← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 209 OF 247

Sashe 209

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

baro aminin nasa"? "Mun baro shi lafiya, Baba Obie Yana a part dinsa, da anjima ki shiga kiyi ma shi barka da dawowa" "Okay, fada min me kake son in kawo maka"? "Bana jin yunwa, Naci abinci agurin hajiya saratu, A yanzu nafi bukartar ki" ya fada tare da daukarta kamar Yar baby, Dariya ta saki tana kallon shi.. Jujjuyata yai kafin ya nufi gadon su da ita, ya jefa ta a hankali, tana daga kwance tana kallon shi yayin da yake a tsaye yana Unbuttoning din rigarsa. "Ba zan raga maki ba, almost one month, dakyar nake Iya bacci saboda rashin ki" Tace"nima haka, ba raga maka zanyi ba, ka tafi ka barni da kewarka" _________________________________ Shigowa dakin ta yi, tana kokarin Yaye veil din da tay rolling, taga wayam babu pravin data bari yana cin abinci adakin. "Ina ya shiga ne? Ko ya shiga toilet"! Ta fada aranta, tare da nufar toilet door ta danyi knocking shiru ba'a amsa mata ba, sai dai taji sautin safkar ruwa alamar ana amfani da shi. Watsa hannayenta tayi, ta koma ta zauna daga gefen gadon, Ta curo waya daga cikin yar purse dinta ta danna na Hajiya laura Kira. "Mara mutunci, Sai yau kika tuna dani? "Banson iya shege matar Yaya, don kar in tuhume ki shine kika rigani magana ko"? Fashewa hajiya laura tayi da dariya"Sorry aminiyar arziki, bana fada maki zanje dubai ba? Sai jiya na dawo agajiye wlh" hajiya saratu tace"kai haba, Ashe kun dawo, Ya gajiyar tafiya" "Alhamdulillah, gajiya tabi jiki, akwai fa kaya, munyi sabuwar auka, Na tura maki videos ta whatsapp yakamata ki hanzarta zabar wanda kikeso tunkafin akwashe kizo kina cizon yatsa" Hajiya saratu tace"Amma naji dadi wlh, dama ga hidima muna da ita, dazu Owais ya nemi alfarmar ayi family meeting a birthday dinsa, kuma kinsan In Owais zaiyi birthday, ko biki albarka saboda yarda baba Obie ke ji da shi ina mai tabbatar maki za'ai harka ta arziki" dariya suka sanya gaba dayansu Laura tace"amma da mamaki Owais daya saba yin birthday a canada inda aka haife sa kice wannan karan A Nigeria za'ae, Amma fa naji dadi wlh, Allah ya nuna mana lokacin lafiya" Sun dan jima sunayin waya da hajiya laura kafin su ka yi sallama. Gallery ta shiga ta bu e hotunan da tayi ma Parveen aranar dinner din Hateem batare da sanin ta ba. Kamar ibada kullum saita kalli hotunanta, ta6e baki ta anyi. _____________UNAISAH ANGEL Tana a kwance kan gadonsu, Ta lumshe idanunta yayin da brain dinta ke tariyo mata memories dinsu da Danish, wani sa'in ta yi murmushi wani sa'in ta zubda kwalla, Amma yau tunanin nata ya kasu gida biyu, saboda kalaman da Chief ya furta mata adaren Jiya da su ta wuni aranta, bata ta6a zaton mutun me matsayi irinsa zai iya aje girmansa da komai donya ja ta a jiki ba. "Unaisah" muryar Ummi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula Su biyu suka shigo dakin, Hannun Batool ruke da wooden tray mai dauke da dinner dinta akan table ta daura mata shi. "Su daddy sun dawo" Ummi tace"a'a may be sun tsaya yin sallar isha'i ne naji an fara kira, yanzu dai ki daure ki tashi kije ki yi wanka" e kafa a tayi"Pls aunty Ummi, dan Allah kibarni, Bana son maganar wankan nan nafi jin dadin jikina a haka, Ni wlh tsoron ma taba ruwan nake"? Baki asake ummi ke kallon ta. Batool tace"pls Ki daure kiyi wankan zaki ji dadin jikin ki, baki ga yarda kika koma ma ba? Kamar yar mahaukaciya" Ummi tace"fada mata dai, Gashin kanki ko kyan gani babu, Pls ki tashi kiyi amfani da ruwan zafi zaki fi jin dadin jikinki" girgiza kai tay Ummi ta dubi Batool"in muka bita ta lalama bayi zatay ba, Abun da za'ay ki kama hannunta ni in kama kafafuwan mu shiga da ita ciki muyi mata wanka" kafin ummi ta karashe maganar suka ga ta zabura ta mike tsaye tana girgiza dariya suka kwashe da ita. "Dan Allah ku kyaleni, tun da nace bana son wankan, Ba jikina bane wai" Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy. Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet. Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya. Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe.. Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara she "Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"? Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi" cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta. Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta. Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"? Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi "Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din. Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji. "Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi" Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan. Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su" "Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin" Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon. Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan. Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau. Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita. "Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay, "Bani da lafiya, amma naji sauki" Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su.. "Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"? aru e ya tambaya yana dubansu. Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly. "Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi. "We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..." Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"? "Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh Imam, Ya girgiza da jin basu dawo Danish ba, wlh yaji zafi acikin zuciyar shi.. Girgiza kai yai idanunsa cike tab da walla. Ya dan jima batare daya furta kalma ba, Can ya numfasa cikin karyayyar murya yai masu nasiha akan suyi hakuri da rashin da sukayi Su mika lamuransu gurin kada su sare, Danish kuma zasu tayashi da addu'a in ya mutu Allah yajikan shi In kuma yana araye Allah ya bayyanar da shi. Sannan Ya bukaci yana son yaje ya duba su Salsabeel chief yace idan suka tashi zuwa zai kirashi sai suje atare su duba jikin su saboda asibitin ba a kusa yake ba. Shiru sukayi falon yai tsit kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyar shi. "Ina auntynku? Ko itama tana a dayan bangaren ne"? Kaitsaye maganar shi ta dira a kunnan Ummi tayi mamakin Jin sheikh Imam ya tambayeta. "Tana anan tare da mu" Batool ce ta bashi amsa.. Batay niyar fitowa ba amma saboda maganar sheikh Imam yasa ta fito jikinta sanye da dogon hijabin data dauko a cikin closet din su Unaisah. Har kasa ta zukunna ta gaishe da shi fuskarsa da fara'a ya amsa mata, ta danyi mamaki mutumin da ko kallonta baisonyi amma yau haryake tambayar tana ina. "Hateem Yasan da maganar"! Girgiza kai chief yai"ban sanar da shi ba ko da zaiji ba yanzu ba," Sheikh yace"Allahu akhbar, Allah baya barin wani don wani yaji dadi, Hateem yaso yaron nan kamar dan cikinsa, nasan in yaji hankalinsa ba
Chapter 209 · 0% Book details