← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 140 OF 247

Sashe 140

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

farat aya ya gane babu lafiya, ciwon nata ma ara ha66aka yakeyi babu alamun sau i, lamarin ya aure mashi kai, a kalla ya shafe mintuna yana kallonta yana nazari akan yanayin ta. Hajjaty dake kallon fuskarshi sheikh imam tuni tasha jinin jikinta ganin yanayin shi ba walwala. mikewa yayi tare da kallon hajjaty"anya kuwa kinbi sharuddan bata maganin dana fada maki dai dai? Ko dai kinyi kuskure ne" arude ta girgiza kai"wallahi ban ta6a kuskureba, ina kokarin kiyayewa kamar yadda na fada maka..." bayani tayi mashi yadda take bata maganin, dalla dalla kamar yanda ya fada mata, tabbas ya yarda da maganarta, abunda bai gane ba ta ina matsalar take! Shiru yayi jim yana kara bin marwa da kallo Muryar hajjaty na rawa tace"malam akwai matsala ne"? Ya fahimci hajjaty bata lura da habbakuwar ciwon marwa ba .. Numsafawa yayi kafin ya furta"ina maganin nata yake"? Jikinta na 6ari tace"ga su can akan mirror, bari in dauko maka" dakatar da ita yayi da hannu tsayawa tayi, tana faman zare idanunta, juyar da kai sheikah imam yayi tare da kallon gaban mirror din marwa A hankali Ya nufi gaban madubin Ya tsaya tare da kallon robobin maganin, aya ya auko ya bu e ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi. Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya ha e rai sosai, aya bayan aya ya bu e murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta "Ya akai haka"? Ya fa a yana dubanta Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" ha e rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya fa i ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata. Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba aya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da an aiken shi ya kawo mata maganin tabbas da ta bu e tana dubawa taga launin ruwan ya banbanta. Wahalallan yawu ta ha iya cikin rawar murya ta furta"wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa bani na canza ruwan maganin ba! Wlh bani bace, bansan wanene ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." gaba aya tabi ta ru e wata irin zufar tashin hankali ce ta wanke fuskarta, gani take kamar shiekh imam yana zargin ta. Girgiza kai shiekh imam yayi"kin bani mamaki! Meyasa zakiyi mata haka? Ko dan kin gaji da jinyarta ne? Ni fa ban tursasa maki ba, aikin lada ne tun lokacin dana bukaci wanda zai kula da ita da kin fadamin bakiso ay da ba haka ba" Runtse idanunta tayi, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta, kalaman sheikh imam sunyi mata tsauri, taji acin su azuciyarta. "ka yarda dani, wlh ni ba muguwa bace, bazan iya cutar da marwa ba, ina da zuciyar imani, ko kiyashi bazan iya cutarwa ba, balle an adam, wlh bani na canza ruwan maganin ba, na shiga ukuna" ta fada tare da dafe goshinta da hannu daya. tunda sheikh imam yaga yadda ta rikice nan take ya fahimci ba ita bace, dama da biyu ya furta "Ya Isa haka, Na yarda bake bace, amma wanene toh? Dole akwai yarda akai aka canza ruwan, kuma koma wanene mutunne, lokacin da dan aikena ya kawo maki maganin a ina kika ajiye shi"? Waro ido waje tayi murya na rawa tace"a dakina" Sheikh imam yace"hakan na nufin anan aka canza ruwan maganin kenan? To wanene? Akwai wanda ke shiga dakin ki ne"? Shiru tayi jim gabanta na faduwa da matsanancin karfi, hankalinta ya tashi, kwata kwata bata kawo ma ranta pravin ba, tasan bazai ta6a yi mata hakan ba, me ma zai kaishi canza maganin marwa? Har abada ba za ta bari wani yasan akwai alaka tsakaninta da pravin ba. Tayi zurfi cikin tunaninta muryar sheikh imam ta katse ta"kinyi shiru baki bani amsa ba? Wakike tunanin ya canza ruwan maganin? In har baki fadamin gaskiya ba, zanje in fada ma baba obie abunda ke faruwa" a firgice ta zare mashi dara daran idanunta, wani irin faduwar gaba ta ji daram kamar ana mata lugude a kirjin ta, arude ta girgiza mashi kai"kayi hakuri sheikh, wlh bani da masaniya, amma nayi maka alkawarin zan binciko koma wanene" jinjina kanshi yayi"kinyi alkawari? aga mashi kai tay"in har kika sa6a hmm kinsan sauran, keda baba obie ne" matse kwalla tayi, cikin sanyin murya tace"in sha Allah ba zan saba ba, amma sheikh meyasa kake tunanin wani ne ya canza ruwan? Baka tunanin bakaken aljanun jikinta ne sukayi mata hakan don kada ta samu sauki? In ba haka ba taya za'ay wani ya canza ruwan? Akan wani dalili"? Ta fa a tana kallon fuskar shi. Murmushi shiekh imam yayi tare da dan girgiza kanshi kafin yace"ba al'janu bane suka canza ruwan, mutunne, dole akwai yadda akayi, ki zauna kiyi tunani dakyau..." Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh, "Sannan sheikh, akwai wani abu da marwa takeyi min, ni dai nagaza fahimta, duk in na shugo dakin zan bata magani, sai ta dinga goga hannunta a kasa, taita yunkurin yi min magana idan taga na kasa gane me take nufi saita kifa kanta jikin pillow...." bata are maganar ba sautin tarin marwa ya katse hanzarin su, sam sun manta da ita dakin, maganganunsu su ne suka farkar da ita Atare suka kalle ta, tana a zaune kan mattress din, ta jingina kanta jikin bango, idanunta suna rufe ga siraran hawaye dake zarya kan kuncinta, gwanin ban tausayi "Marwa"! Jin muryar sheikh iman yasa tay saurin bude idanunta. tana ganin shi ta fara kokarin yin magana donta gaishe da shi sai dai takasa. "Basai kinyi min magana ba, na fahimce ki," ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun ka a jawur da su Zukunnawa yai agaban katifar yana dubanta yace"Hajjaty ta fa a min da akwai wani abu da kike yi mata nuni da hannu ta kasa gane menene ko zaki nuna min in gani"? da sauri ta aga mashi kai, jikinta na kerma ta matso bakin kafitar, ta daura hannunta akan floor ta dinga goga su tana kallon sheikh imam cike da sa ran zai fahimce ta, ita dai hajjaty sai faman zare ido takeyi fatanta Allah yasa shikeh imam ya gane menene marwa ke son fada mata abun yana damunta. A kalla marwa ta kwatanta mashi yafi sau biyar ganin kamar baigane ba yasa ta fara matsar kwalla. zurfin tunani ya shiga can yace"wani yana zuwa dakin nan? Girgiza mashi kai tay alamar a'a" "Ko ana tsoratar dake ne"? Still ta girgiza mashi kai, shiru yayi yana kara hasasowa can yakuma cewa"kodai kina son kiyi rubutu ne.. "Ga mamakin sa sai yaga ta daga mashi kai alamar eh hada an murmushin ta. Hajjaty tayi mamakin jin hakan sosai, da sauri ta nufi drawer din marwa ta fara neman littafi dakyar ta zakulo wata jotter tare da pen, ta dawo bakin katifar ta bu e mata jotter din ta ajiye agabanta, ta zira mata pen din dakyar ta matse biron da hannayenta, ta soma kokarin gogawa paper din, lamarin ya daure masu kai, daga hajjaty har sheikh imam din, sun kagara da suga me ta ke son rubutawa. Duk yadda taso ta rubuta sunan wanda yayi mata aika aikar takasa, biron yaki zama a hannunta duk ta cakalkala paper din akarshe ma ta yayyage, jefar da pen din tayi kasa ta fashe da kuka tare da kifa kanta jikin pillow, gaba daya jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu ta raunata da tausayinta. Cikin sanyin murya shiekh imam ya ce"kiyi hakuri, na fahimce ki, akwai wani abu da kike son fada mana, amma kin kasa, abunda nakeso dake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah nan badajimawa ba ciwonki zai zama labari, zamu tayaki da addu'a sannan zan canza maki wasu magungunan. tun tana shesshekar kuka hartayi shiru ta hakura musamman da taji maganar sheikh imam hankalinta ya an kwanta, har taji zata iya hakura har zuwa time da zataji sauki tunda bata da mafita. Mikewa yayi tare da kallon hajjaty, "ki zubda ruwan maganin dake a cikin robobin, zan kawo maki wani amma fa dole kiyi takatsantsan, kada ki kuskura ki bari wani yasan inda kika boye su ko kuma wani yasan na canza mata maganin nan daga ni sake wannan maganar, In kuwa kikai gangancin da wani ya sani har aka sake samun matsala to ki kuka da kanki domun kuwa bazan kyale ki ba...." a kausashe yayi mata maganar saboda ta auki maganar shi serious, baiwar Allah duk tabi ta rude jikinta har kerma yakeyi sai taji dama bata kar6i aikin ba saboda bata son abunda zai hana ta kwanciyar hankali. Sallama shiekh imam yayi mata, ya fuce yabarta da jimami ________________________ Zaune yake a gefen gadon shi, jikinshi sanye da voile fari, tafukan hannayenshi tallabe da qur'ni, Ya tattara dukkan nutsuwarsa akan kira'ar da yake yi, acan kasan zuciyar shi damuwa ce cunkushe baya jin dadin zuciyarshi saboda halin da Benazir take a ciki ya damu ita, yana matukar jin tausayin ta. Yana tsaka da yin kira'ar, sautin knocking Ya katse shi aga murya yayi"wanene"? "Ya shureim ni ce, Ina son yin magana dakai" jin muryar Benazir yasa shi saurin mi ewa ya ajiye kur'anin Ya nufi kofar ya bu e mata, A hankali ta shigo ciki, jikinta sanye da abaya, tayi rolling veil akanta, hannun ta ru e da yar purse dinta, ga wasu highhill da ta saka a kafarta, aru e yake kallon ta ganin hada make up akan fuskarta. "Ina kwana ya shureim ka tashi lafiya..." "Lafiyalou sister, Ya
Chapter 140 · 0% Book details