Sashe 164
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
sun cike dakin shi, wasu akan couch wasu gefe gadon shi har saman gadon. ta fahimci yau ba karamin nishadi suke ji ba. Kokari take ta hango Danish din duk sun rufe shi dakyar idanun ta suka hango mata bayan shi ya kifa kanshi jikin pillow, Unaisah tana kishingi e gefen shi sun shagala da kallon juna, sun bar su Batool sai umin surutu suke . Yanayin fuskartane Ya canza zuwa tsantsar mamaki da rudani, tun da take rayuwa agidan bata ta6a lura da zanan tottoo din shi ba, tasan yana da shi amma bata ta6a ganin dukanshi ba, sai yau datayi arba dashi babu riga a jikin shi, abunka ga farar fata zanan ya fito 6aro 6aro bakomai ne ya rudar da ita face ganin zanan tattoo dinsa sak irin na big boss kamar anyi copying tattoo din big boss an manna mashi abayan shi. wannan abu ya bata mamaki har ta gaza yi masu magana saboda kallon Abun al'ajabin daya ruke ta.. __________________________ Safa da marwa take yi atsakar dakin ta, fuskarta babu walwala ga dukkan alamu akwai wani abu dake damunta wanda yayi silar shigarta halin da take a jiki... Sallamar dr shureim ce ta katse zancen zucinta, kamar dama jiran shi takeyi da sauri ta nufe fuskarta ayamutse tace"shureim fita zaka yi ne"? Girgiza mata kai yai"a'a, wurinki nazo inaso muyi magana ne" ya fada tare da wuce ta ya zauna gefen gadonta, itama ta zauna tana kallon shi cike da son jin wata magana ne zasuyi.... "Meke damunki ne? Yanayin fuskarki ya nuna kamar bakya jin dadi"? "Shureim lamarin Benazir yana aga min hankali, kai baka lura ba har yanzu da yanayin ta ba? Wani lokaci tana abu kamar mai ta6in hankali ni tsorona kada ta haukace..." ta fa a sukuku babu walwala, maimakon taga tashin hankali akan fuskarshi sai taga ya saki tausasan murmushi arude tace"lafiyarka kuwa? Ko bakaji abun da nake magana akai bane" ruko hannayenta yayi acikin nashi, fuskarshi da fara'a tace"mommy zan fada maki gaskiya amma kada ki fadamawa kowa..." cike da mamaki tace"toh, Ina sauraronka" ta fada tana kallon cikin idanun shi "Benazir taji saukin abinda ke damunta, haukan da kika ga tanayi pretending ne, har tambayarta nayi meyasa take yin hakan? Sai ta nuna min bata son asan ta samu lafiya... Baki asake hajiya layla take sauraron shi tayi mamakin jin hakan aranta ta ayyaba lallai benazir ashe haryanzu tana nan da dabi'arta nayin karyar ciwo. "Amma shureim baka tunanin akwai wani dalili dayasa benazir take pretending? In ba haka ba taya mutun da lafiyarshi zai za6i zama mai ta6in hankali" ta jefa mashi tambayar Shiru yayi jimm shi kanshi yayi wannan tunanin amma koda ya tambayeta sai tace mashi bakomai. "Gaskiya bana tunanin akwai dalilin dayasa yakeyin hakan cos na tambayeta tace min bada wata manufa ba saina rashin son a rabata da azeezaty" Girgiza kai hajiya hajiya layla tayi"ni nasan kayana shureim, Benazir bata ta6a yin abu batare da dalili ba, dole akwai dalili, ni fa najima ina zargin da akwai wani abu da Benazir ta sani ko ta aikata wanda har yaja akayi mata asiri..." maganar hajiya layla ta aga hankalin shi tunawa da bibiyar rayuwar Benazir da akeyi acikin gidan dama kuma yana zargin wanda yayi mata asiri ne yake son karasa kasheta bayan haka itama Benazir din zai iya yiwuwa maganar hajiya layla ta zama gaskiya. amma saboda bayason aga mata hankali shiyasa yaki sanar da ita zancen bibiyar rayuwar Benazir da akeyi sai dai ya yanke shawarar zai je dakin Benazir don ya tambayeta meya faru da ita aranar data kulle dakin ta. Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar Hajiya layla ta katse shi"kaima kana tunanin abunda nake tunani ne ko kuwa" murmushin ya e ya sakar mata"mami bana so ki sanya damuwa aranki, hasashen da kike ba lallai ya zama gaskiya ba, zai iya yiwuwa wani tayi ma rashin kunya kinsan wasu mutanan da bakar zuciya ga mugunta arai watakil ita ta manta da ta bata masu rai shine su kuma da babu Allah aransu suka yi mata asiri don su kuntata rayuwarta, ko kuma wanda ya aikata mata hakan yayi ne da niyar ya auki fansar wani abu da ku ka ta6a yi masa..." dafe kirji hajiya layla tayi da tafin hannunta alamar ta shiga uku itama fa tayi rashin mutunci lokacin da Alhaji ubaid Yake akan mulki tunma kafin ya hau kujerar gomna ba mutunci ne da ita ba, yanzu ne tayi hankali ta gane Allah aya ne. "Ni fa ban fada maki donki tashi hankalinki ba, inaso ne na kwatanta maki ba lallai hasashen ki ya zama gaskiya ba, banaso ki matsa ma benazir kan ta ta fada maki meyasa take pretending, mu kyaleta kawai iyakacinmu da ita addu'ane kawai ubangiji Allah Ya kare mana ita daga sharrin duk wani abin cutarwa..." amsa mashi tayi da Ameen ita dai hankalinta bai kwanta da lamarin benazir ba. sun jima suna fira adakin harya bata labarin zuwansu gidan su Azeezaty duk don ya kara kwantar mata da hankali taji dadi kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsabar farin ciki. __________________________ akwance take kan gadonta, jikinta sanye da night dress, ta ru e wayar ta a hannunta, ta nutsu tana kallon hoton fuskar Unaisah dake akan wallpaper din ta... bata gajiya da kallon fuskar arta, takan wuni tana kallon hotunan su Unaisah ba tare da gajiya ba. kwantar da wayar tayi kan kirjinta ta age kai sama tana kallon ceilling. bakomai take tunawa ba face shawarwarin da Aneelerh ta bata akan yadda zata shawo kan Taj ta hanyar kyautata mashi tun shekaran jiya take tura mashi love messages har yau yaki mata reply kamar tay hauka, ta rasa ya za ta yi ta shawo kanshi har jaraba kiran shi tayi tun da ya aga sau aya yaji muryarta bai kara picking call din ta ba. ago wayar tayi ta shiga cikin whatsapp dinta, a chat dinsu da Anila tayi copying contact din Unaisah data turo mata.. Cike da marmarin son Jin muryarta ta sanya number din tana kokarin yin saving kwatsam ba zato ba tsammani taga number din already akwai ta a contact list dinta da sunan God gift, Yarinyar da ta kira wrong number a matukar rude ta kurawa contact din ido batare da kyaftawa. lamarin ya daure mata kai tunani tayi ko dai Aneeleerh wrong number ta tura mata? zuciyarta ce ta raya mata bakya tunanin duk itace? Dama kuma sunansu iri aya Unaisah hakan na nufin yartace yarinyar da suke waya? Ta jefa ma kanta tambayar, kokwanto ta farayi anya kuwa itace? Yarinyar fa ta fadamata ba abuja suke ba. "Bari dai na jaraba kira inji" call ta danna almost 20 times ba'ay picking ba, damuwace karara akan fuskarta, jin knocking in room door dinta yasa ta yin saurin aje wayar kan side drawer ta fara ha e rai zatay pretending... A hankali ta shigo dakin, Jikinta sanye da dogon hijabi, a tsakar dakin ta tsaya tana kallon Benazir kamar tana jin shakkar tunkararta, tayi mamakin Ganin zeenatu adakinta yau wata rana tun lokacin da aka sallameta ba ta kara kusanta kanta da ita ba. aranta ta ayyana watakil iskokan dake akanta ne suka saketa shiyasa ta fara neman su shirya da juna Kurama juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, har na tsawon mituna kafin zeenatu tay karfin halin firta"Aunty Benazir, zan iya shigowa ciki"? aga mata gira Benazir tay ba tare data furta mata kalma ba, wucewa tayi kan gadon ta haye tare da juya mata baya sunyi shiru kamar basu ta6a sabawa da junan su ba "Aunty benazir ina Azeezaty? Nasan kuna waya da ita, ba ta6a tambayarki ni ba"? Kallon bayanta Benazir tayi kafin tace"kina nufin babyna"? Tace Eh "Tana tambayarki, duk in mu ka yi waya sai tace in gaida mata ke.." dadine ya lullu6e zeenatu har batasan sa'adda ta aje kunyar gefe guda ta juya suka fuskanci juna ita da benazir "Itama ta damu dani, kamar yadda na damu da ita kuma tana so na" ta tambaya tana kallon benazir dake kallon ta.. aga mata gira tay alamar eh Murmushi tasaki"yaushe zaki kiramin ita mu gaisa"? "Gobe in sha Allah" washe baki tayi tana faman kyafkyafta blue eyes din ta... Ita yanzu tausayi zeenatu ke bata, shiyasa kwata kwata bata ru e ta aranta ba. Ganin kallon da Benazir ke yi mata yasa tay saurin rufe idanunta, cike da jin nauyinta tace"Aunty benazir dan Allah ki yi hakuri da abun da na maki" murmushi Benazir tayi"zeenat laifin me kika min"? "Banje asibiti na duba lafiyarki ba, bayan kin dawo ban kula ki ba" yar dariya Benazir tayi"haba karki wani damu wlh, nayi maki uziri ya shureim ya fada min bakyajin dadi .." ajiyar zuciya ta sauke har taji sanyi aranta, ta an bu e idanunta akan fuskar Benazir mi a mata hannu tayi"nayi missing dinki ba ka an ba sisterna rabin raina, da naganki adakina naji dadi, dariyar farin ciki zeenatu tasaki tare da kama hannun Benazir ta ru e shi gam a cikin nata. _________________________________ Bayan sallar Mabrib, gaba dayan su sunyi wanka sun shirya cikin shiga ta mutunci yan matan sun sanya abaya sunyi rolling kamar larabawa, mazan kuma sun sanya jallabiya kusan kalar shigar da su kayi aranar dinner din Hateem sun yi kyau sosai. a falo suka hallara mutun aya ke babu acikin su Danish da har yanzu bai karasa shiryawa ba, Ummi ma tana atare da su ta dage sai daukar su pics take yi saboda sunyi mata kyau "Wai su wanene bakin da zasu zo ne"? Sajeed ne yai tambayar idonshi akan Unaisah, yasan dakyar in batasan su wanene ba, "Nima bansani ba, na kosa naga su wanene mu kara hakuri su karaso Allah yasa muga alkhairi" su ka amsa mata da ameen, su jemimah sai yan guje guje suke atsakar falon ita da azeeza da parvin kamar wasu tsararrakin juna har saida ummi ta tsawatar masu kafin suka daina wasan.. "Ku nutsu pls, manyan bakine su zasu zo.." "Aunty ummi su wanene wai"? Akagare Hanna ta tambaya tana kallonta Ummi tace"nima bansan su wanene ba, amma boss ya fadamin bakin chief ne, tun da naji hakan nasan ba kananun mutane bane, shiyasa nace ku nutsu kada ay