Sashe 9
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
aya bayan aya unaisah ta soma kasa masu abincin tana mi a masu a plate, bayan ta gama da su itama ta zuba nata tare da Boss man a plate aya, suka zauna suna ci gwanin ban sha'awa, falon Yayi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke ci... "Ummi Ina son Yin magana dake bayan sallar magrib" Boss ne yayi mata maganar, amsa mashi tayi da toh. "Amma wannan in abincin daren mu ne"? Acewar Parveen, Harararta Naufal Yayi. "Kusan arfe shida na marece, A haka Har kike tambaya, toh abincin dare ne, mu da cin wani abincin sai gobe da safe in Allah yakaimu" javed ne Ya bata amsa Yayin da yake kur6ar lemu me sanyi. "Ba'a magana idan Ana cin abinci," Boss ne ya fa a yana duban su. "Dariya fa da murmushi suma ba'ayi"? Jemimah ce ta jefa mashi tambayar yayin da take cunkusa abinci abaki tana tauna. Dariya suka sanya gaba ayansu cikin raha. "sajeed Ina wayata" Dafe kai Yai da hannu aya"Am sorry sister, Na cinye maki chargy, bansan ko kina da charger ba" "Akwai charger bani wayar" da sauri ta mi e taje gaban sofa din da yake a zaune, Wayar Ya zaro daga trouser pocket nasa ya mi a mata ita. Tasa hannu ta kar6a, kafin ta nufi bedroom dinsu, shigarta keda wuya wayar hannunta ta soma ringing, tana kokarin aga Wayar ta kashe kanta kamar tayi hauka saboda ta gane number da suka kirane ita da sajeed.' Cikin takun sauri ta nufi backpack din su, ta bu e ta dauko cazar wayar ta jona a socket, akan idonta wayar tayi haske alamar ya auka, lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta jikin gadon, zuciyarta a cike fal da tunanin shi. NAZLI Sautin dadda an ki a ne da ke tashi a katafaren gym room ( akin motsa jiki) da ke a gidan prime minister, an awata shi da manyan injinan motsa jiki, a tsaye take saman thread mill tana gudu cikin shiga ta kayan motsa jiki, sport bra tare da short launin black colour, sunyi bala'in yi mata kyau, sun bayyana farar fatarta sol ko kwarzane babu, tamkar bata ta6a yin rarrafe ba arayuwarta saboda hasken fatarta harta gwiwar afarta tayi jawur da ita, dirar mace doguwa ga kyan sura, ta aure lallausar ba ar sumar kanta sai sal i take yi da she i ta sauko har saitin waist din ta, gaba aya ta tattara nutsuwarta akan abun da take yi, sautin music din ba aramin ni'ima yake samar mata ba, kyawawan idanunta na akan tan ameman madubin dake manne da bango, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina ta ji e sharkaf da ita, babu alamun gajiya atattare da ita, daga gani ta ware a 6angaren gym. Bakomai ne acikin zuciyarta ba, face zallar begensa, duk yadda taso ta hana kanta tunawa da shi abun yaci tura, tayi tunanin zata iya sarrafa zuciyarta wurin hana ta tunaninsa sai dai abun yaci tura, a kowani da a son shi ara ninkuwa yake yi a zuciyarta, ga dukkan alamu Nazli batasan menene So ba, ko da yake girman kai da izza sun hana ta gane cutarwar da take yima kanta, shiyasa ta kasa mi a wuya" Tunanin shi ne ya haifar mata da jin Kasala, ba arzi i ta dakata da motsa jikin, ta kai hannu ta auki short towel fari al ta soma tsane jikin ta da shi, bayan ta kammala fitowa tayi daga gym room din ta nufi bedroom dinta, kai tsaye ta shiga bathroom domin yin wanka. Shigowa akin Yazrin tayi cikin shiga ta riga da wando black and white, tayi rolling veil akanta, hannunta ru e da wayarta. Ganin babu ita a dakin yasa tayi tsammanin ko ta fita ne har zata juya ta juyo motsin ta a toilet da sauri ta la6e a bayan labule. Gently ta zuro afafunta dake sanye cikin slippers, bathrobe ce a jikinta fara yal, hannunta aya ru e da towel sai faman tsane sumar kanta take yi. Yazrin dake a la6e bayan labule, wayarta ta danna ta shiga camera ta age labulen a hankali ta soma aukar Nazli video batare da sanin ta ba. Dressing mirror ta nufa cikin takun qasaita, wasu tsadaddun mayukan gyaran jiki ne asaman mirror din, bayan ta zauna ta soma bin ko'ina tana shafe shi a tsanake, kafin ta dauko bakhhoor burner ( turaren wuta) ta soma turara jikinta da sumar kanta, komai nata cikin aji take yin shi, Nazli macece mai tsafta ga son gayu, kuma ma'abociya son amshi. Duk wani motsinta, Yazrin na kallonta ta cikin camera, bayan ta gama gyaran jikin nata, closet ta nufa jim ka an ta fito, har ta canza kayan jikin ta zuwa kimono robe, yazrin da ke ta daukar ta video kayataccen murmushi ne kan face dinta, aranta ta ayyana ukhty Nazli badai iya gayu ba, bata gama zancen zucin nata ba, taga Nazli ta haye saman Royal bed dinta hannun ta ru e da wayarta, bakomai take kallo ba face hotonsa, har zooming dinshi take yi da zira ziran yatsun hannunta, hoton da take kallo tsohuwar ajiyace a kalla yakai shekara biyar, lokacin yakai masu ziraya a canada, ba tare da sanin shi ba ta dauki hotan, dama duk in yaje basa jituwa da Nazli, har ya bar asar basa sakarma juna fuska kai kace makiyane, Yazrin ce kadai suke mutunci da juna, kuma a lokacin suna matu aunar junansu, amma izza ta hanasu bama juna kulawa sai dai su yi magana ta text message, tamkar basa a gida aya. fita tai daga gallery ta shiga wurin messages dinsu Har ta rubuta "I miss u.... ' sai kuma ta goge, zuciyarta na raya mata zubda aji ne ta nuna ta damu dashi, shi ne yakamata yafara yi mata magana Jefar da wayar tayi gefenta, tare da kai hannu taja lallausan duvet dinta ta lullu6e fuskanta, ganin hakan yasa Yazrin fitowa daga bayan labulen cikin san a ta nufi gadon, tare da hayewa ta janyo wayar Nazli cike da fargaba cikin sa'a ta auko ta batare da security din wayar ya shiga ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba. Whatsapp dinta taso ta shiga sai dai kash password Ya hanata, tunani ta soma yi me Nazli ta rubuta a matsayin password dinta? Gudun kada ta tayi mistake ta samu matsal Zurfi tunani ta shiga, can zuciyarta ta raya mata cewar ta jaraba rubuta date of birth din Aki Owais saboda ta ta6a ganin ta rubuta shi a diary din ta amatsayin rana mafi mahimmanci agare ta. Wani irin tsalle ta daka ganin Ya bu e, da sauri ta shiga nutsuwarta tana le en Nazli, wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita Yazrin tayi mamakin ganin tsawon lokacin da suka dauka ba suyi magana wa junansu ba, Ranta ya sosu bata ji da i ba, ji take kamar ta dauki pillow ta bubbuga mata akanta tsabar haushin da taji. ar bakin ciki, In sha Allah baki da miji a duniyar nan daya wuce big bro, bazan zauna na zuba maki ido kina cutar kanki ba, Akhi Owais shi ya dace ya mallake ki, nayi maki sha'awar auran shi saboda samun miji nagari irin shi ba abu ne mai sau i ba, Ina son kiyi rayuwar farin ciki yar uwata, dole na shirya tsakaninku.... " acikin zuciyarta ta furta maganar tare da cigaba da danna wayar, daga wayarta ta tura video din data dauka, kaitsaye ta yi mashi sending, shaf shaf ta rubuta mashi text message da harshen turanci kamar haka _Nayi kewarka bugun zuciyata, ina mai baka ha urin nuna halin ko'in kula da nayi, ba'asan raina ba, nayi danasanin hakan don ba aramin cutuwa nake yi ba na rashin jin umin jikinka a kusa dani, ka duba whatsapp in ka, na tura maka video dina don ya ebe maka kewar rashi na, nasan zaka ji dadin kallon shi_ fuskar yazrin dauke da murmushin mugunta ta tura mashi message din, bayan ta gama ta ajiye mata wayarta, ta nufi kofar fita daga dakin tana faman sakin dariya, ta riga da tasan me zai biyo baya muddin Nazli taga aika aikan da tayi mata ba aramin husuma zata tada ba, zata ce ta zubda mata aji awurin chief owais. *A GIDAN UNCLE AN IYA* Kusan Atare Su ka yi Parking din motocin su, Mahboob ne Ya fara fitowa daga front seat hannun shi aya ru e da key din Motarshi, fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Motar zahra. "Sannu da dawowa Hajiya Zahra Surukar Kaka Obinna" Ya fa a tare da bu e Back Seat din Motar Shi Ya du ar da kai Yana le an Baby Junaid dake zaune Hannayenshi rungume da Food basket dinshi, Ga school bag din shi a gefe, Sai faman aure fuska Yake, Da alama rigimar tashi ce ta motsa. "Ranka Shi da e, Mun araso gidan, zaka iya takawa da kafarka ne mu shiga ciki ko kuwa ni kake so In goyaka"? Da zolaya mahboob yayi maganar yana dariya. Yamutsa mashi fuska baby junaid yayi "ni ka goyani" Ya fada A kule. Juya mashi baya Mahboob Yayi Ya an zu unna Baby Junaid Ya Haye bayan nashi, Bayan Ya mi e Ya auko mashi Backpack dinsa tare da kwandonsa Adai dai Lokacin Zahra Ta fito daga motarta, tayi shiga cikin Lafaya, Hannunta aya ru e da ar purse dinta Fuskarta da fara'a take duban Baby Junaid Da Mahboob "yau wata rana mun dawo gida atare, baby junaid dina zo nan" ta fa a tare da mi a mashi hannu, babu musu Ya soma kiciniyar saukowa daga saman bayan mahboob, daukarshi tayi Mahboob yace"Wato ni kake gudu? Zamu hadune an rainin wayau, tun da naje dauko shi Daga school Yake ta jin haushina saboda naje amakare shi ka ai Ya rage ba'aje daukarsa ba, baisan nima bada son raina ba, Motarce ta samu matasala sai da nakaita gyara tukunna naje daukoshi da ita" Dariya zahra tayi"Gaskiya baka kyauta ba, taya zaka bar mana Baby Shi kadai Ga yunwa, meyasa baka kirani awaya naje daukosa ba" "Banyi dabarar yin Hakan ba, Yanzu dai tun da mun dawo gida, gashi nan ki kaima jatumarsa, nagaji da kallon kumburarran fuskarshi" "Mahboob baka da