← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 162 OF 247

Sashe 162

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

Walking slowly chief ya isa bakin bathtub in ya zu unna kan kafafunsa ba tare daya kau da ido daga kallon fuskar Danish ba. Allah kadai yasan farin cikin da ya mammaye zuciyar sa wanda misalta shi ma bazai yiwu ba, Yau da ya rasa an tahalikin nan Allah kadai yasan halin da zai shiga. Abun da ya faranta ranshi da baije ko'ina na, ko da suka bata mashi rai bai yi fushi ba, bawan Allah sai ya dawo gida yayi kwanciyar shi cikin ruwa hakan na nufin bazai iya rayuwa ba tare da yan uwansa ba, duk runtsi duk wuya yana atare da su. Cikin sanyin murya ya sake ambaton sunan shi"Danish" Shiru bai motsa ba, cike da fargaban kada ace wani abun ne ya faru da shi chief ya daura tafin hannunsa na dama saman forahead dinsa ya shafa shi har zuwa kan karan hancin sa. Ba zato ba tsammani yaji Danish Ya dam i wuyan Hannun sa, eye lids dinsa na kerma dakyar ya bu e idanun shi da su kai mashi nauyi ya dubi chief. Da wata irin kakkausar murya yace"saboda yan uwana na dawo nan" Wani irin faduwar gaba Unaisah taji, yayin da take kokarin shigowa toilet din cike da fargaban me zata taras jin shiru chief bai fito ba shiyasa ta yanke shawarar bin bayan shi. Lokaci aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata muryarshi, tayi matu ar yin mamaki saboda ita lokacin data shiga toilet din jibgegen wolf tagani zaune cikin bathtub in shiyasa ta raza, yanzu ta gane shi ne ya riki a ya dawo mutun. wani irin tsantsar farin ciki ne mara misaltuwa ya wanke zuciyarta, dama saida ranta ya bata zai dawo, hasashen da tayi ya tabbata maganar da ummi tayi ce ta tuna mata da ranar daya riki a kafin ya zama maciji da jikin shi ya dauki zafi rau cikin kwami ya shiga ya tsuma kanshi da ruwan sanyi. yanzu ta gane idan ranshi ya 6aci yana son yayi cooling temper dinsa ruwan sanyi yake shiga, taji tausayin shi, shi dai rayuwarshi wani sa'i kamar bata mutane ba. "Danish, ka tada min hankalina, daga ni har yan uwanka da abokan aikina, babu irin neman da ba ayi maka ba a garin nan, saboda kai ko abinci na gaza ci, ban ta6a tsammanin damuwar da nayi dakai takai har haka ba..." ya fa a yana kallon cikin idonshi. "Da na san ranka zai 6aci da ban matsa maka mun tafi head quarter ba, banji dadin abunda big guy yayi maka ba, na tsawatar mashi kuma ya gane kuskuren shi, bazai ara gigin bata maka rai ba" yanayin yadda chief ke yi mashi magana da sigar lallashi ba karamin kwantar mashi da hankali yayi ba, zuciyarshi taso ta karaya da jin irin kaunar da yake yi mashi, tun daga kan facial expression dinsa yaji ya yarda da duk wani abu daya fa a masa. "Kayi hakuri idan na bata maka rai, sannan inaso Ka fa a min duk wasu sharrudda da zamu bi don mu zauna dakai lafiya batare da mun 6ata maka rai ba saboda naji jiki ba ka an ba lokacin da aka sanar dani ka fita nayi zaton bazan ada ganinka arayuwata ba" softy ya fada tare da tsamo hannun Danish daga cikin ruwan ya ha e yatsun hannun su cikin na juna, yayi shiru yana sauraron shi. "Sannan Alfarmar da zan roko a gurinka, nasan baka yarda da ni ba, amma dan Allah ko dan saboda yan uwanka kada wata rana kayi fushi ka koma inda ka fito.." ya an dakata yana kallon yanayin fuskar Danish. "nasan za ka yi tunanin kodan saboda ina son ka bamu hadin kai shiyasa nake lallashin ka, ba haka bane, Kamar Yadda Allah ya jarabci Uncle dina da kaunarka nima haka nake jinka a zuciyata" Unaisah dake atsaye bakin toilet door din gaba daya tana sauraran maganar chief, zuciyarta ta karaya da tausayin su, aranta ta ayyana wannan wata irin zazzafar kaunace suke yi ma shi? Anya Danish bai da ala a ta jini da su? Lumshe idanun shi yayi tare da numfasawa slowly ya ware eyes dinsa akan fuskar Chief Baiyi tsammanin zai tanka ma shi ba, in weak Voice Danish Yace"ban ru e ka a zuciyana ba, amma ku daina bata min rai in na nuna bana son abu kada ku tursasa min, ni bana so na cutar da kowa, shiyasa na ke6e kaina saboda in sanyaya zuciyata, kamar yadda kake jina a zuciyarka nima haka nake jinka, ha in kaine kawai bazan baku ba, sannan ka yi hakuri da bata maka rai da nayi, I didn't realize I was rude to you and disrespected you until he told me." runtse idanu chief yayi gam na dan wani lokaci bai furta komai ba, har cikin ranshi yaji dadin maganar da Danish Ya furta mashi na cewa shima yana jin shi kamar yadda yake jin shi, yasan sannu a hankali wata rana zai samu amincewar shi. Phone ringing dinsa ne Ya sa shi hanzarin bu e idanun shi tunawa da bakin su, wrist watch din hannun shi ya duba. "Danish, Ka fito daga cikin ruwan nan haka, Inaso Ka shirya, nasan kana jin yunwa, zan sa ashirya mana dinner" Amsa mashi yayi da Okay Fitowa Chief yayi daga toilet din, Ya zaro wayar daga trouser pocket dinsa, misscalled ya gani da layin big guy. Kira ya danna masa bayan yayi picking, big guy ya sanar da shi cewa yanzu haka suna akan hanya sun dauko su commender daga airpot. fuskar shi da fara'a ya furta Alhamdulillah Allah Ya kawo ku lafiya, bai sanar dashi game da ganin Danish ba, ya bari sai in ya zo gidan ya ganshi. Bayan sun yi sallama, Ya kira layin Ci ya sanar da shi game da ganin Danish yace ya sanarma sauran abokan aikin su, Ci yayi farin ciki sosai harya shawarce shi akan su lalla6a shi kada su yi duk wani abu da zai 6ata ma shi rai. Sai da ya kammala yin wayar ya lura babu Unaisah a dakin, ranshi ya bashi may be ta fita ne don ta sanar da uwanta. bayan fitar Chief da yan mintuna, A hankali Danish Ya futo daga ciki, har ya cire kayan jikin shi, short kadai Ya bari, sumar kanshi dake a jike ta manne ma fatar bayan shi da gefen fuskar shi, tamkar babu kuzari a jikinshi da wata irin kasala yake taka kafafun shi, a duk lokaci daya riki a ya dawo suffar shi ta mutane ba karamin jiki yake ji ba. Gaban dressing mirror ya dakata da tafiya ya dafe gaban mirror in da tafin hannun shi aya. Kunnuwan shi ne suka soma jiyo ma shi motsin mutun a dakin shi, yayi zaton chief ne hakan yasa bai damu daya ago da ido ya kalle wanene ba. "Meyasa ka tafi batare da ka fada min inda zaka je ba? Kasan irin tashin hankalin dana shiga na rashin ganin ka"? Da sauri ya kalle ta ta cikin madubin Tana tsaye abayan shi ta goya hannayenta kan kirjin ta, abayan labulen dakin shi ta la6e saida taga chief ya fita tukunna ta fito don ta samu damar zazzaga mashi masifa. Har sai da gabanshi ya an fadi ganin yadda idanunta suka kumbura sun ka a jawur ko ba afada masa ba yasan tasha kuka tamkar ranta zai fata. tuni yasha jinin jikin shi yasan ba zai tsira daga fushinta ba dole ta hukunta shi. Bai aune ba, yaji ta fa a kan faffa an bayanshi ta zagayo da hannayenta kan broad chest din shi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rufe idanunta da ke tsiyayar da ruwan hawaye ta dunkule yatsunta kamar yar dambe ta dinga bugun kirjin shi da karfi, duk da hakan bata huce ba sai da ta gartsa mashi ciwo har sau uku akan fatar bayan sh Ko ka an baiji zafin abun da tayi mashi ba, ya fahimci irin radadin da taji na rashin shi yasan tayi tunanin Ya koma kurkuku ne. Cikin shesshekar kuka take fada mashi abunda ya faru bayan tafiyar shi. Zuciyar shi ta karaya ya kara jin tsantsar kaunarta da sonta acikin zuciyar shi, yadda takusa salwantar da rayuwarta saboda shi! Duk da fushin da take da shi na abunda ya faru tsakaninsu hakan baisa ta daina damuwa da shi ba, kamar ma ana kara mata zazzafar kaunar shi. yayin da yake wannan tunanin idanunshi sun cicciko tab da kwalla a hankali yake kallon hannuwanta dake akan kirjin shi ta gama naushin nashi yanzu tsunkulin kirjin shi ta ke yi duk fa don ta huce radadin daya kunsa mata, zuciyar shi tayi matu ar karaya saboda tausayin rayuwarsu daya kama shi, yana jin tsoron ranar da mutuwa zatayi masu yankan kauna, yasan dole wata rana aya ya riga aya mutuwa acikin su, fatanshi Allah yasa in ma mutuwarce ta fara daukar shi saboda baisan yaga mutuwar Unaisah, ko ma ta auke su atare saboda yasan ba lallai ta iya surviving batare da shi ba, yana aya daga cikin dalilin dayasa yaki yarda ya bada hadin kai saboda shi ya san me zai biyo baya. Lumshe idanun shi yayi yayin da siraran hawaye suka fara yar tseral kan kuncinsa, shesshekar kukan ta da yake ji a kunnansa ba karamin karya masa zuciya ta ke yi ba. Sai da tayi mai isarta, tayi shiru tana kara makalkale jikin shi yana jin duk wani motsinta a jikinshi harta bugun zuciyarta da dumin jikinta duk yanaji anasa jikin.. In a weak voice ta fara magana taja jan numfashi "Ban hana ka tafi duk inda zaka je ba, amma ka fara tunanin wani hali zan shiga kafin ka yanke shawarar tafiyar, sannan in ma zaka tafi toh ka tafi dani, idan ba haka ba zan hadiyi zuciya na mutu ne" bata kare maganar ba, yai saurin ruko hannunta acikin nashi ya janyota ta dawo ta gabanshi yayi saurin rungumeta tightly a kirjin shi kamar zasu koma mutun daya. hijab din jikinta ta ji e sharkaf da gumi kamar babu a.c adakin tsabar hucin da jikinta keyi mata ba, da alama Unaisah ta manta da hudubar aunty umminsu ta kuma manta da sharuddan data
Chapter 162 · 0% Book details