Sashe 66
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
damu Ya muka are inaga idan baki nan? Duk wani mai nufin mu da sharri zaiji dadin cutar da rayuwarmu, bayan haka mommy tsawon shekara nawa kuna atare da daddy, auren soyayya kukayi kun tara zuri"a da dadi da ba da da i kunyi hakuri kun jure zama da juna sai akan wannan dalilin zaki kashe auranki? Mu kanmu bazamu ji dadi ba dan Allah ki tausaya mana mommy ku dubi girman Allah ki fasa tafiyar nan ko dan saboda mu" benazir ce tayi maganar tana duban fuskar mami kamar zata sanya mata kuka. Zancen zuci ta soma yi _wannan hanyar dana aukarwa kaina ba me 6ullewa ba ce, wara in tsaya in watar mana ancin mu, dole Inyi fa a ko da kuwa zan rasa raina ne saina shiga tsakanin mu da shi_ Ba zato ba tsammani suka ga ta bu e motar, wani irin farin ciki ne Ya lullu6e su, da sauri benazir ta fito shima shureim Ya fito suka dauko trolley dinsu dake a boot suka bi bayanta. Kamar yadda suka bar su hajiya sarah tsaye a falon haka suka taras da su, sunyi mamakin dawowar Hajiya layla, ko kallo ba su isheta ba, Kai tsaye ta wuce room dinta Da gudu zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna suna dariyar farin ciki, Fuskar hajiya sarah dauke da murmushi ta dubi dr shureim"ta fasa tafiyar ne"? "Eh mommy," ya bata amsa, Har cikin ranta taji dadin dawowarsu. Mutumin kuwa murmushin gefen fuska Ya an saki, yayi tunanin security officers din gidanne suka hanata tafiya baisan cewa itace tai ra'ayin kanta ba, fucewa yai daga falon cikin takun isa. Alhaji ubaid dake kallonsu ajiyar zuciya ya sauke. "Daddy, dan Allah kuyi hakuri da abunda Ya faru atsakaninka da mommy, ku yi kokari ku sasanta junanku" Jinjina kanshi yai fuskarshi dauke da murmushi yace"kada ka damu shureim, ni dama ban dauka da zafi ba, itace ke da matsalar, in sha Allah zanje na lallashe ta" ya fada tare dakai hannu yadan bubbuga kafadarsa kafin Ya juya ya nufi dakin layla don su sasanta junan su. Koda ya shiga akin, ya taras da ita zaune agefen gado, kamar mai jin shakkarta Ya raba ya zauna yana duban ta kafin yai magana tai saurin katse shi da cewa"basai ka bani hakuri ba, ni yakamata na nemi yafiyarka, ka yi ha uri idan na 6ata maka rai, in sha Allah bazan ara ba, zan bi umarninka in zauna har zuwa lokacin da ka so mubar gidan" da wani irin mamaki yake duban fuskarta, kamar amafarki yake jin kalamanta, Wai yau layla ce da kanta take bashi hakuri har take fadin zata bi umarnin shi? "Allah yasa ba mafarki nakeyi ba" murmushi tayi tare da dubanshi tace"ba mafarki bane mijina, dagaske ne, abun nayi ban kyauta ba, su shureim sun yi min nasiha nima naga rashin kyautuwar hakan shiyasa na dawo. Ruko hannayenta yai acikin nashi hawaye tuni sun cika idanunsa Cikin sanyin murya yace"layla bazan iya misalta dadin da naji ba, kin faranta raina ayau, duk da nasan nine mai laifi amma kiyi hakuri ki yafe min, sannan inaso ki sanyani a addu'arki, Ni kaina bansan meyasa bana iya bijirema umarninsa ba, bana son bacin ran musa, saboda ya kyautatamin arayuwa shine silar duk wata nasara da na samu..." bai kare maganar ba tai saurin rufe bakinsa da tafin hannunta, saboda ta tsani taji Yana yabon musa, saboda ita tasan ba hakanan Ya kyale shi ba shiyasa baya iya ganin laifinsa, amma taci alwashin zata gano ainihin wanene Alhaji musa da duk wani abu dayake takama da shi. Abun da bai ta6a tsammani ba, Yaji layla ta kwanto da kanshi saman kafadarta, bawan Allah sai Ya kara lafe mata kamar wani karamin yaro. "Kada ka damu, ni bakai min laifin komai ba, In sha Allah zantayaka da addu'a kamar yadda ka bukata, kaima kuma inaso ka dage dayiwa kanka addu'a" amsa mata yai da toh, cigaba da kwantar masa da hankali tayi, har saida ta cika shi da farin ciki ta dinga zolayarsa tana tuna masa farkon haduwarsu kafin su yi aure. "Yanzu tun da komai Ya daidaita mu koma dining mu arasa yin breakfast din" cikin kulawa mom sarah tayi maganar tana dubansu. "Aunty ki tayani murna" acewer benazir "Fada min meya faru"? "Aneelerh ta kirani awaya har mun yi magana da ita" Murmushi hajiya sarah tasaki"masha Allah, ina tayaki murna my daughter, wlh naji dadi yanzu yaushe zaki je can gidan na su"? Kallon dr shureim tayi wanda gaba daya hankalinsa na akan zeenatu dake a gefensa sai dadi take ji sun fasa tafiya. "Yaya shureim yaushe zamuje? Ni ko yanzu ma kace a shirye nake Allah" ta fada a kagare. "Gobe in sha Allah zan kai ki" da sauri zeenatu tace"yaya shureim nima zan bi ku, dan Allah ku tafi dani" ta fa a a shagwa6e tana kallon shi. "Kada ki damu afa ta kafarki, duk in da zani je a tare zamu tafi" cikin muryar ra a yayi mata maganar, dariya murna tasaki. Benazar tace"kwantar da hankalinki rabin raina, gobe atare zamu je" "Nagode auntyna" "Ki daina murna, kin manta da daddyn ki halan, ba lallai ya amince ki fita ba" tur6une fuska tai. "Mommy pls ki ro an mun shi yabar ni inje" ta fada tana bubbuga kafafuwanta "Zanyi mashi magana zuwa anjima nasan zai bari mu tafi da ita" acewar dr shureim Hajiya sarah na murmushi tace"kunfi kusa ay, nasan kana masa magana zai amince, tun da yana ji dakai na gaban goshinsa" dariya sukai gaba dayan su. ______________________Twins A kwance yake kan katafaren gadonsu idanunsa na fuskantar ceilling, yanayin fuskarsa sam babu walwala ya ha e rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa, bakomai ne yake damunsa ba face ha in da mommynsa tayi masa, ya riga da ya san halinta ba lallai ta canza ra'ayin ta ba, shi fa arayuwarshi sam baida ra'ayin yin auren wuri, yafi sha'awar yai sharholiyarsa son ransa, a yadda ya tsara ma kansa sai yakai 45 years zaiyi aure, bugu da ari baya jin zai iya auran yarinyar saboda ba'ajinsa ba ce, jiya kafin ya kwanta bacci sai da yayi bincike akanta ta hanyar amfani da wayarsa har ya gano wanene mahaifinta wato karen an siyasa, aransa ya ayyana tayaya shi da ya fito daga babban gida shahararren family da duniya tasan da zamansa, zai auri wannan yarinyar, Bayan haka mommyn sa minister ce daddynsa Ceo ne na babban companynsu Obi Tech, tayaya zai auri interior designer? Companyn ma da take aiki ba nata ba.... Abu aya daya hana shi sukuni, kyawun fuskarta da surar jikin ta, daren jiya dakyar ya runtsa, ba halin Ya rufe idanunsa sai ya tuna lokacin da ta fashe mashi kuka la66anta na kerma, kissing inta da yayi har cikin zuciyarsa yaji wani irin shau i da bai ta6a jin sa a wajen wata mace ba, kawai yayi arfin halin tofar da yawu ne don Ya muzanta ta. Motsin bu e toilet ne Ya katse masa zancen zucin nasa, A hankali yakai idanunsa ga duban mai fitowa Zaid ne ya fito waist dinsa daure da towel, suna ha a ido da juna Ya sakar masa murmushi "Bro me kake tunani ne? kamar wani abu na damunka? Banza yayi dashi bai tanka mashi ba amin meya faru jiya bayan mommy ta kira ka awaya" Yamutsa fuska yayi, tamkar baisan maganar ya furta"zaka iya tuna yarinyar nan da mommy ta kawo wurin mu"? Shiru zaid yayi yana kokarin tuna ta can yai murmushi tare da cewa"kana nufin Zahra"? Ta6e baki zayn yai kafin yace"oho na manta sunanta" "Itace zahra, yarinyar ta kwanta min araina saboda ina son mace mai kamun kai daga gani iyayen ta sun bata tarbiya" ya fa a tare da samun wuri gefen gadon su Ya zauna yana kallon zayn "Mommy ce ta ha a ni da ita...." bai 6oye masa komai daga abun da ya faru tsakaninsa da zahra. Har Ya are maganarsa zaid bai ankara ba saboda zuciyarsa da ta karaya, har ga Allah bai ji dadin hukuncin da mommynsu ta yanke ba na hada zayn da zahra, saboda yasan halin an uwan nasa bai jin magana fiye da shi, yarinya mai kamin kai an ha a ta da an iska, ina ma ace shi mommynsu ta hada da zahra da ba abun da zai hana ya gyara rayuwarsa saboda samun mace ta gari wadda zuciyarsa ke muradin mallaka... "Zaid? Naji kayi shiru bakace komai ba? Nasan kana tayani jimami ne" Jinjina kai zaid yai kafin yace"zayn banji dadin abun da kayi mata ba, saboda ba laifinta bane, mommy ce ta hada ta dakai, ni nasan ba itace ta shirya faruwar hakan ba..." ya fada cikin sanyin murya yana kallon zayn dake faman ya mutsa masa fuska "Me zai hana ka jaraba amincewa da bu atar mommy, ni nayi imanin ba zaka ta6a danasanin auran zahra ba, watakil ta zama silar shiriyarka...." kafin ya are maganar zayn ya wurga masa harara tare da katse sa da cewa"kana son ta ne? "Meya kawo maganar so? Kawai daga na baka shawara amatsayinka na dan uwana" guntun tsoki zayn yaja"bani bu atar shawarar ka, nayi zaton zaka tayani jimamin abun takaicin daya same ni ashe ba haka bane dakai da mommy kanku aya..." ya fada yana cije la66ansa"har abada bazan ta6a sonta ba, zan amince da ita ne saboda mommy, sannan zan aureta badan ina sonta ba sai don in mayar da ita abun biyan bu ata na amma babu maganar mutunci atsakaninmu muddin ta aure ni taga ma jin dadin zaman duniyar nan" muryarsa a kausashe ya furta maganar Runtse ido zaid yai har cikin ranshi baiji dadin kalaman zayn ba, baisan ya zaiyi ya shawo kan mommynsu akan ta janye maganar ha a shi da zahra saboda zayn ba mutumin kirki bane, muddin ya auri zahra bakin cikinsa zaiyi silar mutuwarta, dole ya nema mata mafita tunkafin afkuwar lamarin, Indai daddyn su baisan da maganar ba zaiyi kokarin tunzurasa akan kada ya amince da maganar mommynsa....Saukowa zayn yai daga kan gado daga shi sai yar singlet da short Ya nufi toilet Yana huci Ya shige ciki, zaid dake zaune gaba daya kamar an zare lakarsa shi dai ya damu da zahra