← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 206 OF 247

Sashe 206

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

da wasu ke kyamatata, da zuciya daya kikai jinyata, na dade banga mace mai kyakkyawar zuciya irinki ba, kina da hakuri ga son taimako...." kasa karasa maganar tay saboda kukan daya kwace mata. Zafafan hawayene suka wanke fuskar hajjaty tabbas hankalinta ya tashi da jin abun da hajiya saratu tasa ay mata ashe tsanar da tay mata har takai ta sa adinga bibiyarta? Laifin me tay mata? Numfasawa tay kafin ta furta"marwa ki daina kuka, wlh na yafe maki, har ita hajiya saratun, Allah ya yafe mana baki daya, kuma naji dadi da kika gane kuskurenki" Bayan Marwa ta tsagaitawa da yin kukan tace"bawai iya wannan ne abun da na kira in fada maki ba..." A kagare hajjaty tace Ina sauraron ki marwa. "Bansan ya zaki auki abun ba, amma kiyi hakuri ban fada maki don in tada maki hankali ba face sai don In ceto rayuwarki saboda Kyautatamin da kika yi, Da farko nayi danasanin aikin da hajiya saratu ta sakani amma daga baya Naji dadi saboda silar aikin Allah ya nuna min wani mugun abu dake rayuwa agidan nan" Yawu hajjaty ta hadiya kutt zuciyarta cike fal da fargaba ta furta"marwa menene? Fada min dan Allah! Numfasawa marwa tay kafin ta daura da cewa"Aunty PRAVIN shine silar ciwo na, Saboda Ya gano nice nake yi maku leken asiri shine Ya daura mini cutar kuturta Ya toshe min bakina" bata kare maganar ba sakamakon tsawar da hajjaty ta daka mata"Ya isa marwa! Bana son karya ki rasa wa zaki wa kazafi sai pravin? Taya pravin zai iya daura maki ciwo? Sai kace dai Aljani"! "Saboda shi din mugun matsafine, kece bakisan wanene Pravin ba, tun farkon fara aikina gidan nasan munanan dabi'unsa, Ya saba Bibiyar mu yana laluban jikinmu dayi mana barazana akan in muka tona masa asiri zaisa a koremu daga aiki....." wani irin faduwar gaba hajjaty taji daram dararam kamar ana mata luguden ta6are a kirjinta, Jikinta sai kerma yake kaf kaf idanunta azazzare cike da tashin hankali wlh ji take kamar a farmaki sam takasa yarda da maganar marwa taya ma wai pravin dinta zay aikata hakan? "Naji kin shiru, dama nasan ba lallai ki fahimce ni ba, amma ki sani wlh rantsuwar dan musulmi ba kazafi nayi masa ba, Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan" Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..." Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor. fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka ka a jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravin Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane, kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..." _________________________________ *Chief Owais Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su. Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana aya daga cikin Elders na gidan kurkukun addara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba. Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya na e kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha .. Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin. "Owais ne" "Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi. baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha. yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit... "Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu. A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa. "Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji dadin maganarshi. Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa. Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya le o mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan" "Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni" Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata" dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi. "Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport, wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani" dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi. Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ara dankon zumunci atsakaninmu da shi" kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai
Chapter 206 · 0% Book details