← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 242 OF 247

Sashe 242

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

Bai arasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma. Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate insu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!' Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzu a za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta. Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike ta ama ne?" Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!" Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hanka o mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..." Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ru u yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka ka a jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?" "Ba zaku auki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da ba en aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..." Pravin ne Ya fa a Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru. Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana arasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta dam i mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya za inta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.." Balbaleta da fa a Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba. Sai da suka gama harzu a kowa zuciyarshi ta zo a wuya. Pravin yana arin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya fa asa ta bi tasa afarta ta take shi ya faffashe. agowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta aga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba aya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya arsu acikin zukatansu, Sun ru e da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita. Sai lokacin ta yi arfin halin bu e baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!" Ta fa a tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya mi e tsaye a ki ime yana zazzare idanunsa! lokaci aya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matu ar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ru e shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa.. Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike ta ama ne, wace ce ke wai..."! Bata are maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ru e ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafa unta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana arin gano wacece ita.. Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!" Ta fa a tana arin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da walla. Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya auke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku aryar na mutu bayan ina a raye...." Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da walwarsu ke arin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki. Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya ji e sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi. Pretending ya yi duk don ya ara dagula masu lissafin walwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!" Ya fa a a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce. "Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..." Ta fa a tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ru ani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu aya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin wayar idanun ta. In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya fa a yana girgiza kansa. Bai are maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ru ani! gaba daya mun ru e, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya fa a fuskarsa sharkaf da hawaye. Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi. "Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku aryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..." La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! arya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya fa a yana nunata da yatsansa dake kerma.. "Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ru iya zaku tabbatar da abunda nake fa a maku..." Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ululun bakin ciki da ya tokare ma ogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shai ani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasi i ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...." bata are maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ru ar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu auka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu. Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa. ar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana fa in, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son ha a uba da yayansa, ni nasan ma iya ne suka turo ki don ki yi mini azafi..." Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata auki. "A'uzu billahi minasshai anir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma ba ar munahika" Ya fa a yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu. Tana kuka ha i da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana mi a masu hannu, "Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni ka ai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta fa a idanunta cike tab da walla, tana ta arin wace hannunta daga mugun ru on da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita. Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya aura a saman kanshi alamar ya shiga uku, irjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya ha a uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfa iya ta kama. Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana arasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife asa kafin ya ago Sharafudeen ya dam o hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon. Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging in ta akan
Chapter 242 · 0% Book details