← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 201 OF 247

Sashe 201

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu. "Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"? Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani" yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki. mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta. "Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba... Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."? Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo... "Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi addara..." wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada. ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya. hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye. Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"? "Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar" jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.." ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin. Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su. saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"! "What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya an lafa, cikin sanyin murya ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.." yana fa an hakan Ya mi e cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa. Yana shiga Ya fa a kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Ya in Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan. abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya dam a mashi saboda ya cancan ta. A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya an numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa. Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa.. _______________________________ "Dan Allah ku fa a mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya... Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba" A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba" Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi asa. mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne" gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta fa a tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne" "Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu" Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka ka a jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta fa a kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi. Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta .. _"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_ _"Abu aya da nakeso Kiyi min al awari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_ "Meyasa zaka yi min haka? Ta fada
Chapter 201 · 0% Book details