← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 120 OF 247

Sashe 120

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai aya ne.... tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano, Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu an banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba.... Su Hajjaty suna a zaune bayin Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka mi e suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci aya daga cikin su ya fara bayani, "Duk da irin arin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana an girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya aura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ru e Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ru e jin bayanan Docs. "Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana aya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai aya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace arara akan fuskokinsu.. "Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar walla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba aya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare aya ba tare da dalili ba..... "Dr ba yadda za'ay ku bu e mata bakin ta? Baba obie ya fa a yana kallon docs Girgiza kai aya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ru e ga tashin hankali...... Dafa kafa ar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sau i, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar, numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan aya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin bu atar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata arin ruwa da wasu allurai da zasu ara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji da in hakan, Baba Obie ya ro esu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi arin hakan. Su Hajjaty sunso su ara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi. Suna a kan hanyarsu ta komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam in ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, an hanjinshi suka motsa, wata irin ki ima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....! _______________________________ A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba. Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya.. yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai fa o mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ru o hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna "In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a" Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da aukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake! kallon zarah tayi"na kira baya shiga!" Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari an anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta "Anila ya kamata ki kira mahboob ki tuna mashi kar ya manta yaje da wuri ya dauko baby junaid, kinsan bayasan jira muma yanzu zamu tashi mu tafi yamma tayi"dariya sukayi su duka ummi tace"gaskia kam" tashi Anila tayi ta koma gefe aya ta kira layin mahboob yana auka tace" please karka manta kaje ka dauko baby junaid da wuri... Katse ta yai da cewa "ohhh Aunty Aneelah saikace karatu kusan kullum sai an tunamin inje dauko sa? to ki kwantar da hankalinki baby junaid tun arfe 2 yana a gida, yau da wuri aka tado su, saboda za'ayi wani taro a school dinsu, nima abokina ne dake koyarwa a school din ya kira ya fada min an tada su shine naje na dauko shi, halan bakuyi waya da Ana bane"? Wani irin bugu zuciyar Anila tayi rass! Taji gabanta ya fadi zuciyarta ajagule ta furta"wai kana nufin tun karfe biyu junaid yana agida"? "Kwarai kuwa, naga kamar kin daga hankalin ki, idan ma don saboda shine kada ki damu kanki yana atare da Ana ita na damka ma amanar shi" Still hankalin ta bai kwanta ba tace"mahboob na kira layin Ana a kashe, pls ko zaka duba min su"? voice dinta kamar zatayi kuka ga wani faduwa da gabanta keyi "ki sake kira kiji ni yanzu bana agidan na tafi kallon match" sallama sukayi ta kashe wayar hannunta har kyarma yake wurin kiran layin Ana still dai a switch off, cikin sauri ta koma falo ta gayama su ummi yadda tayi da mahboob mikewa mami tayi tare da kallon su uncle abdallah "to mufa baki zasuyi halinsu" ta fada tare da yar dariya, hajiya adama tace"wlh kamar ku kwana banso ku tafi Allah, kun ebemin kewa yau, Anya bazan biku ba" da zolaya uncle dan iya yace"shi kuma abdallan ina zamu kai shi? aikuwa su duka suka sa dariya, Aneelarh kamar jira take ta yafa mayafinta zarah ma haka gaba aya suka fito compound din gidan inda sukayi parking car dinsu... "Allah ya kiyaye hanya, mungode sosai, in sha Allah zanzo ganin jikana, agaida min shi..." Uncle abdalla yayi masu sallama akan idon su motocin suka fuce daga gidan hajiya adama hada kwallarta saboda bataji dadin tafiyar su ba, ruke hannunta uncle Abdalla yayi a
Chapter 120 · 0% Book details