← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 185 OF 247

Sashe 185

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Ya i a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_ ya fa a babu wasa akan fuskar shi, harya bu e baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar aga mashi hannu"na gama magana Owais," ya fa a tare Ya duba agogon hannunsa "I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce. Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu addamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karan Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi. Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba. Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace. Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci aya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint in daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking inta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana. Gwiwowin afafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta ebe shi gaba aya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi. Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking. "My baby boy, how are you"? Kokari yake ya bu e labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy." yana fa an hakan wayar ta sulbe daga hannun shi. Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne? Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ara sanin inda kan shi Ya ke ba.. (TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA __________________________________ Yayin Da Chief Owais ke a gar ame Cikin akin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa arfe biyar na maraice dai dai ba ari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbu e Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan ya i sun shirya tsaf. Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform. Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a al awari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a auki abun da mahimmanci ba ne. Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka aga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu" ya fa a idanun shi akan screen in wayar shi dake ru e a hannun shi.. Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"? "Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..." Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa" "Har layin daddyn nasa na kira baya shiga" "To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta aga" "Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number.. e sakon yayi tare da karantawa _Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_ (Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta maya an, Na soke kai farmakin) Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun ka a jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa. jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin Bu e kofar main Falon, zumbur Ya mi e Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu... aya bayan aya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna.. Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"? Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi "Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai aci Ya ha iya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira" Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba. "Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon.. Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi" "Na kira layin shi baya shiga" "Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy. Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi. kallon big guy yayi "Har yanzu baka same shi ba"? Jinjina mashi kai yai alamar eh.. Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki" "Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita" ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna. ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba. "chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai a an bace Yai maganar. Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su" "Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka aga kaji me zaice maka"! Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira" yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama. Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi "Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau" wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau" Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi ayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya wara muje villa din.." Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci. gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwa awa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su bu e masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama. wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke. "Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar
Chapter 185 · 0% Book details