← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 26 OF 247

Sashe 26

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

baki yayi masu magana amna yakiya sai dai fa kallo ko irin sakin fuskarnan babu Hakan bai wani dame su ba, tun da ya farka falillahil hamdu, duk wannan mai saukin ne, dama sun riga da sun san halin kayan su, bayan sun gama murnar samun lafiyan dan uwan nasu, Ummi ta tattarasu suka koma dakunansu, kowan na su yayi wanka, Suka soma shiryawa cikin kayan su cike da zumudi, bayan haka dangane da abun da ya faru a hall na kashe Hasken lantarki aikin chief owais ne shine ya tsara komai, tare da interior designers da sukayi decoration na hall din saboda yana son yaga reaction din family nasa, bayan ya gama tsara komai, Shi yafara halartar dinner din, ya riga su Unaisah tafiya kamar yadda ya tsara saboda yana son ya fara yi masu hanyar shiga batare da an samu matsala ba, tun da wurine mai tsaron gaske, su boss da big guy ne da wasu daga cikin jami'an isod sukayi jigilar daukar su Unaisah a cikin motocin su, suka kawo su bakin hall din, bayan tafiyar su tuni Ummi ta shirya saboda ta samu amincewar chief akan fitar da za ta yi, taje ne ya nema mata alfarma, Jami'in isod ne yayi driving dinta zuwa gidan da tace zata je na kawarta. (Wannan shine abunda ya faru kafin zuwansu dinner hall din) (CIGABAN LABARI) Ha a ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...? Jinjina mashi kai chief owais yayi alamar eh, wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarshi dauke da wani irin annurin farin ciki mara misaltuwa da tafukansa ya tallabo fuskarshi yana bin shi da kallo mai nuni da tsantsar aunarsa, kasa jurewa yayi baisan sa'adda Ya janyoshi zuwa ga faffadan kirjinsa yai huggin insa tightly kamar zai mayar da shi cikin cikinsa, hannayensa biyu dukansu ya tallabe bayan danish dasu, yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da bugu mai tsanani, wani irin yanayi mara misaltuwa.... Hakan ba karamin aga hankulan mutanan dake a hall din yayi ba, gaba aya sun ara rudewa da ganin rungumarshi da prime minister yayi. Muryar Hajiya saratu tamkar zata fashe da kuka ta furta"wai ba zakuyi mana bayanin su wanene ba? Kun barmu atsaitsaye cirko cirkon kamar sakarkaru" ta fada tana kallon chief owais don ta fahimci yasan da zamansu tun da taji Pm hateem ya tambaye shi shine.... "Owais su wanene wadannan Yaran! "? Baba obie ne ya furta maganar Sai lokacin chief Owais ya soma takowa yana tunkaro wurin da su ke atsaitsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya soma magana genlty "A gafarce ni, nayi laifi ban sanar da zuwan su ba....' ya fa a awayance yana bin kowan nan su da kallo. "Idan ba zaku manta ba, na ta6a baku labarin Yaran da Sojin america suka tsinta a evil forest, suka dam a case dinsu ga hukumar mu ta Isod, ga wadanda basu san da zaman su ba, to ga su nan, sune yaran da nake ru o a hannuna, na gayyace su ne don su gana da dangina saboda sun zama tamkar an uwa agare ni" Lokacin da ya arasa maganar, hajiya saratu ta zabga salati tana huci ta furta"wlh baka isa ba Owais! Ka haukace ne? da Zaka kwaso mana tsintattun Yaran da ba'asan asalin su ba, ka kawo mana acikin dangi? Anya kuwa kana a hayyacin ka? Rai amatu ar 6ace tayi maganar, Hankalin su Unaisah ba karamin tashi yayi ba, Masu tsoro acikin su har sun fara Ja da baya jiki na kerma... A matu ar firgice Senate Lateef Yace"kana nufin an uwan yaron nan da ya riki a ya koma maciji"? Wannan maganar da senate lateef Ya furtane Yaja hankulan mutanan Hall din, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, Muryoyinsu a kidime suke maimaita kalmar maciji ga wadanda basu san da zancen faruwar lamarin ba, nan take Pravin yayi wuf ya kwashe komai daya faru ya sanar da su, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un shine abunda suke furtawa a bakunansu.... Prime minister sam baya gane me su ke cewa saboda idanunsa sun makance, Ya kurmance baya ji baya gani tunda ya rungumi danish a jikin shi bai ara ago da kanshi ba, Kamar daga sama yaji an dam i damtsen hannunsa da arfi aka raba shi daga jikin danish wanda bakowa ne yayi hakan ba face Senate Lateef, ya janye shi gefe guda, Yana faman zazzaga masifa"wlh bazamu lamunta ba! Don Na fahimci bakasan ciwon kan ka ba, taya zaka kwaso mana mugun abu ka kawo mana a cikin dangi? Wannan wata iriyar masiface? So kake ka tarwatsa mana farin cikin mu? Ko kuwa so kake ka arar mana da dangin mu ne!? Wai ma wanene ya baka shawarar ka kawo su wurin nan....."? Tunkafin Senate lafeef ya kare maganar, sautin shesshe ar kukansu Ya soma kara e hall din, sun girgiza da jin munanan kalamin da ake fada akansu, bayin Allah da farin cikin su da zumudi su ka zo ganin dangin chief owais sunyi tsammanin suma zasu sosu kamar yarda shima yake son su ashe ba haka bane......' "Wallahi sai dai ka za6a, ko dai ka tattara su ku koma can gidanka, ko kuma mu mu fita mubar maka hall din ka are dinner din tare da su, don wlh baka isa ka jazamana masifa ba, wannan ay annobace ka kwaso mana" acewar hajiya saratu ta fa a tana watsa hannayen ta. Chief owais dake sauraronsu aya bayan aya yake binsu da kallo daman yasan za'a rina ba lallai su wanye lafiya ba, sai gashi ta tabbata, kowa da abun da yake tofawa, mutane alilan ne basu tanka ba. Hankalin Hateem yafi na kowa tashi, ganin za'a raba shi da muradin ranshi, Ga samu ga rashi, Ji yake tamkar Ya fasa ihu, iri iri su Senate lateef sun rurru e hannayenshi gudun kada Ya ara tunkarar Danish. Security advisor din Hateem ne ya tambayi meke faruwa ne? Muryarsa a bubbu e yasha ya bugu baya gane komai sama sama yake jin kan shi, Kasancewar basa jin yaren hausa basu san takan zancen ba, da sauri pravin uban an zigi Ya bu e baki da niyar Ya sanar dasu, wata irin tsawa mai kama da saukar aradu chief owais Ya sakar mashi, wadda tay matu ar gigitasu a hanzar ce yaja baki ya yi shiru. Dalilin dayasa ya yi mashi hakan gudun kada ya sanar da su, don muddin sukaji da zancen Yaron daya rikida ya koma maciji to kuwa nan take zasu sa a dakatar da taron bayan haka zasu sanya jami'ansu su kori su unaisah don ba zasuyi ganganci da rayuwar hateem ba... Cikin sanyin murya prime minister yayi ma mutanansa bayani da yaren da zasu gane ya kwantar masu da hankalin su, da cewa family issue ne kuma in sha Allah zasu shawo kan matsalar yanzu, iya abun da ya fada masu kenan, dama kuma ba ahayyacin su suke ba, shiyasa abin yazo masa da sauki da tuni sunsa an tada taron gaba aya. Da kakkausar murya chief owais Ya soma magana babu annuri akan fuskarshi. "ni ne silar dana kawo su wurin taron nan, bawani ya bani iznin in gayyace su ba, kuma basu suka nuna suna son zuwa ba, face don ni nake so su zo...." bai are maganar ba, Hajiya saratu tayi yunkurin dakatar dashi aikuwa a fusace Ya aga mata hannu alamar tayi shiru, Waro idanu waje tayi ba ita ba hatta sauran mutanan hall din sunyi mamakin rashin kunyar da owais yayi. "Suma ya'yane kamar kowa! Yaro kuma da bashi da lafiya, Bayin kanshi bane, Aljanu ne suka shafe shi, kuma ya samu lafiya bayan da shiekh Imam ya dau kwanaki Yana duba shi.....' bai are maganar ba, muryar sheikh imam ta kara a kunnuwansu a yayin da yake shuowa dakin taron. "Tabbas maganar owais gaskiya ne, Yaran nan ba masu cutarwa bane, mutanene kamar kowa, kuma abin a tausayamawa ne....." a tsanake cikin hikma sheikh imam ya fayyace masu komai dangane da halin da danish yake a ciki, wasu sun fahimta yayin da wasu sam kamar kurame basa gane komai. Gaba aya hall din Ya rikice da maganganunsu, wasu suna hura wutar akore su daga hall din yayin da wasu sukayi shiru basu tanka ba irin su mai girma sharafudden, sun natsu suna bin duk wani mai magana da kallo, ga dukkan alamu akwai abun da suke jira shiyasa suka yi shiru. Cikin sanyin murya prime minister yace"dan Allah kowa yakwantar da hankalin shi, Idan har saboda ni aka shirya dinner din nan, to ina rokon alfarmar ku bar su na yau kawai su zauna, in sha Allah ba abinda zai faru" idanunshi akan danish ya are maganar, wanda tun shigowarshi hall din idanunsa suke alumshe tamkar ma baisan sunayi ba, su batool daine suka ru e jikinsu sai kerma yakeyi bayin Allah sun firgita. "Meye amfanin kawo su wurin nan? Inace an shirya dinner din nan ne saboda mu an family ba bare ba! Don haka afitar mana da su idan ana son zaman lafiya, idan ba haka ba mu zamu tattara yanamu yanamu mubar masu hall din" rai a6ace hajiya laurat tayi maganar tana faman ha e rai. Runtse ido chief owais ya yi, har cikin ranshi baiji dadin irin tarbar da akayi ma yaran ba, zuciyarshi ta raunana duk sai yaji dama bai sa anzo da su ba. _Cikin sanyin murya mai ratsa zuciya Unaisah ta soma magana"dan Allah ku yi hakuri idan mun 6ata maku ra i, wlh ba mu zo da niyar mu cutar da kowa ba, hasalima ba da son ranmu mu zo ba, face don chief ya nuna yana son mu ziyarci danginsa, ba ku san mu ba, muma bamu san ku ba, bai kamata kuna munana mana zato ba, akan abun da baku da tabbas akanshi_ tun da ta fara magana hankula suka dawo kanta, Idanu zuru zuru cike da mamakin karfin halin ta. _A hankali ta sanya hannu ta cire facemask din fuskarta tare da jefar da shi gefe aya, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Hankalin maza ya tashi da ganin kyakkyawar fuskar unaisah wadda take a jike sharkaf da hawaye_ _Cikin murya kuka taci gaba da cewa"Idan bakusan ganin mu ba sai kun kore mu ba, zamu tafi da kafafuwan mu,' kalamanta
Chapter 26 · 0% Book details