← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 160 OF 247

Sashe 160

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen ewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"? hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su, "Nima fitsarin nake ji, tun azu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su. "Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi aki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya fa a yana duban su. Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta mi e idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi azu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!. an tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harhar e kamar zata kife asa har sai da ta shige dakin tukunna ya auke ido daga kallon ta. Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist inta daure da towel, hannun ta ru e da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi. Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin "Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki bu e min ofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta. "Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne" "Toh" Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya ba a mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana bu ewa Batool tayi sauri fa awa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba. e ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta fa a tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye Jijjiga kafa arta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta. La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish. Hankalinta Ya tashi matu a muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar. "Yanzu Ina su Unaisah din"? "Duk suna adakin su, gaba aya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji" tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta. "Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba. "Aunty Ummi ko sallah banyi ba.." "Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet. _________________________________ *ANEELERH a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ru e da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwa ayi, kadan yake balla ya an dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi Shekaran jiya izuwa yau ya ara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya auke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam iwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba. Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta "Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya fa a yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu" yamutsa fuska yai tare da ma e mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya fa a da shagwa6a yana hade fuska. ura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata. "Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in an maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi "Yaushe zaka koma school"? e mata kafa a yai"shaina ara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki "Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita" ya fa a tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam Takai hannu ta shafa sumar kan shi. "Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari. da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara. "Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...." tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar agara da son jin meya faru da su aranar!. Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi. can dai ta an bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...." bata are maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye" kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci aya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..." girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake fa e maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..." yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya ha ance yana fa a mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi. "Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..." kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta an ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..." bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane. _______________________________ alla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nanna e kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish. aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba. "Unaisah!" ummi ce ta kira
Chapter 160 · 0% Book details