Sashe 241
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
shi ta hanyar aga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba. Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji. "ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..." bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya dam i kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..." "Haba yaya Sharafudeen pls Owais.." Hajiya saratu da ta auko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba. Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!" fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, an sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da a suna fa a atsakanin su.." fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace. Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba. "Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba.. Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa.. Lokaci aya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi. bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa. wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin "zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...." girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa. "Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa. Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma. Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. "Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..." His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa. "Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"? Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba, "Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....." Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..." dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar aga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...." juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi. Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne. Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi. Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais.. Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa.. "Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"? Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya. "ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar. Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba. A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba.. Hannayen shi dake kerma ya aga sama cikin karyayyar murya ya ce _"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...." bai kaiga arasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data kara e kunnuwan su *_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_ ~*_________________________________*~ *Daga Al alamin Boss Bature *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 8:15 PM] Amina Musa Mustapha _ * *_ ~___________________________________ A matu ar ru e suka juya tare da kallon mai shigowa... Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, da yar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma. Cike da tsantsar ru ani suke kallon ta daga asa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ahon zuciya. A sukwane Sharafudeen Ya mi e yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba. Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani.. Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta i aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ru ani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo... "Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba aya sun agara da su ji dame ta zo musu. "Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate in?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke. Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah.. Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka mi e daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo... "Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq... "Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya fa a yana zare idanun sa.. "Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..." Senate Lateef ne ya auko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin. Tana gab da zata arasa gaban Sofas ta an dakata tana mayar da numfashi. Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka araso tsakiyar Sofas in, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...."