Sashe 207
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma ya iya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.." "Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki" "Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa" "Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace. Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba" Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne" gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa.. "Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi.. Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye" Shiru ya anyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina" da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba. "Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa" Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi. Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa" "Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince" fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai "Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you" "Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba," "Ina fata kaji alfarmar da an naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan. Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi.. Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi. "Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice. kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..." waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"? Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka" harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya sha e wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa. Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"! Hankalin Sharafudeen ba karamin tashi yayi ba, He couldn't believe that wai owais ne ke yi masa magana kamar zai doke sa? Babu tausasa harshe? Anya bai fara shaye shaye ba? Ko dai har yanzu wayar maganin bancin daya bashi ce ke aiki ajikin shi *DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ~<><><><><><><><><><><><><><><><> ~______________________________________~ Cikin sanyin murya ya furta"Owais, bayan dana hana ka zuwa kai farmakin sai da kaje ko? Ka daina jin magana ta Owais! " ya fa a idanunsa akan ciwon goshinsa daya an le o batare da saninsa ba. "Lafiyata bata shafeka ba! Kuma Daga Rana Irin ta yau babu ni babu kai! Ni ba dan ka bane, kakane shine mahaifina mutumin kirki ba irinka ba, Kuma na rantse ka jira ka gani..." yana arasa maganar Ya jefar da hannun sa daya ru e, Ya juya azafafe Yabar Part din Ko sallama bai je yayi ma baba Obie ba. Ya tafi Yabar Sharafudeen cikin rudani, bai taba zaton owais zaiyi masa haka ba, Kai ko a mafarki, Ji yayi bazai Iya jurewa ba, Cikin sauri Yabi bayanshi Yana fitowa Ya hango Motar Owais dake fita, da sauri ya nufi Security Details dinsa tunkafin ya karaso suka bude mashi cardoor din motarsa Ya shiga ciki, ya basu Umarnin su kai shi Gidan owais. Chief yana zaune seat din baya na motar, ya rufe gefen fuskarsa da hanky, Idanunsa sun ka a jawur, bai ta6a karaya da rayuwar duniya ba irin wannan karan yayi fatan ace ba'a halitto shi acikin ta ba, wai mahaifinsa matsafi ne! fasiki mai shan jini da cin naman mutun, Ya Ilahi! "Sir, motocin mahaifinka suna abiye da bayan mu" SA din dake driving dinsa ne yayi maganar, aransa ya furta wato mutumin nan saida ya biyo ni! Motarsu na shiga main gate na villa dinsa Ya ba Security officers Umarnin karsu kuskura su bar kowa ya shigo gidan. Bayan ya fito daga Motar, Cikin sauri Ya Part dinsa Yana kokarin Haura wa kan stairs Unexpectedly muryar Shi ta katse hanzarinsa"Owais? Lalacewar taka har takaiga ni kake bada Umarnin a hana shugowa gidan ka"? Dafe kanshi yayi da hannu aya wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin shi Ya tsani jin koda muryarsa. a cikin kunnansa yake jiyo takun tafiyar shi bai motsa ba har ya karaso ya zagayo ta gaban shi suka fuskanci juna. Gabansa ya dan fadi ganin hawaye na sintiri kan kuncin mahaifinsa. Cikin raunanniyar murya yace"owais, Dan Allah ka fadamin Laifin me namaka? Wlh Hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har baka fadamin ba..." Zuciyarshi taso ta karaya, amma In ya tuna wanene Mahaifinsa nasa sai yaji kamar ana kara rura wutar iyayyarsa a zuciyarshi. Bai ko kula shi ba, Ya nemi ra6awa ta gefen shi zai wuce, cikin sauri Sharafudeen Ya dam i Arm dinsa. Cikin karyayyar murya yace"Owais, in har ba so kake zuciyata ta buga in mutu ba, ka fadamin laifin me nayi maka da yaja har kake zargina! wai ni owais, mahaifinka"! Kallo mai cike da tsana Chief Ya watsa mashi kafin yace"kafi kowa sanin laifin da ka aikata min, zaifi ka fita sabgata, don bazan taba fahimtarka ba, kawai ka jira lokacin da zan fallasa asirinka a bainar jama'a.." ya fa a tare da bangaje hannun sharafudeen Ya kara gaba Ya shige part dinsa Yayi locking room door dinsa rai a6ace. A bangaren Mai girma sharafudeen Kasa motsawa yayi, al'ajabi da bakin Cikin maganganun da Owais ya gaggaya masa sun ru e zuciyarshi tamau sun hana kafafunsa motsawa, Ya rasa ya zaiyi bai ta6a sanin Owais yana da kafiya da taurin kai ba Sai yau da Allah ya nuna masa, tunani ya soma yi waya kamata Ya kira ya fada masa halin da yake a ciki!. Tsadaddar Wayarsa Ya zaro Ya daga aljihu ya shiga call logs Ya danna ma Number din da yayi saving da jini aya kira, Tana fara ringin yayi picking.. A mutunce suka gaisa da junansu kafin Yace"pls ko zaka kira Owais, kuyi magana, akwai wani abu da ke damunsa ya i fadamin may be kai ya sanar dakai" tun daga yanayin muryarsa prime minister Hateem Ya fahimci dan uwan nasa yana acikin damuwa. Othe other hand prime minister yace"Okay, Don't worry, I'll call him Just calm down and take care of yourself for me" "Okay, Nagode kaima ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama ya juya ya tafi zuciyarsa a hautsine.. *ANEELERH* Ta fi karfin rabin awa tana safa da marwa a tsakar dakin ta, tana ta tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin, tun da ta saurari maganganun Ana gabanta keta faduwa, Hankalinta ya i kwanciya, damuwarta Ina Ana? Tana raye ko ya kashe ta? batajin zata Iya hakura taja baki tayi shiru batare da tayi gaggawar daukar mataki ba ko dan ta kwatarwa Ana hakkinta, ta kuma ku6utar da family dinta, zuciyarta ce ta dinga azalzalarta da tunzurata akan taje ta tunkare shi kaitsaye ta fada masa ta san komai sannan tayi masa barazana in har bai fada mata ina take ba zata tona masa a asiri uban kowa yasan me ya ke aikatawa sannan ta kaishi kara gurin hukuma. Kwakkwaran Numfashi taja, fuskarta babu annuri ta fito daga dakin bata iske kowa a falo ba, Mami da ummi suna a kitchen suna aikin lunch. Bata nufi ko'ina ba sai akin Uncle dan Iya, da kwarin gwiwa take tafiya yayin da bugun zuciyarta ke aruwa Ga tsoro tanaji amma ahaka ta dage ta durfafi dakin nasa har takusa kutsa kai Cikin akin taji kamar an ruke kafafunta dakatawa tayi da yin tafiyar, nan take brain dinta ta fara tariyo mata maganar Ana. _watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda yace bazai kyaleni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kunga ni kadaice agidan, yanzun nan