Sashe 181
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
addinin musulunci"? Shiekh imam ne ya tambaya yana kallon shi.. Gaba daya sun kagara da su ji me zai ce Sai da ya mula ya sha iska kafin ya firta"bani da ra'ayi," "Meyasa"? Shiru yayi bai tanka ma shi ba. Hakan ba karamin karya zuciyoyin su yayi ba.. "Inason Yin magana dakai, a akin ka" bai yi mashi musu ba, Ya mike sheikh Imam Yabi bayan shi suka nufi second floor har dakin danish bayan sun shiga Shiekh Imam Ya kulle Kofar. Gaba daya sun kagara da su fito, fatan su Allah yasa Ya kar6i musulunci. Kasa kasa da murya Taj yace ma Unaisah"kun ci abincin daren ku"? "Eh daddy," "Pls ki daina sanya damuwa aranki, banason ganin ki a rame haka babu walwala, in har saboda tafiyar da zamuyi ne addu'arki muke bukata ba damuwarki ba.." "Toh daddy, zan daina, amma pls ka fadamin date da zaku tafi na maka alkawarin bazan sanar da kowa ba" Aranshi ya ayyana ay ko da zan fada ma kowa Unaisah bazan fada maki ba, ni nasan me zai biyo baya in kikaji, rigima zaki sa sai mun tafi da ke .. "Daddy ka yi shiru" "Unaisah, Chief Yana kallon mu, kuma shi Ya hana asanar da kowa, kuma mun yi mashi al awarin zamu ruke amana, kinga bai kamata in zama mutun na farko da zanci amanar shi ba, amma ki ara hakuri zan nemi izni daga gurin shi In har Ya amince zan sanar da ke" yamutsa fuska tayi tamkar zata sanya kuka tace"ran nan ma haka ka ce min zaka yi mi shi magana akan in biku amma baka yi masa ba" Shiru yayi bai tanka mata ba, ta fahimci wayou ya ke yi mata gashi takasa tunkarar Chief din da maganar wani irin nauyinsa ta ke ji. Agogon Hannunsa ya duba karfe goma na dare, agowa yayi tare da kallon Chief, Wanda Hankalinsa ke akan Phone dinsa da yake daddanawa.. Har saida suka fara gajiya da jiran sheikah Imam, A kalla sun shafe mintuna talatin Cuf, Wasu daga cikin Prisoners har sun fara bacci. A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga sheikh Imam Ya fito daga dakin batare da Danish ba, tunkafin ya karaso su ka lura da yanayin damuwar dake akan fuskarshi, nan take suka fahimci ba ay nasara ba... Har ya zauna ba su daina kallon shi ba, yayi shiru babu walwala akan fuskarsa "Baba an dace kuwa"? Kallon chief yayi tare da girgiza mashi kai yace"ban ta6a yi ma wani an adam da'awa irin wadda nayi mashi ba, kuma da wuya inyi har in gama mutun baiji imani ya shige shi koda bai musuluntan ba, amma banaso hakan Ya dame ku, kowa ni dan adam da irin tashi Jarabawar, wani har ya mutu baiyi imani da Allah ba, amma fa kada ku yanke kauna da shi, idan Allah yaso shi da rahama koda da numfashi na karshe ne in Allah ya nufa sai kuga ya furta kalmatusshahada..." bai are maganar ba, Unaisah ta mike da gudu ta bar falon, gaba daya suka bita da kallo har ta 6ace ma ganin su. Suma sauran yan uwan nata, kuka suka kamayi, shiekh imam ne yayi masu nasiha mai tsuma zuciya harya samu ya shawo kan su, Kafin tafiyarshi, sai da Ya arfafa masu Chief gwiwa, Ya jima agidan har wuraren karfe sha daya kafin yayi masu sallama ya tafi. Bayan tafiyar shi, Taj Yace suje su kwanta, jikin kowan nan su asanyaye suka mike ko sallama ba su yi ma su ba, kowa ya nufi akin shi Ummi ma ta yi ma su sallama ta nufi nata akin. (After two days da zuwan Sheikh imam, Bayan kwana biyu) Yau tunda sanyin safiya, kiran Taj ya farkar da Ummi tana tsaka da yin baccin ta, bayan ta daga sun gaisa Yace Ta shirya su Unaisah, tare da ita kanta, yana son su kawo ziyara part dinsa gurin Danejo, Ummi taji dadi dama Ta gaji da zama guri daya tafi son tana an yawata. Batare da 6ata Lokaci ba, taje dakunansu ta tada su daga bacci ta isar masu da sakon Boss, duk da halin da damuwar da suke a ciki hakan bai hanasu jin dadin zasu je part din daddy taj ba, Unaisace kadai Hankalinta bai kwanta da zancen zuwansu part din daddynta, saboda ranta yana bata yau ne kwanan watan da zasu je kai farmaki, shiyasa akayi masu wayau don a kawar masu da tunanin su, aikuwa ko brush batayi ba, wankan ma ta kasa yi, A karkashin gado ta boye kanta duk don kada tabisu. "Sister! sis! Where are You, Mun fa shirya, ke kadai muke jira" muryoyin su Batool tajiyo a cikin kunnanta, shiru tayi bata amsa masu ba. Can tajiyo muryar Ummi tana fadin"Unaisah Ina kika shiga ne? Kun duba toilet inta kuwa"? Ta fada tana kokarin tura kofar toilet dinta, koda Ummi ta bu e kofar ta shiga ciki bata ga kowa ba, tayi mamakin ganin babu ita a ciki, rufe kofar tayi, tare da kallon su, sunyi tsaitsaye. "Aunty ummi ki kira daddyn nata, Muji idan taje can in" acewar Sajeed Waya ta zaro daga Cikin Yar purse inta, ta danna ma Taj kira almost 3 times tana kira baya shiga har ta gaji ta hakura da kiran nashi.. "Mu tafi, may be tana can din" fitowarsu keda wuya daga dakin sai ga big guy ya shigo part din su Kaitsaye idanun shi suka sauka akan Ummi, from head to toe Yabi ta da kallo, fitted gown ce a jikinta ta material launin ash colour kamar ajikinta aka dinka kayan, ta kashe daurin dankwalinta sai an gyalen data yarfa a kafadarta, ko makeup batayi ba amma tayi matukar jan hankalin shi. Gaba daya sunyi mamakin kallon da big guy keyi ma Auntyn ummin nasu, ita sam bata lura ba da fara'a tace"Gm Sir, ya gajiyar aiki? dakyar ya ha iye abunda ke ransa Yace"lafiyalou Ummi, Ina zuwa haka"? Ya tambaya kamar baisan da plan din su ba "Zamuje kai ziyara a Part din Daddyn Unaisah" murmushin gefen fuska Ya sakar ta, kafin Ya dubi prisoners. "Guys, Kunyi kyau, Muje na raka ku part din nasa" ya fada tare da nuna masu hanya, su ka yi gaba shi kuma Yajera da Ummi cikin nutsuwa suke yin tafiya. "Kinyi mini kyau, badan Ina busy ba, da na daukeki mun fita yawan bu e ido" "Banyi zaton kana Kula mata ba.." ta fada tare da kallon shi.. Murmushin gefen fuska yayi"nima fa banajin magana, tubabbe ne, daga baya na shiryu silar Owais.." "Allah sarki Chief, Mutumin kirki, har kasa na kara jin kaunar shi saboda shi din na dabanne samun irin shi da wahala" still fuskarshi da murmushi yace"That's why I'm proud of him..." "Kasan wani abu"? Girgiza mata kai yai saikin fa "najima ina yi maka kallon sani, hatta muryarka tayi min kama data wani mutumina Allah, kuma kun anyi kama da shi" "Zan iya sanin sunanshi"? "A'a, bana fa i, amma ka fadamin sunan Family dinka" Yar dariya yayi yana binta da wani shu'umin kallo, kamshin turarenta duk ya kashe mashi kuzarin shi musamam Yadda qugunta ke gogar nashi ba karamin tsuma shi take ba.. "Wayau zaki min Ummi, Ke kin ki fa amin sunan mutumin naki sai ni zan fada maki sunan family ina, bazai yiwuwa ba Allah" Murmushi tayi"na yarda kowa ya ruke nashi, amma kai ba hausa bane zalla ko? Cos kayi kama da ruwa biyu" aga mata gira yayi. "Meye Full name inka"? har ya bu e baki zaiyi magana Muryar Sarah Ta katse su"Aunty Ummi, ke muke jira fa" Gaba daya sun shagala sunata fira sam sun manta da su, har sun karasa bakin kofar part din... Karasowa sukayi, big guy ya kwankwasa kofar, almost 3 times kafin suka ji motsin bude kofar ta ciki Taj Ne Ya fito Jikin shi sanye da kakinsa Yana ganinsu ya saki fuskar shi da fara'a suka gaisa da juna cikin girmamawa. "Bismillah Ku shiga, madam Tana a ciki tana jiran ku..." murmushi suka saki gaba dayan su, har sun fara shiga ciki Taj ya lura babu Angel acikin su.. Da sauri Yace"Ina ita Unaisah din"? Ummi tace"wlh bamu ganta ba, mun duba ko'ina har cikin toilet dinsu, mun yi zaton ta riga mu karasowa ne" Big guy yace"ni banma lura babu ita a cikin su ba, sai yanzu da kayi maganar nan.." fuskar Taj A yamutse Yace"ku shiga daga ciki, Bari naje na dubota" ya fada tare da kallon Big guy"muje" sai da ya fara kallon ummi Yai mata waving kafin Yabi bayan Taj, suna fitowa daga falon,yayi locking door din dama da biyu suka turo su nan. Bin falon su ka yi da kallo, jin shiru matar gidan bata fito ba, ummi tace mu zauna mu jira ta.." da sauri kowannansu ya samu guri kan Sofas suka zauna. Badajimawa ba, sautin takalamanta Ya karade kunnuwansu, kusan atare suka kalleta yayin da take saukowa down, ta dauki wankan abaya ba a, tayi rolling akanta. jinjina kai ummi tayi aranta ta furta masha Allah. Sallama tayi masu, kamar tana jin shakkarsu, har yanzu bata saba da mutane ba.. A wayance Ummi ta mike tare da ruko hannayen Danejo Acikin nata, ta sakar mata murmushi"sannu madam, fatan mun same ku lafiya.." sai faman rarraba idanu takeyi akansu Rubina Dakyar ta firta"lafiyalou" Ummi tace"kamar baki gane su wanene ba, Ko dai Mijin naki bai fada maki zuwan mu bane" sai lokaci tayi murmushi"wlh ya fadamin, na shafa'a ne, da yake banganku tare da artawa ba shiyasa na an ru e amma yanzu nagane ku" Hugging inta Ummi tayi, Kafin suka zauna kusa da juna. Da sauri Prisoners suka gaishe da ita. Da fara'a tace"tabarakallahu ahsanul khalikin, Kune Yan uwan Angel in? Atare suka amsa mata da eh "Masha Allah Jinsin kyawawa Naji dadin ha uwa daku, amma Ina Unaisah in take"? Ummi tace"bata karasa shiryawa bane, shiyasa muka tafo, amma dadynta Yaje ya taho da ita" "Ke ce mommynsu ne"? Yar dariya ummi tayi"kina nufin wadda ta haife su? Daga mata kai tay, dariya ta kumayi kafin tace"kin iya zolaya, ni ina zan iya haifan wadannan har su goma sha, ko nayi maki kama da matar aure ne"? Ta tambaya tana kallonta, murmushi Danejo