Sashe 100
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
back seat, security din da zai yi driving dinsu yana a mazaunin driver, Hajiya saratu na daga gefen shi... Kaitsaye motar ta nufi cikin estate din "Kamar yadda nake fada maku, munyi magana da shi jiya, nayi masa bayanin komai dangane da zuwan ku, to a gaskiya yarinyar bata wurin ku ba ce, amma yace zai iya baku ita har zuwa time da ita patient din naku zata ji sau i...." fuskarta babu fara'a tayi maganar. kallon juna zahra da Aneelerh su ka yi jikin su yayi sanyi lakwas... Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"hakan ma yayi mungode sosai..." ___________________________________ Firgigit ta farka daga bacci tana faman zazzare gray eyes dinta tamkar kwayar idanunta zata fa o kasa, hannun ta aya dafe da goshin ta, numfashin ta na fita da sauri, kwata kwata babu kuzari a jikinta kamar wadda aka zarewa laka, ga wata kasala data baibaye sassan jikin ta, dakyar ta yunkura ta mi e zaune tare da jingina bayanta jikin pillow, fuskarta ta kumbura suntum, kumatun sunyi jawur, haka la66anta ma sun dan kumbura, idanunta sun ance kwarmin idon yayi ja daga gani ta jigata ba ka an ba... Lokaci aya walwarta ta fara tariyo mata abunda Ya faru da ita adaren jiya, runtse idanunta tayi sosai kwallar da ta taru acikin su ta fara ar tseral kan kuncin ta, ta rasa gane meya faru? Shin mafarki ne ko gaske? Kokwanto ta soma yi saboda zuciyarta tagaza yarda da abun da ya faru, was wasi ta kama yi tana faman tariyo komai daya wakana adaren jiya, babu wata alama da zata tabbatar mata da abun ya faru dagaske, da sauri ta dubi yar rigar jikin ta, tayi uban squeezing kamar an watota daga bakin kura, da sauri taja rigar ta rufe santala santalan laps dinta, ta sauko daga kan gado tana faman bin dakin da kallo, mirror chair ta gani yashe ta jirkice kan floor "Ina wandona Yake"? Ta jefa ma kanta tambayar, Ringing din wayarta ne Ya doki dodon kunnanta, jiki na rawa ta nufi toilet saboda tana tunanin kamar anan ta cire wandon Tana shuga ciki ta iske shi akan hanger, tunawa tayi da jinin daya dawo mata gadan gadan adaren jira aranta ta ayyana shima dagaske ne ko duk cikin mafarkin ne"? Ta kare maganar tare da bu e laps dinta ta laluba jikin ta, bata ga komai ba, sai dai wani farin ruwa mai yau i yau i dake gangarowa... Gaba aya ta gama rikicewa, tunaninta ya kasu gida biyu, ta jima a toilet din kafin ta fara tunanin yin wankan Bada jimawa ba, ta fito sanye da rigar wanka, har ta kusa isa gaban mirror tajiyo bugun kofa, "Wanene"? ta fada tare da kallon ofar "Daddyn ki ne..." sanyi taji ya ratsa zuciyarta, da sauri ta nufi kofar ta bu e mashi Tun daga kasa ta fara kallon shi, jallabiya ce a jikin shi maroon colour, sai kamshin turare ke tashi a jikin shi "Daddy, Ina kwana..." bata are maganarba, ganin yadda yake binta da kallo mai tattare da ru "Unaisah! Baki da lafiya ne? Meya faru naga fuskarki ta kumbura tayi ja, kamar kinyi kuka..." wani irin mugun bugu kirjinta yayi, babban tashin hankalinta kada ace abunda Ya faru jiya dagaske ne, ba mafarki ba Muryarta adabarbace ta furta"da.. ddy.. lafiyana lou, meka gani ne."? girgiza kai taj yayi"no ban yarda ba, fada min ko dai wani ya buge ki ne"? "Wallahi daddy ba komai, watakil ko dan saboda firar da muka tsaya yi jiyane ban samu isasshen bacci ba shiyasa fuskata ta kumbura..." kwata kwata hankalinsa bai kwanta da yanayin ta ba, janyota yayi tare huggin dinta, ya daura hanneyensa akan bayanta "Nayi missing dinki my daugher, ina fata kin tashi lafiya.." "Lafiyalou daddy ..." dago da kanta yayi"baki jin ciwon kai? Ko zazza6i haka" aro murmushi tayi akan fuskarta duk don ta kwantar mashi da hankalin shi "Bana jin komai daddy, ni yau da karfina na tashi..." ajiyar zuciya ya sauke "Okey, ki shiga ciki ki karasa shiryawa, Chief Yana son ganin ki" waro idanu waje tayi alamar mamaki "Daddy ni kuma? aga mata gira yai alamar eh "Ki sanya kaya masu kyau, zan jira ki awaje" cike da mamaki ta amsa mashi da toh, Bayan fitarshi cikin sauri ta nufi closet dinsu, ta dauko wasu hadaddun riga da wando an pakistan, rigar fara wandon yellow, veil din kayan yellow, ita kanta data sanya kayan saida ta jinjina ma kyan da sukai mata, gaban mirror ta zauna ta fara gyara sumar kanta dakyar take sharce ta da comb, bayan ta kammala gyara gashin, ta shafa powder da lipstick, kafin tayi rolling veil din akanta, takalma ta dauko masu tsini ta zura su a kafafunta, Komawa tayi gaban mirror ta feshe jikin ta da turare Har lokacin bata daina tunanin abun da ya faru a daren jiya ba, was wasi take tayi aranta.., kwata kwata bata so ya zamana gaskiyane abun da ya faru da ita.... A hankali ta zura kafarta ta fito daga dakin, Walking slowly ta nufi daddyn ta dake atsaye yana jiran ta, babu kowa a falon da alama basu kaiga fitowa ba "Daddy yunwa nake ji, Ciki na babu komai.." ta fada yayin da ta ruko hannunsa acikin nashi "Kada ki damu, nima banyi breakfast ba, idan munje wurin chief din zamuyi atare da shi..." amsa mashi tayi da toh Kaitsaye suka nufi walkway bata san ina za su bula ba "Daddy ba part dinsa zamuje ba"? "Eh, yace mu same shi a backyard.. Zazzaune suke akan wasu jigunannun sofas an ubansu, backyard din ya Ha u an awata shi sosai, chief da hajiya saratu suna a zaune kan sofa daya, Aneelerh da zahra suna fuskantar su, tun da suka zauna Aneelerh take ta jinjina ma haduwar gidan da shi kanshi mamallakin gidan wato chief, kallo aya tayi mashi saida gabanta Ya fa i, ya auki wankan suit navy blue sunyi bala'en yi mashi kyau Zahra dake satar kallon shi, gani take kamar a mafarki yau gata ga director general na isod, crush inta, mutumin da tayi haukan son shi a lokacin baya.. Round table din dake a tsakiyarsu, cool drinks ne da Snacks asaman hadadden wooden tray "Idan muka baku aron yarinyar sai yaushe ne zaku dawo mana da ita.."? Hajiya saratuce tayi masu tambayar "Idan da hali har zuwa lokacin da benazir din zata ji sau i, dan Allah ayi mana alfarmar nan..." gya a kai hajiya saratu tayi"okey, amma fa zaku bani tukuici tun da ni nayi maku hanya a wurin chief..." ta fa a da yar zolaya tana kallon su Murmushi suka saki zahra tace"bakomai mommy, ay duk abunda kikeso zamu baki.." yar dariya tayi"zolayarku nakeyi..." dariya sukai su kansu sun san tafi karfin tukuici, ta dai fa i ne don ayi raha... Kwas kwas sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka dago tare da kallon inda sautin ke fitowa.... *Daga alkalamin Boss Bature mu ha u next page on monday idan Allah yakaimu da rai da lafiya *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions Buy bestselling books online [14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 30 Novels Elite Admin August 11, 2024 Sponsored Link Novels Elite English Kwas! kwas !! sautin takalmanta Ya ratsa kunnuwansu, kusan atare su Aneelerh suka ago tare da kallon inda sautin ke fitowa... ura idanu sukayi suna kallon su, kafin Aneelerh tayi wani irin yunkuri ta mi e jikin ta na 6ari, zuciyarta na dakan uku uku, gaba aya tabi ta rikice gani take kamar a mafarki take kallon su!! Kokwanto ta farayi anya kuwa sune? Tajudeen da Angel? Ko dai idanunta ne suke nuna mata badai dai ba? Tayaya mutanan da suka 6ace almost 16years yau kwatsam ta gansu, da ransu da lafiyar su, kanta ne ya wani irin sara mata da sauri ta dafe goshin ta, ganin hakan yasa Zahra ta mi e a matu ar ru e take kallon Aneelerh... Lokacin da unaisah ta aura kwayar idanunta akan fuskar Aneelerh, Ras taji gabanta Ya fa i, wani irin burki taci ta dakata da yin tafiyar, idanunta azare take kallon ta, wlh ko amafarki taga fuskar Aneelerh sai ta shaida ta balle kuma azahiri, La66anta na kerma ta furta"Aunty Aneelerh? Daddy! Auntyna ne? Ita ne nake gani azahiri ba mafarki ba? Daddy wallahi itace aunty Aneelerh ce...." kalamanta ne suka dira akan kunnan Aneelerh, baiwar Allah jiki na 6ari ta watso da gudu mayafin ta har yana arin zamewa, da gudu unaisah ta nufe ta, takalman kafarta suka kusa kayar da ita kasa, amma ahaka ta jure don bazata iya jira aunty Aneeleeh ta karaso gareta ba, zubewa Aneelerh tayi akan gwiwowinta tare da ware hannayenta biyu ta rungume unaisah, tayi hugging dinta tightly lokaci aya suka fashe da matsanancin kukan farin ciki mai tsuma zuciya A