Sashe 61
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
da dubansa ga sauran gawawwakin dake baje asa da sauri yakai hannu ya an ta6a afar Rubina wani iko na Allah nan take Taja Numfashi da arfi ta fesoshi batare da ta bude idanunta ba, sai la66anta dake kerma, aya bayan aya yake farkar da su babu wanda yake a cikin hayyacin sa duk sun jigata sun galabaita, sai sambatu su ke yi suna ambaton ruwa ruwa za su sha, i shi suke ji. Maimakon salsabeel yayi farin cikin farfa owar su, sai ya fashe da kuka yana fa in "wallahi banso suka rayu ba, saboda bani da yadda zanyi da su, mutuwar ita ce hutunsu, ga shi babu yan uwansu sun riga sun tafi...." Cikin tashin hankali ya ru o hannun Danish yaci gaba da fa in"ka taimakamin Mu binne su kawai, su arasa mutuwa acikin abarinsu, ni banga amfanin suci gaba da rayuwa a wannan duniyar ba, wahala zasu sha idan mutanan nan suka riske mu zasu kashe su ne bayan sun gama wula anta rayuwarsu....", kafin Ya are maganar Danish Yace"bazai yiwu ba, kamar yadda yan uwansu suka rayu suma haka zasu rayu, bazan ta6a bari su rasa ransu acikin gidan kurkukun kaddara ba, ko da kuwa zan jefa kaina cikin hatsari ne sai nayi musu hanyar da za su gudu" da warin gwiwa ya furta kalaman tare da fucewa daga dakin tsohuwa yaje asan gadon Batool inda suke ajiye robobin ruwa ya dauko su ya wuce toilets din dakin su ya samo masu ruwan da zasu sha, bayan ya dawo yabi su daya bayan daya ya basu ruwan suka soma sha. Salsabeel dake kallon shi tsabar ululun bakin ciki baisan sa'adda ya fashe da kuka yana fadin "Danish ka tafi kawai, idan har bazaka taimaka min mu binnesu ba, dan Allah ka tafi zaifi min kwaciyar hankali, Ka rigada kasan bamu da wata hanya da zamu iya ceton su...." Cak Ya tsaya da yin maganar ganin babu danish Kamar walkiya Ya 6ace ma ganin shi, Shiru yayi yana faman ha iyar yawu cike da zullumin ina Danish Yaje? Ko dai Ya tafin ne ...? Tuni ido Ya raina fata sai kace ba shi bane yake korarsa akan Ya tafi ba, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, hankali atashe yake kallon su Dija dake zazzaune a asa cikin fitar hayyaci suke ambaton sunan an uwan su musamman sunan Unaisah da na Danish, gaba aya sun zauce, gawar mahaifiyarsa ya kalla tuni wani kukan ya kuma zuwa mashi cikin matsanancin tashin hankali Ya soma walawa Danish Kira don Ya dawo ya taimake shi ko ya samu ya binne su. Jin shiru babu alamun zai dawo ne ya sa shi zubewa kan gwiwowinsa Yana ta faman yin shesshekar kuka kamar ransa zai fita. Kamar daga sama Yaji motsi a akin, A firgice Ya ago da idanunsa azazzare ya kai duban sa ga Bookshelve akin tsohuwa tamira dake Ta motsi, Kafin yai wani yunkuri gaba aya Ya rikito Ya rubza asa, Jikinsa na 6ari Ya mi e yana kallon ofar da ta 6ullo, da matu ar mamaki akan fuskar shi. Ta cikin ofar Danish ya fito, fuskarshi sharkaf da gumi Ya dubi Salsabeel. "Zamu Iya tafiya" wani irin farin Cikine Ya lullu6e Salsabeel. A ru e ya furta"Danish tayaya akai ka gano ofar nan? Ban ta6a sanin akwai ta ba, kuma bana tsammanin ko ita tsohuwa tamira tasan da zaman ta" ya fa a cike da son jin arin bayani. Yana faman huci yace"Kada ka manta, ka riga ni tsintar kanka acikin kurkukun addara ni kuma nafi ka sanin komai na cikin sa, duk wata ofar sirri dake a kurkukun nan nasan da zamanta, tabbas tsohuwa bata san da wannan kofar ba, tsohuwar hanyace da aka jima da toshe ta, ni da kaina na sake ha a ta da sihiri na, Idan muka bi ta cikin ta, zata 6ular da mu cikin wani kogon dutse dake wajen kurkukun nan, dalilin dayasa na za6i ku raba hanya da su Unaisah saboda nasan zasu iya farmakar mu idan har suka gano abunda ke wakana, inaso na raba masu hankali ne watakil in mukayi hakan wasu su rayu daga cikin mu" Bazai iya jure kallon Danish ba, Yaron Ya burge shi, Ya yi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba, ya taimake sa a lokacin da rayuwarsa take akan ga6ar salwanta, da sauri ya janyo shi ya rungume shi yana kuka, kafin ya raba jikin su cikin sanyin murya yace "Amma danish su Angel fa? Yakamata ka koma wurinsu suna bu atar ka, bana so wani abu ya same su" Girgiza kai Danish yayi "kada ka damu, babu abunda zai cutar da su, saboda na rigada na aure hanyar da suka bi da sihiri babu wani mahalukin da ya isa ya iya tsaga kofar ya shiga balle har ya cutar da su, kafin nazo nan sai da na kiyasta awannin da za su yi kafin su arasa kofar da zata 6ular da su waje ni kuma zan riga su komawa bayan na taimake ku" Murmushin farin ciki salsabeel ya saki, Basu tsaya bata lokaci ba suka yi kokarin taimaka ma su Hibba don su mi ar da su tsaye, saidai mutun biyu daga ciki kafafunsu sun kasa aukar su sakamakon abunda tsohuwa Zafreen ta yi ma su, bayin Allah sai ihun azaba suke saki, da sauri Danish Ya sungumi deeja ya goyata a bayan shi, ya sanya mayafin daya auko a asa ya aureta tamau, kafin ya auki Rubina ya aurata a kafa ar shi dama su biyune basu iya tafiya. shi kuma Salsabeel ya yi amfani da bargon tsohuwa tamira ya nanna e gawarta aciki ya aurata a kafadarsa. A haka suka bi hanyar mai duhun gaske ga zafi tamkar ana rura garwashin wuta, sunci ba ar wahala su sarah kamar numfashinsu zai auke. Cikin awanni takwas da su Angel sukayi suna rarrafawa akan hanyar su duk wannan abun Ya faru, baifi awa biyar ba su salsabeel sukayi nasarar fita daga cikin gidan kurkukun addara hakan na nufin sun riga su Angel ku6uta saboda tasu hanyar batai nisan wadda su Angel suka bi ba. Bayan su Salsabeel sun 6ula cikin kogon dutsen, Danish Ya sauke deeja da Rubina daya auko, shima Salsabeel ya sauke gawar tsohuwa tamira, su hibba duk suka zube agajiye har lokacin bakunansu basu gushe da ambaton sunayen an uwansu. Kallon juna sukayi kowan nan su na haki, da sauri salsabeel ya ru o hannun Danish, cikin sanyin murya yace "Danish, bazan ta6a mantawa da halaccin da ka yi min ba, kayi min abunda har abada bazan ta6a mantawa dakai ba, kaine silar ku6uta na daga Gidan kurkukun kaddara kuma kaine silar cikar burina na ganin na cika al awarin mahaifiyata dana aukar mata akan in rufe gawarta kada in bari ta wula an ta, Danish ko a mafarki ban ta6a tunanin akwai ranar da zan bar gidan kurkukun kaddara ba, nasha jaraba guduwa nida mahaifiyata amma mun kasa saboda karfin sihirin mu bai kai ba, sai gashi a sanadiyar ka nayi nasarar fita...." tuni hawaye sun wanke fuskarshi. "Danish, Koda ace ban rayu ba, ni ka gama min komai wallahi, koba komai na sha i iskar duniya bayan tsawon lokaci da na kasance a kulle" ya fa a yana duban cikin idanunsa "ni dai burina ka yi rayuwar farin ciki tare da yan uwanka, ubangiji Allah Ya kare min ku ya tsareku a duk inda zaku kasance, bani da tabbacin zamu sake haduwa wata il ma ba lallai mu rayu ba....." bai arasa maganarba ya fashe da kuka mai cin rai, da sauri Danish ya janyoshi suka rungume juna sosai suka kankame jikinsu. Bubbuga bayanshi Salsabeel yai da hannunshi " an uwana, ka kula min da kanka, wallahi ina mutuwar sonka tun farkon ranar da aka kawo ka gidan kurkukun addara a cikin tsumman ka, naso ka Danish, zan tafi da kewarka, Allah ya rayamin kai Danish, Ina fata wata rana kaima ka zama cikakken musulmi, ka yi rayuwa kamar kowa kayi Aure ka hayayyafa....." Lumshe idanu Danish yayi cikin sanyin murya yace"ina sonka an uwana, nima zanyi kewarka, ka kula min da kanka, ina fata mu sake ha uwa" Yana fa a Ya raba Jikin shi daga na Salsabeel, A hankali ya soma tafiya yana ja da baya yana duban Salsabeel da an uwan shi wa anda kwata kwata basa a hayyacin su, wasu irin zafafen hawaye ne suka cika idanuwan Danish bai daina kallon su ba har saida yayi nisa kafin Ya 6ace ma ganin su. Bai dira a ko'ina ba sai a bakin kogon bishiyar da su Angel zasu 6ula, adai dai lokacin su kuma har sun araso bakin kogon bishiyar suna ta faman ambaton sunan shi. Bayan tafiyar Danish A cikin Dajin salsabeel Ya samu wuri a gefen wata bishiya ya binne gawar tsohuwa tamira, ya zu unna gaban abarinta yai mata addu'o'i yasha kuka kamar ba gobe, har shaida sai da yayi ma kabarin nata saboda yana da burin wata rana ya kawo masa ziyara tare da an uwansa prisoners don su yi mata addu'a. (Masu karatu kunji yadda akai salsabeel da su Deeja suka ku6uta daga Gidan kurkukun addara, nasan wasu zasu ce tayaya har suka dau lokacin nan batare da an ritsa da su ba? To idan ba zaku manta ba, shuwagabannin kurkukun addara basa a ciki, bayan haka an samu tawayar tsaro, sannan babu wanda yasan meke faruwa a sashen su Angel saboda an rikita lissafin Allon tsafin su, su kan su wa annan giants din da suka shigo sashen har suka ga salsabeel, bawai sun san me suke shiryawa bane, sun zo ne domin tafiya da su Deeja zuwa wani sashe na daban da suke tarasu don su basu ruwan sihiri wanda zai dawo masu da jinin al'adar su saboda su samu damar gudanar da black night in da za'ayi a arshen watan, amma saboda 6arnar da Danish yayi masu yasa duk wani shirinsu ya wargaje, ha a sunji zafin tafiyar garkuwa da kuma yaran daya tseratar daga tarkon su, wannan ne yasa lokacin da suka yi taron zaman tattaunawa aya daga cikin Elders Yace Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu mi e tsaye mun nema ma kanmu mafita ba,