taji shiru bata kawo masu abinci ba, gashi ko breakfast basuyi ba suka taho Hannunta dafe da cikinta tace"Aunty Danejo, mufa Yunwa muke ji, bamu ci komai ba muka taho" dan zaro ido ummi tayi tana kallonta, sarai parveen taga kallon da ummi tayi mata amma saita kawar da idonta gefe. Mikewa Danejo tayi"i'm really sorry, na cika ku da surutu, kunsan mutumin dake zama cikin kadaici in ya samu abokin fira komai ma mantawa yakeyi, kuma fa tun dazu Nayi maku girki tunda daddyn angel ya sanar dani zuwanku..." har ta fara tafiya ta juyo tare da kallon su"wa zai bini kitchen din mu dauko kayan abincin"? Da sauri Parveen da Yasmeen suka mike atare suka nufi kitchen. Ajiyar zuciya sajeed Ya sauke tare da kallon aunty umminsu yace"da farko dana ganta kyakkyawa nayi zaton miskila ce ashe ta iya dan banzan surutu" dariya ummi tayi tana fadin"Pls kadaina maganar nan kada taji ka, amma fa kamar ka shiga zuciyata, Nima nayi zaton hakan" Jemimah tace"gulma haramun, Allah In tadawo saina fada mata abunda kuka ce" Harara sajeed Ya galla mata"dako Kin ci na jaki Allah, Yar sa ido kawai" gatsina mashi hanci tayi tare da hararar shi, Ya janyo throw pillow Ya an buga mata akanta. Azeeza tace"Aunty Ummi, wai itace maman angel ne? Wadda Ta gudu tabarta acikin kwamin wanka" waro idanu waje sukayi Batool tace"ke fa baki gane komai, Kin manta bafullatar dajin da Angel ta bamu labarinta? Wadda ta tsinceta acikin ruwa.." ta fa a tana kokarin fahimtar da ita can tace"Yanzu na gane ta" ummi dake kallonsu a hankali ta sauke idanunta kan Deeja, data daura kanta saman kafadar Haris, hannunsu ruke cikin na juna tun zuwansu basuyi magana ba, aranta ta ayyana"Mun baro romeo da juliet agida, ga kuma layla da majnoon" Fitowar su Danejo daga kitchen ne Ya katse firarsu, kowan nan su ruke da farantai shake da kayan abinci , akan rug suka ajiyesu, kowannansu ya sauko kan rug din suka kewaye farantan,tun da kamshin abincin ya daki hancinsu suka fara hadiyar yawu Har sun fara Cin abincin, Batool tace"ba zamu jira Unaisah ba"? Ummi tace"nima dai naji shiru bata karaso ba"danejo tace"kada ku damu, itama na ajiye mata abincin ta, duk lokacin data karaso sai taci" daga haka ba su kara magana ba, Kowa ya maida hankali kan abincin da yake ci da alama yayi masu dadi, su parveen ba baka sai kunne, Hannu baka hannu kurya, kwata kwata bata Iya bakunta ba. Ummi har alama tayi mata da ido donta daina loma amma ta wani basar kamar bata ganta ba Danejo ko sai fadi take kuci ku koshi in ma bai isheku ba, akwai saura abincin dana aje mana.. _________________________________ Around arfe 2 na rana da matsakaicin gudu motocin su suka kunno kai Cikin Villa din.. Su biyune zaune a back seat din Motar Chief, babu mai magana a cikin su, sunyi shiru daga gani ba karamar gajiya suka kwaso ba .. Gently yake daddana wayar hannun sa, yana kokarin kiran daddy dinsa sai ga kiran shi ya shigo, yayi mamaki kamar yasan shi yake shirin kira.. Picking call in yayi tare da kara wayar a kunnansa yana niyar yi mashi sallama miryar Mai girma sharafudden Ta katse masa hanzarinsa"Owais Inason ganinka Yanzun nan..." har saida gabansa yadan fadi da jin yanayin muryar daddyn nasa. "Am...daddy, Ina fata lafiya" bai kare maganar ba Yace"idan kazo zaka ji koma menene" daga haka Ya katse Kiran Lamarin Ya daure mashi kai! Bai ta6a jin muryar daddynsa cikin fushi irin Na yau ba, fatan shi Allah Yasa ba wani abun bane ya taso. A hankali Ya dubi Danish dake a hakimce kan seat, Ya langwa6e kan shi, Idanun shi suna a lumshe kamar ma bacci ne yayi awon gaba da shi. "My Boy, Bacci kake Yi"? Cikin kunnanshi ya tsinkayi muryar chief a wahalce ya bu e rinannun idanun shi batare daya iya furta kalma ba. Adaidai Lokacin Motocin suka yi parking, agent Ya bu e masu cardoors in. . Atare suka fito, adai dai lokacin Taj da big guy sun fito daga motarsu.. Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish.. "Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su "Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..." yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay" "Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su.. "Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su. "Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi.. Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.." kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..." an zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar an aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi." Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku" ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi" murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face an uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba. tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa. A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa. Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa. "Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking inta already.." dafe kai yayi da hannu aya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah.. "Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota" "Okay, sai naji daga gare ka" Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka. Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown in jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse. Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ankance... Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba A fa ace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki" Make mashi kafa a tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba, anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba" aure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka yaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..." Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba ka an ba. ________________________________ Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist insa aure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom in nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki.. Yatsun kafafunta Ya hango ta asan labulen daya age sai kerma suke ...farat aya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa
Chapter 182 · 0% Book details