Sashe 88
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
Yai hanzarin katse ta da cewa"dan Allah kiyi hakuri ki daina aga masa murya, jiya agajiye muka dawo gidan shiyasa Yace haka" harara ta wurga masa"kai ay saboda yarkace jiya ka hana idon ka bacci duk da agajiyen ka dawo gida, na tabbata da ace yarsace ke ahalin da benazir take aciki wallahi ba zaka iya runtsawa ba...." tun da tafara magana Alhaji musa Yake bin ta da kallo, arayuwarsa Ya tsani mutumin dake masa fa a Yana aga masa murya, babu wanda ya ta6a gigin yi masa hakan sai hajiya layla.... Dr shureim Bai tsaya kula su ba, ya juya ya nufi dakinsa zuciyarsa sam bata masa dadi, lamarin Family dinsa Ya fara gundurarsa kwata kwata ba zaman lafiya daga wannan sai wannan Jinjina kai Alhaji musa Yayi, ba tare daya tanka mata ba, har Ya aga afa zai wuce Hajiya layla ta dakatar da shi ta hanyar shan gaban shi Da mamaki Ya dago Yana kallon ta "Wallahi babu inda zakaje! In har bakasa an bu e kofar dakin benazir ba ni kuma bazan ta6a bari kabar wurin nan ba..." tana huci ta fa a ha i da ru e qugun ta, wlh a lokaci niyar kwashe ta da mari yayi amma sai Ya fasa Yatsun hannunsa har kerma su ke tsabar 6acin rai, wai shi yau mace zata tari gabansa? Batare da jin shakkarsa ba? Wacece ita? Dame take ta ama ne"? "Layla ba haka mukai dake ba! Kin manta alkawarin da kikai mun na cewa ba zaki ara shiga huruminsa ba"? Azafafe ta kalli Alhaji ubaid"ban manta ba, amma wallahi Yau bazan raga masa ba, ay shi yasan ta yadda zaisa abude kofar, don haka bazan tsaya inaji ina gani in rasa ata ba dole yasa aballe kofar can" ta yi maganar tana watsa masa harara... Fashewa da kuka zeenatu tayi jikin ta har jijjiga yakeyi, cikin shesshekar kuka tace"daddy dan Allah kasa a bude kofar, ni bana son inga kuna samun sa6ani atsakaninku, dan Allah daddy ka taimaka mana..." kukan zeenatu ba karamin tafasa zuciyarsa yakeyi ba Gauran numfashi Yaja, tare da an jinjina kansa Yana huci kamar mayunwacin zaki ya dubi hajiya layla da tai masa erere kamar zata rufesa da bugu A fakaice taga Ya sakar mata wani shu'umin murmushi har saida taji gabanta Ya fa Sassauta fushin fuskarsa Yayi"naji zan bu ofar, ki bani hanya na wuce" matsawa tayi idanunta akan fuskarshi Ya nufi kofar dakin benazir Yana arasawa bakin ofar, Ya aura faffa an tafin hannunsa, turata yayi wani iko na Allah sai ga ofar ta bu Kallon Juna Alhaji ubaid da Hajiya layla sukai, abun da daure kai tun jiya suke gabzar kofar donta bu e babu wanda bai jaraba karfinsa ba amma duk abanza ko motsi batayi amma shi daga turawa ta bu e wani irin arfi ne da shi? Basu tsaya dogon tunani ba, jiki na 6ari suka nufi akin zeenatu da gudu ta rigasu fa awa a ciki. Shugarsu keda wuya kowan nan su Yaci burki, Abun da suka gani Yayi matu aga hankulansu, kamar matatta haka suka hangota kwance kan floor rabin jikin ta a cikin toilet dake a bu e, kamar irin tayi gudu ta kife awurin har kanta Ya daku goshin ta Ya fashe "Innalillahi wa'inna ilaihirraji!"un"! hajiya layla ce ta zagba salati tana tafa hannayenta, zeenatu da ta gama ru ewa agaban benazir ta zube bisa gwiwowinta, takai hannu tana tatta6ata Aunty benazir! Meke damunki dan Allah ki tashi inna lillahi..mami daddy ku ce ta tashi dan Allah.... da sauri Alhaji Ubaid Yaje Ya ago da ita, jikinta duk Ya saki ya auko ta da hannu biyu ya kwantar da ita akan gadon ta, sumar kanta duk Ta yamutse Fita hajiya layla tayi jim ka an ta dawo da robar ruwa ta bu e murfin ta kur6i ruwan tare da furzar da shi kan fuskar benazir Ruwan na dura tayi wata irin zabura tana ambaton sunan taj ... adai dai lokacin shureim Ya shigo dakin ganin su tsaitsaye bakin gadon ta yasa shi saurin karasawa Tunkafin yayi magana Hajiya layla tace"shureim ka gani ko? Abun da nake gudu kenan! bansan ya akai ta fa i kasa daga cikin toilet, kanta Ya bugu..." Hankalinsa atashe Yake kallon Benazir yatsun hannunta sai kerma suke, ta runtse ido tana sambatu kwata kwata bata acikin hayyacin ta Zeenatu duk ta damu, Hannunta ruke dana benazir sai faman shesshekar kuka take "Ya akai kofar ta bu e"? "Uncle din ku ne Ya bu e kofar," ta bashi amsa ataikaice, Alhaji ubaid Tuni Ya fuce Yabi Alhaji musa don Ya fada masa halin da benazir take ciki A lokacin Har Ya koma Part dinsa, sallamar Alhaji ubaid ce ta katse sa kamar bazai fito ba, don saida Ya au lokaci har sai da hajiya sara tace da shi baiji ana sallama bane? Tukunna Ya mike cikin takun izza Ya fito daga dakin "Me kuma zanyi bayan na bu ofar"? A fa ace Ya fa a Yana ance idanunsa "Dan Allah ka yi hakuri da abun da layla tayi maka, bata jin maganata naja mata kunne taki bansan ya zanyi da ita ba..." ya mutsa fuska Alhaji musa yai"naji, Yanzu awani hali benazir din take a ciki? Kamar mai jin shakkarsa Alhaji ubaid Ya furta"mun sameta akwance kan floor, rabin jikin ta a toilet, kamar fa uwa tayi don har kanta Ya daku sosai, ta farka sai dai kamar bata a hayyacin ta shiyasa nazo don na sanar dakai...." ta6e la66ansa yai kafin yace"zanyi magana da likita na, zaizo Ya duba ta" godiya ya yi masa kamar zai masa sujjada, komawa cikin dakin yai hajiya sarah dake a zaune kan darduma ta mi e tana tambayarshi meya faru ne? Ko benazir ta bu e kofar ne' amsa mata yai da eh jiki na rawa ta fuce daga dakin don taje dubota... Gaba aya sun hallara a dakin Benazir kowan nan su Ya shiga hali na damuwa, bada jimawa ba Dr Mark Ya shigo gidan, wani basamuden Likita ne irin african american din nan, yadda kasan Jinin Alhaji musa, Fuskarsa babu fara'a, sumar kansa hada kitson zane, tun da Hajiya layla tayi arba da fuskar dr mark kuma taji cewa Alhaji musa ne Ya kira shi don Ya duba lafiyar benazir, tace wallahi bazai ta6a benazir ba, ai kwata kwata ita baiyi mata kama da likita ba, ta dinga surfa bala'e duk yadda alhaji ubaid Yaso Ya shawo kanta shi da su hajiya sarah akan ta bari aduba ta, amma abun Ya faskara a karshe sai dai Alhaji musa Ya sallami likitan Ya tafi ba tare da ya duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da abun da layla tayi Alhaji ubaid har Ya gaji da yi mata fa a, hajiya sarah ce ta basu shawarar su yi gaggawar kaita asibiti don abinciki laifiyarta, ba su tsaya bata lokaci ba, dr shureim Ya dauko benazir da hannu biyu ya tallabota, suka fito daga falon, A mazaunin baya na motarsa ya shigar da benazir, hajiya layla ta shiga ta rungume ta a jikinta, Alhaji ubaid Ya zauna a front seat tare da shureim, yayin da hajiya sarah ta shiga motarta tare da zeenatu kusan atare motocin suka nufi Gate din gidan, Wa annan gabza gabzan security officers din suka tari gabansu har sai da suka kira Alhaji musa Ya basu iznin su barsu su fita kafin suka basu hanya Direct suka nufi Obie International Hospital. __________________ANEELERH Wuraren arfe tara, Aneelerh ta kammala shiryawa cikin abaya tayi rolling, gaba aya ta agara su karasa estate din kamar tayi fiffike haka take ji, fitowa tayi daga bedroom dinta ta nufi dakin mami, bayan tayi sallama mami ta amsa mata ta shiga daga ciki ta gaishe da ita Kallo aya mami tayi mata ta fahimci kamar bata jin dadi "Aneelerh baki da lafiyane naga idanunki sunyi ja? Kokarin danne damuwarta tayi"mami lafiyata lou, ban samu isasshen bacci jiya ba..." "Meyasa? Kar dai ace damuwar abun da Ya faru jiya ne"? Girgiza kai tay"a'a mami na tashi yin nafila ne shiyasa banyi bacci da wuri ba..." "Kunyi waya da su benazir din? Inataso inji ko sun isa gida lafiya"? "Tun jiya bayan sun tafi nake ta trying layinta baya shiga, har da safen nan saida na kira ba'a aga ba "To Allah yasa dai Lafiya, Yanzu ina zakije ne naga kin shirya ko hakanan kikai gayu"? "Mami wani abun al'ajabi na gani jiya awayar zahra, wanda ya daure min kai shiyasa ma na shigo don in fa a maki" "To fa, menene ? Zaro waya aneelerh tayi daga handbag dinta, ta lalubo layin zahra ta danna mata kira, Bugu aya tay picking"zahra Kin gama shiryawa? "Eh yanzu zan fito" "Okey Ki same ni adakin mami dan Allah kada ki bata lokaci" Bayan ta katse wayar ta dubi mami"gata nan zuwa, abun da zan nuna maki yana awayarta" amsa mata mami tayi da toh cike da zullumin abun da zata gani Jim ka an zahra ta shigo dakin da sallama, Itama ta shiya cikin abaya maroon colour, ta yi rolling, hannun ta ru e da wayarta, a bakin gadon mami ta zukunna"ina kwana mami? Kun tashi lafiya"? "Lafiyalou zahrana, Ina abun da za'a nuna min"? danna wayar zahra tayi bayan ta bu o hoton, ta mi a ma mami wayar tasa hannu ta arba. kura ma fuskar unaisah ido tayi kamar ta an ru e can dai ta mi e daga kishigi an da take ta an kalli fuskar zahra da aneelerh kafin tace"wannan ay hoton Angel ne ko? Yaushe akai wannan hoton? Amma ya akai naga kamar ta ara girma anan..." at same time zahra da aneelerh suka saki murmushi saboda sunji dadin yadda mami itama ta gasgata abunda idanunta suka gane mata tunkafin ma su fada mata wa suke hasashen itace "Mami wannan yarinyar da kike gani sunanta Unaisah, a wurin dinner din prime minister zahra ta dauko hotonta a dakin taron..." da tsantsar mamaki Mami tace"oh wai da ba Angel din bace? Me kama da itace kenan"! "Mami itace, abunda muke hasashe kenan, zahra ki bata labarin abun da Ya faru a wurin