Sashe 208
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
naga shigowar shi shiyasa na gudo daki don in samu damar yi maku video, dan Allah don sonku da manzon Allah saw Aduk lokacin da kuka kalli videon nan kuyi gaggawar kaishi ara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku bata lokaci, saboda shi din mutum ne mai hadarin gaske, ya sha yi min barazana akan In har na kuskura na fada ma wani abun da ya ke min wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na fadamawa shiyasa nakasa sanar daku_ Tuna wannan maganar yasa Aneelerh taji tsoro ya mamaye zuciyarta, tayi shiru tana sauraron gargadin da zuciyarta ke yi mata. _Kada ki kuskura Anila! Ba zaki Iya ja da shi ba, in har yasan kin san sirrin shi kashe ki zaiyi, mutane irinsa basu da imani zasu iya aikata komai donsu rufawa kansu asiri, Kwara ki nemi wata mafitar...." tayi zurfi cikin tunaninta kwatsam Ta tsinkayi muryar mutum abayanta "ANEELERH"! Ras gabanta Ya fadi jin muryar mutumin datazo nema, tuni taji tsigar jikinta na tashi, Yan hanjin cikin ta suka hau kadawa. "Ko ba ita bace"? Zazzare Idanu tayi, Cikin sauri Ta daidaita nutsuwarta, A hankali ta juyo ta fuskance shi, Yana atsaye Cikin riga yar shara da gajeran wando, Junaid Ya jima Yana fada mata Uncle dinta mummuna ne ba ta6a ganin muninsa ba sai yau data gano mugun halinsa. zuba mata jajayen idanun shi yayi, Cikin rawar murya ta furta"am.. um..un uncle barka da rana, dad..dama kai nake nema, um.. inaso ne dama in tuna maka maganar...." cike da rudani yake kallonta Jin yadda take yin magana a dabarbarce kamar mara gaskiya amma bai kawo komai aransa ba yasan Anila da kunya may be tana jin nauyin yi masa magana ne shiyasa ta ru Murmushi yayi tare da cewa"Anila kenan, to meye abun rudewa aciki? Kawai don zakiyi min magana? Waini sai yaushe zaki daina jin kunyata? Sai kace ba Uncle dinki ba"? kakaro murmushin ya e tayi kan fuskarta batare da ta tanka masa ba. Dafe kai yai"kash Kiyi hakuri kinji shiru tun da kika tura min credentials in ki, har yanzu ba'a neme ki ba, kema ce baki tuna min, kinsan uncle din naki da mantuwa abubuwane sunyi yawa akaina bakasai nake tunawa ba, In sha Allah zan tuntubi Md din asibitin mutuminane ai..." washe baki tayi tace"bana so na takura maka ne, nasan uzirurrukane sukai maka yawa, shiyasa bana yi maka magana, yau ma don naji kace kana gida shine nace bari na tuna maka" "Allah sarki, nasa maki rai kina ta faman jirana, ki kara hakuri In sha Allah yanzun nan dana shiga daki zan kira shi awaya in tuna ma shi, Ki ma fara shirye shiryen fara zuwa aiki" ya fada tare da tafa hannayen sa. Washe baki ta kumayi alamar taji dadi tace"nagode uncle, Allah yasa ka da alkhairi Saina Ji daga gare ka, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" "Ameen Anila, ai baki da wata damuwa, ke da kike dani? Asibitin Obie ai namune ke sai ma kin zabi albashin da kike so a yankar maki Allah wallahi" fashewa tayi da dariya tana fadin"kai uncle, Ina kara gdy da kulawarka agare ni" batai gangancin da zai gano ta ba, lokacin da ta baro gurinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tafin hannunta dafe da saitin Zuciyarta. Tana shigowa falo taja tunga ta tsaya tana tunanin meya kamata tayi? dafe kai tay kamar mai fama da ciwon kai. Aranta ta ayyana Ko dai ta sanarma Mami? Can kuma ta girgiza kai ba lallai su yarda ba, ko da ta nuna masu video din tun da bayani ne Ana tayi bawai videon abun da ya ke yi mata ne ba, Bakowane zai gasgata maganarta ba kai koda zasu yarda hadari ne Ta gaya ma wani acikin gidan hankalinsu zai tashi a karshe ma garin nukunuku Ya gano su. Gaba daya Aneelerh ta ru e, kwakwalwata na neman rikicewa.. Juyawar da za ta yi ke da wuya tayi arba da mami dake ta kallon ta. Washe baki tayi adabarbarce ta furta"ma.. mi dama yanzu nake niyar shigowa kitchen din don in tayaku aiki"! Wani kallo mami ta yi mata. "Aneelerh lafiyarki kuwa? Tun dazu Ina tsaye abayanki baki lura dani ba har kiran sunanki nayi kusan sau uku baki amsa min ba, meke damunki ne!" yawu ta ha iya ut jikinta na tsuma tace"mami ki yarda dani babu komai, ba abunda ke damuna" "Anya Anila? Ko dai baki da lafiya? Ta fada tana karewa fuskarta. girgiza kai tay"lafiyana lou mami" Ba don ta yarda da maganarta ba tace"toh," har zata juya ta dan dakata"Kunyi waya da mahboob ne"? "A'a," "Kinsan ba kai gare shi ba, kada yabar mana yaro da yunwa, Ki kira shi ya dawo da junaid gida" amsa wa tay da toh. "Naji kince zaki ta ya mu girki, mun kammala ay, ga gidan nan ki kara gyara shi" ta amsa mata da toh. Mami na barin gurin ta sauke ajiyar zuciya. ________________________________________ *PRAVIN* Cike da zumudin son ganin ta, ya shigo dakin tashin farko yai arba da awarwaron ta akan floor inda ta watsar da su, Hankalinsa ba aramin ta shi yai ba, a yadda yasan Hajjaty da tsafta ba karamin abu zaisa tabar dakinta a yamutse ba gyara ba, hakan yasa shi fahimtar babu lafiya. Sam bai lura da ita ba, har saida ya karasa tsakiyar dakin, Idanunsa suka sauka akanta tana a kwance kan gadonta bayan data gama koke koken bacci ne yai awon gaba da ita, from head to toe yabi ta da kallo kamar mahaukaciya, na in sarin jikinta duk ya warware, har inners din ta sun fito, ga gashin kanta a hargitse kamar bata gyara shi ba, aransa ya ayyana meya faru da ita? Meke damunta"? damuwace karara akan fuskarta, hawa yai kan gadon ya matsa kusa da ita, da ya dubi fuskarta sai da yaji gabansa ya fadi, Gaba daya kwalliyar da tayi ma fuskarta ta baci da jan bakin data shafa ma lips dinta. Lumshe idanun shi yayi tare da sake bu e su kan fuskarta A hankali ya Shafa fuskar da yatsun sa har izuwa kan wuyanta ya dire su kan kirjin ta. Numfashi ta an ja tare da sauke shi da hucin zafi. Baya so ya katse mata baccin ta, amma yana son yaji meke damun ta. Can kasan makoshi ya furta"My lovely wife, am back, nayi kewarki sosai" ya fa a tare da manna mata sumbata kan lips dinta. ya saba duk in ya dawo daga aiki ko ya dawo daga tafiya ya shigo dakinta zai taras da ita tayi gayu ta gyara ko'ina na dakin don ta faranta masa kuma zata watso da gudu ta rungume shi sannan ta yi kissing din shi amma yau sai yaga akasin hakan taya ba zai damu ba? Hannunshi ya zura ta bayanta yana kokarin kwance igiyoyin rigarta bai aune ba yaji ta dam i hannunsa, da sauri ya kalle ta, A hankali ta bu e idanunta wadanda suka kada jawur ta sauke su a cikin nashi, gaban sa ne ya ara fa uwa ganin yadda idanunta suka yi ja kamar an watsa barkono acikin su. Arude ya furta"kin tada min hankalina, meke damunki ne? Gaba daya dakin a hargitse babu gyara, ke kanki ba acikin nutsuwarki kike ba, wai meke faruwa ne"? Maganganun marwa ne suka soma dawo mata a cikin zuciyarta, Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, hakan ba karamin daga hankalinsa yai ba, duk yabi ya rude cikin rawar murya yake yi mata magiya akan ta fada masa damuwarta.. Lumshe idanunta ta danyi kafin ta kuma bude su akan fuskarta. Zuciyarta naci gaba da tariyo mata abun da marwa ta fa a mata akansa. Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Pravin ta katse ta ransa adan bace ya furta"wai ba zaki fada min abun da ke damunki ba ne? Kina ji ina magana kin share ni"! Numfashi taja tare da sauke shi da karfi. Ta yi saurin daidaita nutsuwarta cikin disasshiyar murya tace"s annu da dawowa. "Ba wannan na tambayeki ba, ki fada min meke damunki" "Kada ka damu, babu komai" "Karya kike yi, Dole akwai abunda ke damunki" "Hakane, bana so na tada maka hankali ne, wlh Cikina ke ciwo, kasan halin da nake shiga idan na fara ciwon ciki" girgiza kai yai"ban yarda ba, kawai ki fada min abunda ke damunki"? Ya fada fuskarsa a daure. Tunani ta soma yi ya zatay da shi? Don bata jin zata iya fada masa abunda marawa tace akan shi, tasan bazaiji dadi ba in yaji anyi masa kazafi kwara ta bar abun acikin zuciyar ta. Kurama juna idanu sukayi har na tsawon mintuna goma, sai da ransa ya gama baci jin tayi shiru taki tanka masa, yana huci yace"yau ni kike boye ma abunda ke damunki? kina da wanda yafi ni ne? Okay, kada Allah yasa ki fada" Saukowa yai daga kan gadon Har ya kusa fucewa daga dakin tayi saurin mikewa ta duro daga kan gadon ta nufe shi da gudu ta fa a bayanshi tare da zagayo hannayenta kan kirjin shi Dakatawa yai da yin tafiyar da kakkausar murya ya furta"kin shirya fadamin"? "eh" batare daya juyaba yai shiru yana sauraronta. "Hajiya saratu ce ta bata min rai, taci mutuncina pravin, ni bansan wata irin tsana tayi min ba..." karya ta shiga shirga mashi abun da ba halin ta ba, duk don ta samu ta kawar masa da tunanin abunda ke damun ta. Ransa ya baci da jin abunda hajiya saratu tayi mata. Cikin shesshekar kuka ta kara da cewa"ita ce ma ta cabemin kwalliyar da nayi maka" ta fada tare da ruko sareen dai dai Inda hajiya saratu ta goge mata kwalliyar da shi ta nuna mashi da yar shagawaba tace"ka gani ko"? Runtse idanun yai ji yake kamar yaje ya shake wuyan hajiya saratu. Yana huci yace "bazan yale ta ba, dole In rama maki cin zalun da takeyi maki, mara mutunci kawai.." still da shagwa6a ta tallabo fuskarsa da tafukanta"babe, Ni ban fada maka don ka rama min ba, wlh na yafe mata, kawai banji dadi bane, amma komai ya wuce, mu kyale ta kawai" Jinjina mata kai yai tace"ina fata kun dawo lafiya? Ya baba Obie? Ya kuka