Sashe 176
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
yi. "Me kike yi adakinsa? Har na tsawon awanni hudu"? He asked throwing her a suspicious look She could see the jealousy on his face Muryarta da inda inda tace"am..um..dama azu ne da dare naje kai mashi backpack in Unaizah daya bukaci yana son ganin ta saboda binciken da suke yi, shi ne da na shiga dakin na iske ya shiga toilet wanka, bansan bacci ya dauke ni ba, sai yanzu na farka..." kasa karasa maganar tayi ganin yadda ya matso kusa da ita kamar zai rufe ta da bugu tuni tasha jinin jikin ta, bakomai yake kallo ba face kayan baccin jikinta sunyi uban squeezing kamar an kwatosu daga bakin kura, zuciya da sa e sa e saita dinga hasaso mashi abinda ya shiga tsakaninta da chief har wani jirin 6acin rai yake gani a cikin idaninsa. Da wata irin kasalalliyar murya tamkar tame jin bacci ya furta"na yarda dake nasan ba zaki iya cin amana ta ba, amma meyasa zaki je dakinsa ki auki lokaci har haka? Ki rasa inda zaki bacci sai dakinsa"? Dafe kai tayi da hannu aya harta fara tunanin lallashin shi ta bashi hakuri amma da ta tuna maganar daddynta sai ta samu kwarim gwiwar cewa"Sai me Danish in nayi bacci dakinsa? Fiye da haka ma zan iyayi!" gabansa ne ya fadi cike da mamaki yake kallon ta "Ka bani kunya my man, ka rasa wa zaka butulce mawa sai Chief? Da ya Salsabeel? i heard everything daya faru tsakaninka da Chief" ta fada tana galla masa harara "Wai har elders kake ikirarin basu ta6a cutar da rayuwarka ba, kuma sune kake kallo amatsayin iyayenka! Are you crazy? Ko ka fara shaye shaye ne"? Ta fada tana kallon cikin idanunshi, babu alamun zai tanka mata, kamar ana tunzurata ta cigaba da cewa "Saboda me zaka i ba su ha in kai? Meyasa zaka rufawa Elders asiri? Ko dai kun ha a baki da su? In ba haka ba, tayaya zaka rufa asirin miyagun da suka kaskantar da rayuwarka saboda muguwar manufarsu akanka"! Runtse idanun shi yayi gam maganarta ta daki zuciyarshi bai ta6a zaton zaiji kalaman nan daga bakin ta ba. "Hmmm, dama nasan ba zaka ce komai ba, saboda baka da gaskiya Danish! I have been suspecting you for a long time since we were in prison baka ta6a fa amin komai dangane da kurkukun addara ba, ni ban ma ta6a sanin me ake aikatawa a cikin kurkukun ba sai da karanbani na yakaini na gani da ido, meyasa ka boye min a lokacin uhyum"? Bata jira amsar shi ba ta daura da cewa"Bayan haka ranar da Giants suka zo daukar Batool da hannunka ka mi ata, ta rayu ko ta mutu, baka damu ba, hakan na nufin kaima da sa hannunka ake akaita komai, watakil ma an le en asirin su ne halan...." kasa karasa maganar tayi sakamakon bugun handrail da yayi da tafin hannun shi, saboda zafin maganarta dayaji, bu e idanunshi yayi sun kada jawur ita kanta sai da taji gabanta Ya fa i amma ta dake ta jajirce don ta harzu a shi tayi karfin hali cigaba da magana "Ka sha fa amin kai garkuwane agareni, mai bani kariya, zaka iya komai dan farin cikina, Danish Ina son na tabbatar da son da kake min, shin zaka Iya sadaukar da farin cikin ka saboda nawa" ta fada batare da ta kau da ido daga kallon shi ba.. Jinjina mata kai yai alamar eh, murmushin gefen fuska ta dan saki kafin ta ha e fuskarta tamkar bata ta6a dariya ba. "Danish, Inaso ka yi masu jagora zuwa gidan Kurkukun addara..." bata kare maganar ba Yai hanzarin furta"bazan Iya ba, pls kada ki tursasamin inyi abunda banyi niya ba..." a rude yake maganar da kakkausar murya tace"nasan zaka Iya ne shiyasa na umarce ka da kaje, saboda ni nasan wanene Man dina, kada ka bani kunya, bansan ka da tsoro ba.." "Bazan je ba, bana son duk wani abu da zaiyi silar raba mu, suma ina jiye masu ha arin da zasu jefa rayuwarsu, Ja da Elders ba abune mai sau i ba, basu da karfin da zasu iya farmakarsu please understand me..." fuskarsa ayamutse yayi maganar "Danish Idan har bazaka je ba, to inaso ka sani zan yanke duk wata ala a dake a tsakanin mu! Saboda bazan ta6a auran ragwon namiji ba, matsoraci wanda bazai iya jefa rayuwarshi cikin hadari don ya ceci rayukan Al'umma ba ya kuma kawar da masu aikata zalunci a doron asa.." waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata fa asa. "Chief yafika jarumtaka, yana da zuciyar imani da tausayi, baisan mu ba, bai hada alakar komai damu ba, amma saboda kyakkyawar zuciyarshi burinshi Ya taimaki rayuwarmu data sauran yaran dake agidan kurkukun kaddara sannan ya kawar da miyagu a cikin al'umma bai damu daya rasa ranshi ba! a shirye yake da ya sadaukar da ranshi saboda ya ceci rayuka kaifa? Ta jefa mashi tambayar shiru yayi bai tanka mata ba "Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai ku i mai asali an babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?...dakyar ta are maganar saboda hawayen da suka kubce mata tana mai jin takaicin tilasta masan da take kokarin yi. "Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"? Cikin shesshekar kuka ta fa "Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaki? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili dabaisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"! Kiris Ya rage Ya yanke jiki ya fadi saboda wutar bacin rai data ziyarci zuciyar sa Maganganunta sun ta6a zuciyarshi ba adan ba, Yaji zafin su sosai, ita kanta ta tsorata da ganin yadda gumi ke tsastsafo ma shi, duk da tana jin tsoron kada Evil's heart dinsa ta motsa, amma dayake idanunta sun rufe burinta kawai ya amsa bukatarta. Da wata irin karyayyar murya mai cike da 6acin rai ya furta"Angel, mafarki nake ko gaske? Da kanki kike jifana da wa annan munanan kalaman? ni Angel? Your Shield"? numfashi ya an ja kamar bazai iya karasa maganar ba yace"meyasa zaki min haka? Lafin me nayi maki da cancani cin mutunci daga gareki? Angel kema Kina min kallon jahili? Mara asali? Kuma kika kira ni da matsafi"? aga mashi gira tai"Hell fucking yeah, ko nayi arya ne"? Kasa magana yayi, "abu aya ne zakayi wanda zai wanke ka daga gareni, shine Ka cire tsoro, Ka basu ha in kai akai farmaki gidan kurkukun kaddara, ta hakanne ka ai zan yarda dakai in kuma har ka bijire min kaki bin Umarnina, wlh na rantse da wanda raina yake a hannunsa muddin baka bada goyon baya ba, na kwammace in mutu da ciwon sonka, akan in aure ka"! Da sauti mai karfi tayi maganar tare dakai hannu ta daki handrail.. duk abunda ke faru tsakanin su babu wanda ya sani "In kuwa har ka bari Chief yayi nasarar ruguza kurkukun addara batare da taimakonka ba, zan mallaka mashi kaina..." bata kare maganar ba sakamakon zazzafan marin daya kwasa mata wanda shi kanshi bada sanin shi ba, a karo na farko data fara jin tafin hannunsa akan fuskarta da sunan mari, wa'iyazubillah wani azababben radadi taji ya ratsa sassan jikin ta kamar an watsa mata wuta jirine Ya kwashe ta, ta tafi zata kife asa cikin zafin nama Ya taro ta da hannunshi ya dawo da ita kan kirjin shi, yayi hanzarin daukarta kan kafadarshi Ya nufi bedroom dinshi da ita gudun kada wani ya riskesu a halin da suke a ciki. Yana shiga akin Ya kwantar da kan gadon shi, kamar matatta, da alama suma tayi saboda azabar da taji. Hankalin shi idan yai dubu toh ya tashi, Jikinshi sai kerma yake kamar wanda sanyi Ya kama, zafin Kishi Yaja mishi bala'e.. Duk da sanyin A.c din dakin hakan bai hana gumi tsastsafo mashi kan fuskarshi ba, zukunnawa yayi daga bakin gadon yana kallon gefen fuskarta, shi kanshi Ya tsorata da ganin yadda fatar gurin tayi ja sosai, shatun fingers in shi ya fito ru u ru Yatsun hannayen shi Ya zuba ma Idanun shi Yana kallon su cike da danasanin marin da yayi mata, ya san yadda marin Evil giant yake da zafi, zata Iya kai Sati da radadin dafin marin a jikin ta. cike da takaici ya dinga bugun kanshi da hannayen shi kamar zai zauce saboda zafin abun da ya yi mata Tuni hawayen da suka taru cikin idanunshi suka fara Yar tseral kan kuncin shi, abu biyu ya ha e mashi ga zafin munanan kalaman data jefe shi da su ga takaicin marin da yayi mata. Cikin karyayyar murya ya furta"ba laifina bane, ke ce kika bata min rai, gashi kinja na mareki bada son raina ba" ya fa a tare da daura tafin hannunsa saitin inda Ya mare ta, dabara ce ta fado mashi da sauri ya saita fuskar shi saitin tata, sihiri gaskiyar mai shi, ruwan hawayensa dake iga kan fuskarta sune suka goge tabon marin da ya yi mata cikin kankanin lokaci fatar ta dawo fara sol kamar ta jinjira, numfashi Yaja tare da sauke ajiyar zuciya a hankali launin idanunsa suka dawo yadda suke. kallonta da yake yi ahaka yafi masa kwanciyar hankali akan Ya farfa o da ita saboda fargaban masifarta. Daga gefenta Ya raba jikin shi, Ya kwanta tare da lumshe idanun shi, bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na yau ba, tayaya zai iya shawo kan Unaisah ta fahimci abunda yake nufi"? Kwatsam yana a cikin mawuyacin halin nan ba zato ba tsammani ya tsinkayi Muryar Khala a cikin kunnanshi.. "Uhum Garkuwa Namu" A rude Ya mike zaune yana bin dakin da kallo, cikin sauri Ya share hawayen fuskarsa, jikinshi har 6ari yake garin zumudin ya sauko daga kan gadon, Hasken akin shi ne Ya dauke uff Duhu Ya mamaye ko'ina, bai nufi ko'ina ba sai gaban mirror Ya yaye madubin idanunshi su ka yi mashi tozali da tsohuwa Khala zaune kan armchair, Cikin shigarta ta gado fuskarta a yamutse ba annuri. Zama yayi