← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 15 OF 247

Sashe 15

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

tana faman sakin nishi tace"Zaka ci ubanka, Kai ne 6arawon dake cinye mana sauran da muka rage a kitchen ko"? Ta fa a tana le en idanun 6eran Yayi zuzuru dashi. "Ba zaka yi magana ba? Baka da gaskiya bakin munafuki, kai ne kake gwigwiyar mana bready, Bari na kai ka Gaban Al ali Ya salsabeel Ya kashe min kai har lahira" Ta fa a tare da fitowa da gudu ta nufi bedroom din salsabeel, Har Ya koma bacci, Yajiyo muryar khadeeja tana fadin"Ya salsabeel Ka bu e min kofa na kama 6arawon dake cinye mana sauran abincin mu, gashi nan a hannuna, Ya salsabeel ka bu e zai gudu' Afirgice Ya farka har yana tuntube garin sauri, koda Ya bu ofar Mi a mashi 6eran tayi "Gashi ka kashe shi ko ka cire mashi hannayensa" Fuskarshi a yamutse ya kalli 6eran da idanunsa masu dauke da bacci, sun ka a jawur da su, yayi mamakin da har ta iya kamo 6era, tun da suka fara zama gidan bai ta6a ganin gifcin 6era ba sai yau. Muryarshi adisashe yace"khadeeja ba zaki barni inyi bacci ba? Ke baki runtsa ba nima kuma kin hana in runtsa, Meke damun ki ne"? Ta6e mashi lips dinta tayi alamar zata fashe mashi da kuka Da sauri yace"ya isa ni bance kimin kuka ba, Yanzu fada min ya kikeso ayi da 6eran nan da kika kama" "Ka cire mashi hannuwa" gyada kai yayi tare da sanya hannu ya kar6i 6eran"ki jira ni yanzu zan dawo amsa mashi tayi da toh, fita yai daga dakin tana atsaye tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannunsa babu 6eran "Yana ina"? "Na cire mashi hannuwa na yar" murmushi tasaki"mun hutu da masifa ko"? aga mata gira yai alamar eh "Muje na rakaki daki kiyi bacci" ma e mashi kafada tayi"Ni yunwa nake ji, kaje kitchen ka dafa min abinci" Wahalallan kallo yabita dashi gaba aya ta takurasa "Shikenan muje" Ya fada tare da yin gaba tabi bayan shi suka shiga falo, ta zauna saman sofa. Kitchen Ya shiga bawan Allah ga gajiyar bacci A haka Ya dafa mata indomie, Ya ha o mata da water bottle, Ya shigo Da plate din Ya mi a mata, gefen ta ya zauna don yasan koya koma daki indai batayi bacci ba to shima bazai runtsa ba. Yana kallonta Har ta cinye taliyar ta kora da ruwa, kwanciya tayi saman sofa din ta daura kafafuwanta saman laps dinshi bai tanka mata ba, yasan rigima take nema, Cikin sa'a bacci yai awon gaba da ita, A hankali Ya zame afafuwanta ya mi e tare da aukarta ya nufi upstairs da ita, a kan gado ya kwantar da ita, yabi da bargo ya lullu6e mata jikinta, kafin ya fito ya datse kofar dakin nata, cikin sauri ya nufi dakinsa don ya kwanta ya karasa baccin dabai isheshi ba, bayan shigarshi daki har ya kwanta ya soma tunanin ko me ya hana jazz zuwa? Tun safe yake jaraba kiran layin shi baya picking, har ta 6angaren danish ba a kira shi ba wunin yau, fatan shi Allah yasa lafiya da wannan tunanin bacci 6arawo ya auke shi. BENAZIR Kwance take a saman darduma, tun bayan data kammala sallar Isha bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, yayin da zeenatu take a can saman gado tana bacci. Tana a nanna e cikin dogon hijab dinta, tayi nisa acikin baccin ta, Ba zato ba tsammani hasken fitilar bedroom inta ya auke uff, wani iko na Allah ba wutar gidan bace ta samu matsala, akinta ne kadai hasken ya auke, abun ka game bacci sam bata ji alamun hasken dakin ta ya auke ba. Kwatsam! taji an dam i wuyanta, tsabar zafin sha ar da akayi mata ne yasa ta ware idanunta waje, bata iya ganin komai sai duhu ba i wulik a idanunta Wani irin mahaukacin bugun fargaba zuciyarta keyi mata, Hankalinta a matu ar tashe ta soma kokarin kwace wuyanta daga hannun mutumin daya sha eta, wuyanta tuni ya soma yi mata zogin azaba, zufa ta ko'ina ta wanke fuskarta, duk yadda benazir taso ta kwace kanta sai dai kash takasa, ga zeenatu kwance saman gado sai dai babu halin da zata iya bu e baki ta nemi agajin ta, koma wanene yayi mata muguwar sha ar da ko yatsanta takasa agawa, bakinta tamkar an aure mata shi takasa bu e shi, hakan yasa tafara kukan zuci tana ambaton sunan Daddy, mommy, yaya shurem, Zeenatu, A karshe ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un tacigaba da anbatonta acikin zuciyarta. Tana acikin wannan mawuyacin Halin har tafara fidda rai da rayuwa kwatsam wayar zeenatu da ta ajiye kan gado ta soma ringing, taken karatun al' ur'ani mai girma ne, Kamar Walkiya taji alamun an sakar mata wuyanta, kuma nan take hasken akinta ya kawo, a gigice ta zabura ta mi e zaune tana faman zazzare idanunta, bin ko'ina na dakin tayi da kallo bata ga kowa ba, Lamarin ya daure mata kai, tagaza gane meke shirin faruwa da ita? Don wannan yafi karfin a kirashi da mafarki, tabbas akwai me son rabata da rayuwarta, lokaci aya ta fashe da matsanancin kuka tamkar aramar yarinya ita kadai tasan rada in da wuyan ta ke yi mata, zeenatu dake ta sharar baccin ta tuni ta soma mutsu mutsun farkawa saboda sautin kukan benazir daya fara addabar kunnuwanta, da sauri benazir ta tsagaita da yin kukan gudun kada zeenatu ta farka taga halin da take a ciki, cikin juriya ta mi e ta zame hijab din jikinta, ta jefar da shi gefen gado, gaban madubi taje ta tsaya tana kallon wuyanta yayi jawur da shi hada sawun yatsun hannuwan mutun rudu rudu.. Hakika Ta gigita ta kuma tsorata a yanzu ta ara tabbatarwa kanta cewa akwai me son ganin bayan ta? Wanene? Laifin me ta aikata da har ake son kashe ta? Zuciyarta ce ta raya mata cewa zai iya yiwuwa jinnu ne, tafi yarda da abun da zuciyan nata ta raya mata saboda babu wanda take zargin zai iya yi mata haka acikin mutanan da take rayuwa da su,ta dai yanke shawarar zata sanarwa yaya shureim ko dan su nemi mafita a tare. Miryarta na rawa ta furta"Ya Allah ban cutar da kowa ba, Kada ka bada damar da wani zai cutar dani" ta jima atsaye gaban mirror, zuciyarta cike da rudani, ta nufi toilet, tsawon mintuna kafin ta fito jikinta da alamun lemar ruwan da ta watsa ma kanta. Tunawa da kiran wayar da akai mata ne yasa ta nufi bakin gado ta auko phone din ta soma daddanawa call logs ta shiga nan take taga missed call na bakuwar number din nan Sai da ta fara kallon agogo, karfe wani abu na dare kafin ta danna call tana faman zazzare idanunta, jikinta nata kerma kamar wadda aka kada ma mazari Adai dai wannan lokacin Unaisah tana a zaune kan darduma ta zumbula hijabi a jikinta ta aga hannayenta sama fuskarta sharkaf da hawaye bakomai take yi ba face yima danish addu'ar samun lafiya, Batul tana a kwance gefen ta, tun bayan da boss ya tashe su domin yin nafilfilin da za su yi kowannansu bai koma bacci ba, duk suna a dakunansu suna yin sallah, ita dama batul bata da jumurin yin sallah duka raka'a biyu ta samu tayi adaddafe kafin bacci yai awon gaba da ita, shigowar kiran wayar ta ne yasa takai hannu ta dauke ta , a inda ta ajiye ta gefen prayer mat din da suka akai Ko da tayi tozali da layin da take ta dannawa kira taga da shi aka kirata Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin yin picking din kiran, hadi da kara wayar a kunnanta. Tamkar kurame sunyi shiru suna sauraran sautin fitar numfashin juna. Jira take taji wanene mamallakin layin nan daya kira, Haka zalika itama benazir jira take tafara jin wanda ya aga kiran yayi mata magana. Jin shirun yayi yawane yasa unaisah tace"Assalamu Alaikum" sautin dadda an muryarta ne ya daki kunnan Benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin fa uwar gaba ba. Muryarta babu nutsuwa ta amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salam, barka da dare, dan Allah zan iya sanin dawa nake magana" ta fada cikin agara. Shiru Unaisah tayi tana tunanin wacece wannan matar mai muryar an gayu? Daga ji dai wayayyiya ce. Jin shiru ba'a ara magana ba yasa banezir furta"nayi magana anyi shiru b'a bani amsa ba, in ansan baza'a tanka min ba meyasa za'a takurani da kira da tsakar dare"? Har zata katse kiran Unaisah tayi saurin cewa"Aunty kiyi ha uri, bakisan wacece ni ba, nima bansan ki ba" Ajiyar zuciya Benezir ta sauke kafin tace"okey, amma meyasa kika kira layina bayan baki sanni ba"! "Nayi kuskurene wurin rubuta number din da zan kira" "Okey" shiru su ka yi, babu mai magana na tsawon mintuna kafin benazir tayi karfin hali cewa"meye sunan ki? Shekarun ki nawa"? ta tambaya ne jin muryar kamar ta aramar yarinya "sunana Unaisah, shekarata goma sha shida, ke fa"? Murmushine ya bayyana akan fuskar benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin farin ciki ba. "Sunana Aunty pretty, Amma fa ni ba yarinya bace, na girme ki, Shekarata talatin da wani abu" Murmushi unaisah tayi ita kanta dadi take ji, duk da halin damuwar da take aciki silar kiran nan ya haifar mata da kwanciyar hankali. "Kiyi hakuri na kiraki bisa kuskure, sannan na katse maki baccin ki" "Kada ki damu, Naji dadin haduwa dake" Shiru sukayi Kamar karsu Kashe kiran haka suke ji. "Baki so na sake kiranki"? Unaisah ce ta jefa mata tambayar . Murmushi benazir tayi don ta fahinci yarinyar batason su daina magana. "Ina so mana, tun da naji muryarki naji kin kwanta min araina, da ace babba ce ke da mun kulla kawance sai dai kin min anta" Cike da zumu i Unaisah tace"zan dinga kiranki muna gaisawa a matsayin aunty na, Idan kuma kina da iya kamar ni, ko anwa to ki hadani da ita sai mu dinga zumunci" "In sha Allah, yanzu ki kwanta ki yi bacci kada mommyn ki ta kama ki kina waya da dare, gobe zan kiraki mu arasa gaisawa, Yanzu kinga dare yayi," Kamar karsu rabu, Haka sukayi sallama da junansu, fuskar kowannansu dauke da
Chapter 15 · 0% Book details